-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

YADDA AKE ZAMAN AURE

YADDA AKE ZAMAN AURE

YADDA AKE ZAMAN AURE

 shawara ga ma aurata, mazaje gareku ya kamata Ku gyara, kada kazamo azzalumi ga iyalanka, kamar yadda wasu sukeyi kaga magidanci yabar iyalanshi da abinci garaugarau, aci yafi babu, shi kuma yaje gurin me indomie adafamai indomie da akwai ga katan bread, yanaci bayajin kunyar ubangijj, idan Allah ya wadataka kaima ka wadata iyalanka domin ciyar da iyankama sadakane, Wanan shine namiji, Wanda yafi acikin maza ,shine Wanda yafi kyautatawa iyalanshi, kyautawawa iyalai kuwa, kasa asamu daukaka duniya da lahira, Kada ka zamo me takurawa iyalanka idan ka shigo gida kana muzurai da zazzara ido waikai aji tsoronka, manzon Allah ba haka yace mana ba, ka zamo mai sakin fuska ga iyalanka da wasa dasu, ta hakan zaka basu dama kasan matsalar dame tare dash domin magancewa, amma idan kazamo Mai tsangwama da hantara acikin gida, tabbasa ka dauko hanyar ruguza farin cikin iyakanka, yaranka zasu tashi suna tsoronka bazasu sake da kaiba, kuma hakan ze iya taba tunanin yaro, haka itama matarka zaka shiga hakkinta, kada kazamo mai duka ga iyalinka,wai kai mai saurin fushi, Abu kadan kace zaka daketa, a ah wanan ba mutumcinka bane, idan kanayin haka zaka jawoka kanka raini, har agurin Yayanku, akoda yaushe suna ganin kana Dakar musu mahaifiya, tabbas wata ran zakaga ba daidaiba, daga wajensu, hakan ze taba musu tarbiya, kada ka zamo me zagin matarka, idan taima lefi, domin yin hakan ba girmanka bane, kuma ze jayo maka raini atsakaninmu da ita, zata dena ganin mutumcinka, duk abinda matarka taima, nasiha itace mafita, kabi matakan daya dace domin yi mata hukunci, ka kyautata ma amularka ga matarka, kada kaga ance Kaine na miji Kaine babba yazama kana tauye mata hakki, tabbas ubangiji baze barkaba, kamar yadda aka fada aljanar mace na tafin kafar mijinta, wanan kalma ba zatasa kana yi mata abinda kaga damaba, kazamo namijin kafi karfin gidanka, ka  mutuntata, ka bata hakkita ka darajata, ka mutunta yan uwanta da abokan arzikinta, kana yi mata abinda ya dace, ka shagwabata, kariritata, ka maida ita tanajin cewa bayan kai aduniyarnan batada tamkarka, lalle zaka samu kulawa matuka awajen matarka

0 Response to "YADDA AKE ZAMAN AURE"

Post a Comment