ABUBUWANDA YA DACE MACE TAYI BAYAN HAIHUWA
ABUBUWANDA YA DACE MACE TAYI BAYAN HAIHUWA
Wannan gabar tanada matuqar muhinmanci mata su Santa sosai.
Mafiya yawan matsaloli da suke faruwa tsakanin ma'aurata suna farawa ne bayan haihuwa, saboda a lokacin duk Wani yanayi na diya mace y canja, Sannan yanayin gudanarda rayuwarta zai canja, zai canja daga ita kadai d mijinta zuwa itada miji d yaro ko yara.
Bayan mace ta haihu Abu na farko y kamata ta dage wajen gyaran jikinta bakin gwargwado Kuma ta yanda Bai Saba wa shari'a ba, kada mace ta zama Kara zube, saboda aiki y Dan qaru gareta sai tazama bata gyra jiki, gyaran jiki sosai fa nake nufi, musamman qasan jikinta, saboda mace d ta haihu yanayin halittar jikinta y sauya, ta haka ne qwayoyin cuta suke daurin shiga jikin 'ya mace akan da namiji saboda yanayi na haihuwa, sai an dage d gyara sosai, sannan kwalliya, tarairayar miji, kula d gda, da sauransu.
Kakanninmu na cewa ba'a gane tsabtar mace mai aure sai ta haihu, saboda a lokacin komai y canja, g kula d yaro, miji, gda d Kuma ke kanki.
Abu na biyu shine yanayin girki. Idan mace ta haihu yanayin girkin ta na cikin abubuwanda y kamata ta dauki mataki Akai, kafin ki haihu, abinci daga ke sai miji, ynzu Kuma ayukka sun qara yawa komai zakiyi sai kin saka lissafin d yara aciki, saboda dawainiya d yara shi kesa wasu basa qare girki d wuri, mun sani sarai abinci bayan miji y dawo shine Abu mai muhinmanci d yake buqata, idan y tarar ba'a qare ba to akwai damuwa, irin haka shi yake haddasa maza suke cin abinci a waje, ko Kuma ku fara samun sabani d miji, saboda yunwa ba irin abinda bata haifarwa.
Har wayau dai mace bayan ta haihu tsabta dai itace kan gaba.
Duk macen d tahaihu to ta kiyaye tsabta hani'an, tsabtar kuwa ta hada da,
Wanki
Wanka
Wanke wanke
Goge goge
D share share
Mafi muhinmanci Kuma tsabtar jiki taki data yaro.
Y kamata mace bayan ta haihu ta samu abubuwa masu Gina jiki nata d na yaronta wanda Zaina qara masu lafiya bakin gwargwado, saboda ta abinda mace keci ne yaro yake samun abinda yaci shima.
Abu da yafi kowane mahinmanci shine bayan mace ta haihu y kamata ta qara duqufa d dagewa wajen yima iyalanta addu'a, da neman tsari da Kuma tattalinsu gwargwadon iko.
0 Response to "ABUBUWANDA YA DACE MACE TAYI BAYAN HAIHUWA"
Post a Comment