-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Yadda ake ZAMAN BUDURCI BUDURCI A WANNAN ZAMANI

Yadda ake ZAMAN BUDURCI BUDURCI A WANNAN ZAMANI

Yadda ake ZAMAN BUDURCI BUDURCI A WANNAN ZAMANI

 Yar uwa nikab baya hana samun miji, sedai lokaci beyiba, da zararar lokaci yayi shikenan komai ze zama tarihi, yar uwa idan zaki saka nikab da hujab kitabbatar nhijab din naki ya cika sharudan hijab, amusulunci ya kasance mai tsayi mai fadi mai kauri, kuma ki yabbatar kin saka safa ko takalmi Wanda ze rufe kafarki ruf, kada ki saka turare mai karfi, manufar saka hijabi shine ki suturce jikinki ba dole sekin saka nikab ba, amma atakaita kwalliya don Allah. 

Sanan kuma alokacin da kike zaman budurci, ki zama mai kula wajan zabawa kanki abokin rayuwa, ma ana miji da zaki aura, ki tsaya ki nutsu wajan samowa kanji abokin rayuwa, idan na miji ya aureki domin kyaune to wlh akwai lokacin da kyauwun nan ze gushe agareki, domin dama ba don Allah ya aure kiba amma so na tsakani da Allah baya gushewa har abada.

Kibi wadanan hanyoyin kafin samawa kanki miji na gari, ki kasance mai yawan Istikhara da ma aiki ya koya mana, domin samun miji nagari, Istikhara daya koya mana tashi cikin dare musamman tsakiyar dare, kiyi al wala sanan kizo kiyi sallah raka a biyu, kafin kiyi sallama, zaki iya yi acikin sujjada ko kafin kiyi sallama bayan kinyi tahiya, ki karanta kamar haka.

Zakice, Allahumma inni astakirukha bi ilmikha, was astak dirukha bi kudratikha, wa as aluka min fadlikal azeem, fa innaka takdiru wala akdir, wa ta alamu wala a alam, wa anta allamul guyub, Allahumma in kunta ta a lamu anna hazal amru,(seka fadi abinda yake ranka Wanda kake neman zabi akansa) seka ciga gaba, kace khairillu fi dini wama ashi wa akibatu amri, fakdurhuli wa yassirhuli, summa barikli fihi, wa in kunta ta alamu anna hazal amru sharrili fi dini wa ma ashi wa akibati amri, fasrifhu anni wasrufni anhu wakdur liyal khaira haisu khana, summa radduni bihi. 

Wanan itace istikhara mafi inganci da ma aiki ya koya mana muyi idan wani al amari ya taso mana, bama iya samun Mijin aureba, fassarar wanan it's addu shine, 

Ya Allah ina neman zabinka domin ilminka, kuma ina neman ka bani iko domin ikonka, kuma ina rokonka daga falalarka mai girma, domin Kaine mai iko ni kuma bani da iko, kuma kaine masani ni kuma ban saniba, kuma Kaine masanin abubuwan fake, ya Allah idan kasan cewa wanan al amari, ( se mutun ya ambaci bukatarsa) Alherine gareni acikin addini na da rayuwa ta, da kuma karshen al amarina awata rayuwar, da magaggaucin al amarina da majinkiri ka kaddara minshi kuma ka saukake minshi, sanan ka albarka ceni acikinsa, kuma idan kasan wanan al amarin sharrine gareni acikin addinina, da rayuwa ta da karshen al amarina a wata rayuwar da magaggaucin al amarina da majinkiri ka kawar dashi daga gareni, kuma ka kawar dani daga gareshi, kuma ma kaddara min alheri aduk inda yake, kuma ka Sanya ni in yarda dashi. Wanan shine fassarar abinda ka fada, akwai shi acikin littafin hisnul Muslim, a duba idan ka dur fafi wanan shi kadai ya isheki ba sekin tafi gurin bokaye ba da masu tsibbu da tsaface tsaface ace kiyi wanan kiyi wancan ki kawo wannan, duk bashi bane kitsaya ga Allah daya shine maiyi idan ka rokeshi yana jinki kuma kisa aranki yaji ya amsa miki, kuma shine maiyi ba wan ba, ki gwada wannan kiga zakiga sauyi kuma insha Allah Allah ze miki zabi mafi Alkhairi Wanda baki taba zata ba ammafa sekin tsaya ga Allah, tukun. 

Sannan bayan wanan, kiyi Shawara da ma abota ilmi da hankali, domin ubangij madaukakin sarkin yana cewa acikin alkur ani mai girma,yace ku kasance ma abota shawara a al amarinku,

Sanan kibarma Allah al amarinki domin Allah shi kadai yasan abinda ze faru dake, kuma shine masa nin gaibu.

Sanan kuma yar uwa ki kuma zama mai kula, awajan irin namijin dazaki tsaya dashi, bafa farin jini bane ace ko wana gara da sauna yazo yace yana sonki ke kuma daga yazo ki karbe shi waike me farinjini, wanan ba farin jini bane, samari yan karya sun cika gari, kada ki zamo daya daga cikin yan matan da se maza sun musu karya suke burgesu, yana iya yi miki karya ya kaiki gidanshi ya Aureki, amma karyarshi ba zata iya rike kuba keda shi, ki kiyaye wanan.

 kudi mulki nasaba kyau kada ki tsaya wadanan kadai wajen tantance na miji da zaki kula, kifi maids hankali wajen ilmi, nutsuwa, hankali, wadatar zuci, uwa uba addini.

Kada ki zamo mai bin kyalkyalin duniya da zuciyarki, karshe kizo kiyi dana sani bayan kinyi aure, idan kinaso ki zama daya daga cikin wadanda suke hutawa suke shakatawa game da kwanciyar hankali, to ki zama daga irin matan da sukabi addini wajan zaban abokin rayuwa wato Mijin aure, ba kyalkyalin banza ba na duniya.

Kada ki yarda ace se bayan kinyi aure zakiyi hankali , ki daure kiyi hankali tinyanzu hankali wajan zabar abokin rayuwa. 

Kada ki rinka tunanin idan kin aure me kudi zaki huta, ba anan takeba kedai kiyi aikin da shawa ra da ma aiki ya gaya mana wato mai addini shine zaki huta Hutu mara adadi, hakki yana kanki dolene ki zabawa yayanki uba nagari wajan tantancen irin mijin da zaki aura tare da mikawa Allah ragamar ki da yarddarki. 

Sannan kuma, yake yar uwa ki rike wannan kada ki manta, akwai wasu mazaje kala hudu dabe dace mata su kallesu ba. 

Ba duk namijine ya dace da kulawarki ba, baduk namiji bane zaki bashi zuciyarki ba, ba duk namiji bane zaki amince daya aureki ba, duk zakuwarki da son aure kuwa, ki tsaya ki nutsu kada kizo kiyi auran kizo kina cizan yatsa, ki saurara kiji.

Na farko, shine na miji mara ibadah, shi rashin ibada yakan iya mutum ya zama baida duk wani imani ko tausayi da ake bukata magidanci ya kasance dasu, muddin kika fahimci irin wanan namiji yana Sonki to kada ki saurareshi.

 Na biyu, namiji me dagawa, kada ki sake ki kula namijin da yake da dagawa, ji dakai takama da dagawa, muddin kuwa kika bashi rana koda da rana dayane, seya nuna miki iyakarki, sune irin mazan dake iya duban cikin idanuwan mace su goranta mata, su kuma kaskantar da iyayenta, sune irin mazan da suke ganin auren mace tamkar alfarma suke mata da suka aureta. 

Na uku, namiji da bai ganin darajar mata, sune suke ganin mace ba a bakin komai takeba, irinsu basu ganin darajar mace suna iya yi mata wulakanci aduk inda ya kama kuma ko agaban waye, irinsu suna ganin mace kawai abar jima ice aji dadi da ita daga nan kuma bata da wani amfani se kuma wannan bukatar idan ta taso, muddin idan kika baiwa mazan nan dama azuciyarki to zaki dana sani mara iyaka mara amfani.

Na hudu, sune maza makaryata, duk inda aka samu makaryaci zaka samu shi mayaudarine, don haka mayaudara maza sunada hadari, da ace mace zata basu amincewarta saboda rashin sanin tabbacinsu, dase tayi kuka wataran, yadda yake shimfida miki zance haka nan yake shimfidawa wata acan, don haka mu amala dashi yanada mutukar hadari. 

Idan har kasa kanada wanan halayya yi kokari ka canza domin baka makara ba. Idan kuna kinsan kinada saurayi mai irin wannan halin yi kokari ki fadakar dashi idan kuma bai dainaba ki barshi, amma kada kiji ance kibarshi kice zaki yiwa mutum wulakanci a ah, kibi mutum ahankali Ku rabu lafiya, domin bakisan kalar wanda zaki wulakantaba, tunda mutane kala kala ne, akwai mugaye wanda da zarar sunga bazasu aurekiba to zasu kudiri niyyar kema bazakiyi aureba, don haka akula sosai yan uwa mata.

Sanan yake yar uwa, ki kula, ki samawa kanki lafiya da kuma tsira da mutunci, shine duk na mijin daya so miki da haramtacciyar soyaiya ki rabu dashi duk son da kikeyi masa, kowana namiji da matarsa haka kuma ko wace mace da Mijinta, Allah madaukakin sarki ya riga ya kaddara, kawai shi aure al amarine na lokaci don haka kada ki watsar da kanki mutumcinki, da kimarki, saboda tsoron rasa saurayi, kirinka tunani idan ya tafi yanzu waye zezo wannan duk tunanine daga shedanne, idan mijinki yana bangon duniya ta gabas to se Allah ya hadaku kunyi aure.

Sannan yar uwa ki kiyaye kanki daga aikata zina, yin zina yana da mutukar hadari ga rayuwar ya mace, kamar yadda Abdullahi bin mas ud radiyallahu anhu yace, da ace mace tasan hatsarin dake cikin zina wallahi idan an bata duniya da abinda yake cikinta da bazata yi zinaba.

Duk wanda yace yana sonki da niyar ya bataki, kuma yace sonki yake to karya yakeyi.

Bara kiji yar uwa hakika bakida makiyi aduniya wanda ya yaudareki da wasu kalaman banza da kudin banza, yayi zina dake ya tarwatsa miki budurcinki, Wanda koda auranki yayi har abada ba za kiyi mutunci a idonsa ba, kuma bazai taba aminta dakeba har abada, saboda bakida abinda mace take takama dashi a wajen Mijinta shine budurcinta, to mezesa ki mika masa ragamar kanki tin kafin ya aureki, to wanan ba kauna bace.

Saboda haka 'yar uwa duk kyawun namiji ko arzikinshi, ko nasabarshi, ko ilminshi, ko menene ma kada ki bata alakarki da Allah saboda shi, kizubar da mutumcinki da darajarki ta 'ya mace saboda shi, kiyi yaki da zuciyarki matuka kiji tsoron Allah, tabbas Allah ze baki farincikin da baki taba tunaniba, kuma ya baki wanda ya fishi, yadda acikin hadithi manzon Allah (s a w) yace duk wanda ya bar wani abu saboda Allah to Allah ze bashi Wanda ya fishi.

0 Response to "Yadda ake ZAMAN BUDURCI BUDURCI A WANNAN ZAMANI"

Post a Comment