-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Wa Yakamata na Aura

Wa Yakamata na Aura

Wa Yakamata na AuraMu Kyautata Rayuwarmu. Halaye da Dabi un da mace budurwa  ya kamata ta tasiffantu dasu. Abu na farko dai shine riko da addininki sosai sauda kafa, babu kasala ibadarki kiriketa GAM, da zarar kinji ana kiran sallah azaharne ko la asar ko magriba ko isha ko asuba, to duk wani Abu da kikeyi a rayuwarki ki jingine shi gurin daya, kije kiyi sallahr ki akan lokaci, domin haka Allah yace kuma haka Allah yake so ayi masa ibadar sa alokacin da yace bawai  a lokacin da zuciyarki take soba, matukar kina da tsarki, ma ana bakya cikin jinin al ada, yawaita yin azumin nafila kaamr na litinin da alhamis, ko kuma azumin da ake gudanarwa idan watan musulunci ya kama, azumin tasu a da ashura, ko sitta shawal guda shida da dai sauran azumun muka na nafila, to dukkan wata mace  budurwa idan ta rikesu zata zama mace ta gari, insha Allah, indai kina yinsu tsakani da Allah, domin samun  awajen Ubangiji, to insha Allah zaki kasance cikin kariyar Allah, amma idan kinayi ne don mutane su  gani suce kinyi to gaskiya ba lada sedai tarin dunbin zunubi. Riko da iyayenki sauda kafa biyayya garesu, idan sunce wance bari sau daya tak, to kada ki yadda ki kara aikata abu harsu kara miki magana ta biyu, idan sunce kiyi Abu atake ki tashi kiyi abinda suka umarceki da yinsa alokacin da suke so, ba tareda sun kara miki magana akaro na biyu ba, kiyi musu shi alokacin da suke so, bawai alokacin da zuciyarki take soba, matukar wanan abun ba sabon Allah bane.

Sanan duk abinda zakiyi arayuwarki karki bari iyayenki suyi fushi kosu bata rai, kai wataran har suyi kamar zasu tsine miki, to ka abayan idan sune, to kada ki taba yadda, ace so ko kaunar wani ta debeki kin aikata wani abu a rayuwarki, duk abinda iyayenki zasu gani suji dadin haka aransu suyi farin ciki arayuwar su harma suyi miki addu a, to koda ace bayan idan sune kina iya aikata wannan, abun kai tsaye. Bin iyaye da yi musu biyaiya, tamkar yiwa Allah da a ne, fushin iyaye, tamkar fushin Allah ne, kenan idan since miki kada ki aikata kaza, kika zauna kika shirya karya, har kika aikata shi, har suka dawo suna fushi dake, to Allah ma na fushi dake kuma ibadar kima dakyar Allah ze karba, matukar iyayenki suna fushi dake, sanan idan kinyi aure kin haihu zaki gani yaranki har fiye da abinda kika aikata abun bazai miki dadi ba, don haka tin yanzu ki gyara, kuma ki kintsa rayuwarki, domin kyautata gobenki da samun rabauta awajan ubangiji. Sanan da tsoron Allah fadin gaskiyarki tsakani da Allah, koda kuwa wanda zaki gayawa abin bazai mashi dadi hakan ba, kedai ki furta masa gaskiya, kada ki sake ki fadi karya, sabida fadin gaskiya da aiki dashi arayuwarki, hakan na saka ki zama mace ta gari insha Allah, rashin fadar gaskiya da yin aiki dashi ze miki illah amatsayin ki na wacca zataje gidan miji nan gaba, wasu mata agidan mazajen su rashin fadar gaskiya da rikon amana da yadara,ya jawo dayawa basajin dadin gidan mazanjen su, amma matukar kikai riko da wadanan abubu da akab lissafo, zakiji dadi agidan mijinki, bazaki sha wahala ba,

Ki zama mai kamun kai, da kunya, idan kin kasance acikin maza  a makaranta ne ko a inane to kada ki yadda namiji yazo ya zauna akusa daf dake, ga cinyarsa ga naki cinyar har kuna  taba juna, duk yadda zaku zauna dana miji ya zama na akwai tazarar miter 2 zuwa daya a tsakanin Ku dashi, koma waye shi. Sanan sanya suturarki da kwalliyarki, ya zama na idan waje zaki futa kada ki sanya sutura Wanda zaki baiyanar da tsiraicin ki, ko kyan halittarki, har hakan yasa kina tafiya maza suna sha awarki, har suna binki saboda haka, ki bada misali da wayar da take hannun ki da kike amfanin da ita, gashi kin siyeta da tsada, kinsa mata glad dinta afuska, domin kada ta fadi ta fashe, Wanda idan kin yashi siyarwa farashin ze ragu, kin siya rigar  ko ace cover kinsa mata, domin kada ta kode, kinsa mata leda abaya duk kada ta kode, jikin wayarki kota ina kin rufe kin boye kada ta kode, to haka ya kamata ace kinwa jikinki ko ina, bawai ki suturta wayarki ki bata mahimmanci, fiye da kanki ba, haka idan kina tafiya, gefen hanya zaki rinka bi bawai tsakiyar hanya ba, sannan idan kinga na miji ahanya ke  zaki kokarin ki matsa mai, bawai shi ya matsaba, wanan kuskurene sosai ki jira se shine ze matsa miki, sanan yawaita yin nafilolin dare, da rana, karatun alkur ani yawaita yin azkar din kwanciya bacci, da tashi safiya da maraice, yi addu o i, salatin annabi da sauran duk abinda ya dace, matukar kin rike Wannan abubu, to insha Allah, Allah ze tsare rayuwar, ze kareki daga duk wasu masifu, ko sharrin jinnu kona mutane, kuma lallai duk Wanda ze aureki zeyi alfahari da samunki matsayin matarshi, bayan haka Allah ze kawo miki miji na gari me addini da  tsoron Allah, insha Allah, sanan mutane ma zasuji dadin zama dake, Yayan da zaki haifama haka da kuma mijinki, kina raye, bayan baki Raye kuma,  zasuyi ta miki addu a domin siffarki ta siffantu dana mata na gari, da fatan zaki gane wanan kuma ki rike kiyi aiki dashi, Allah yai mana dacewa duniya da lahira,

0 Response to "Wa Yakamata na Aura"

Post a Comment