-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Me yadace Kiyi Kafin/Lokacin Aure

Me yadace Kiyi Kafin/Lokacin Aure

Me yadace Kiyi Kafin/Lokacin Aure. Gareku maza, masu mata daya ko biyu ko uku zuwa hudu. Kada ka sake Kayi aure ba tareda kanada tabbacin zaka sauke hakkinda Allah ya dorama ba, Kada ka sake ka karo aure ba tareda kanada tabbacin zakai adalci atsakaniba kuma zaka iya, Shin zaka iya yin adalcin tsakanin matanka idan ka kara aure, shin itama ta cikin kana bata hakkinta yadda ya kamata, shin karfinka yakai yadda zaka iya biyawa kowacce bukatarta, misali ciyar dasu, rashin lafiyar su dana yaransu, karfinka yakai yadda zaka iya daukar nauyin su, wani abinci daze ciyar da mace wahala yakemai, rabonta da dinki kuwa tun sallah, ko kuma agidansu kotaiwa kanta, amma ya tashi ze karo aure, wanan ba adalci bane, tayaya mata baza au daga hankalin su ba, wani lokacin ba kishi bane sunada gaskiyarsu, irin Wanan namijin idan mace tai musu bore ba laifi bane. Shin kanada ilmin da zaka ilmantar dasu su san addinin su, Dolene ka tabbatar kanada wadanan abubuwa kafin kace zaka kara aure, kara aure bawai gasar kwallon kafa bane, dole seka cika sharadai da Shari a musulumci ta yadda da na miji ya kara aure, sanan ya auransa, amma da yawa mazan Kawai auren sukeyi ba tareda sunsan wanan ba, to aji tsoron Allah. Ka zama mai koyi da annabi, yadda ya zauna da iyalansa, Kada ka auro yarinyar mutane ka ajiye agidanka amma ace kullum tashin hankalinta da rashin nutsuwarta kaine Wanda da ace diyar kace take wani gida yake aure akewa haka ba zakaji dadi ba, dole seka mataki, Kada kabar yarinyar mutane tana zubar da nawaye akanka ba tareda wani kwakwaran daliliba, Kada ka rinka zaluntar yar mutane, Wanan ba rayuwar musulunci bane, Kayi koyi Sa halayen Manson Allah, s a w, be taba cutar yar wani ba, be taba zalintar yar waniba, idan kanaso Kayi zaman takewa mai dadi da matayenka to wajibine ka nemi ilimin yadda manzon Allah ya zauna da matansa, Kayi koyi dashi sallalahu alaihi wasalam har taya matansa aikin gida yake yi, kaifa ka taba taya matarka aiki koda sau dayane, ka tabbatar cewa kanada ilmin addini domin wajibine ka koyar dasu, idan kuma kaki kabarsu acikin duhun kai, to lallai zakaiwa Allah bayani, domin yace yaku wadanda kukai imani ku tseratar da iyalanku daga wuta wanda wanan wutar makamashinta mutanene da duwatsu,Kayi adalci tsakanin Yayan su, Kada ka fifita wasu daga ciki kace Wanan ai Dan Amarya ne, kafison yaranta samada yaran uwar gidanka, ko kuma ai Wadanan yaran uwar gidanka ne ka fijin tsoranta akan na amaryar ka, don hakane kafi kula dasu da kyautata masu fiye dana amaryarka, Wanan zaluncine Sa rashin adalci, komai zakayi kamar yadda zakaiwa yaran amarya haka zakaiwa na uwar gidanka, sedai inda ya kasance yaran amarya ba lafiya ka siya magani, kace itama uwargida seka bata kudi wanan ba haka ake nufiba sedai idan basu da lafiya to yadda zaka kula dana wancan haka zaka kula Dana wanan, ka kwatanta adalci atsakani. Kayi hakuri da halayensu domin su masu raunine, bazaka taba hada hankakinka Dana su kace daya bane kaga dolene kai hakuri kaima, da juriyar yin afuwa to se a zauna lafiya. Babu wulakantacce awajen ubangiji semai wulajanta mata, kuma babu mai girma awajanshi semai girma masu, kaga kenan idan takamarka wulakanta yarinyar mutane to tabbas, kaima wulakantaccene awajan ubagiji. Kuma Manzon Allah s a w yace mafi Alkhairin acikinku shine Wanda yafi kyautatawa iyalanshi, kuma ni nafiku kyautatawa iyalainai, to kuyi koyi da Annabi s a w, gurin kyautatawa matanja, Kada Dan kanada dukiya, ka hana iyalanka, Sedai kaita bawa matan banza awaje, wannan ba karamar asara bace agareka, kuma Kayi aikin banza, matarka itace ya kamata ace itacen farkon wacca zata fara bada sheda akan kayutatawar ka kafin wani ya bayar, don haka ka tsaya tsayin daka domin ganin Kayi adalci ga matarka, ko matanka, domin kuwa idan bakai ba to lalle makomarka bazataima dadiba, da lahirarka, kuma zakaiwa Allah bayani, Allah yasa mudace

0 Response to "Me yadace Kiyi Kafin/Lokacin Aure"

Post a Comment