-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Zaman Aure a Wannan Zamani

Zaman Aure a Wannan Zamani

Zaman Aure a Wannan Zamani



Yadda ake zaman aure  bangaren tarbiyantar da yara da kula dasu, uwar gida ya dace ki kula da tarbiyar yaranki sosai ta kowana bangare, ki zamo me lura da duk wani motsi na yaranki acikin gida ko awaje, yar uwa ta kibawa  yaranki tarbiya tun suna kanana ki koya musu dabi a tagari, tmbawai sesun girma ba,yaro tun  yana karaminshi zakina yawan furta mishi ambaton Allah da kalmomi masu ma ana, kada kiga yaro karamine duk abinda kike yana gani, ki dabi antu da dabi u masu kyau, kada ki yawaita zagi ko fadar kalmomi marasa kyau, kada ki yawaita hantararshi ko dukan shi yayin da yai wani lefi, kiwaita shimasa Albarka da nema mai shariya, cewa Allah ya shiryeshi, kizamo mai kula da Sa ido akan yaro me yake aikatawa, ko me yake, meke damunshi, ki zama mai kula akan duk Wanda ze dauki danki, kada ki yawaita bari ana shigar miki da danki ko yarki makota, ko wani waje a Dade ba a dawoba, yayin da yaro ze kwanta bacci kiyi mishi addu a ki tofamai, idan ya tashi nanma kiyimai addu a ki tofamai, kada ki rinka barinshi da kazanta ajiki, tabbas wanan ma yana jawo hankalin me gida akan yadda kike kukamai da yaronshi. kizamo mai tsaftace yaro akoda yaushe karki barshi da kazanta koyane, haka kuma yayin da yara suka fara girma megida yanaso yaga ranshi anutse ga tarbiya, koda kuwa shi ba haka yakeba, kuma dama jigon tarbiya da iyaye take musamman ma uwa, yar uwa kizamo me koyawa yaranki dabi u masu kyau, amma dolene sekin sansu ahanya kuma kema dole sekin kasance mai nutsuwar, kizamo mai koyawa yaranki  zikirai da  ambaton Allah da addu oi  akoda yaushe.

Yayin da zasu kwanta baccima kisa ido akansu kitabbatar sunyi addu kafin sukwanta, kuma kema ki kara yi musu, ki kura da yanayin kwanciyar su ma ana yadda zasu kwanta, domin domin akwai ladubai na kwanciya, kada ki bari suyi rufda ciki yayin kwanciya, kisa su kwanta da hannun dama, sanan ki raba musu gurin kwanciya, maza da ban mata daban, idan akwai halima mata ma  daban, yayin da yaro yakai shekara shida ko bakwai akoya mai tashi sallah asuba anuna musu mahimmancin sallah asuba, sanan yayin da suka tashi daga barci  ki koya musu addu ar tashi daga bacci koda kuwa ana musu a makaranta ki yawaita tunatar dasu, ki nuna musu gaisar da mutane da safiya, idan sun tashi sugaida duk wani Wanda ya girmesu koda kuwa bakone, hakama addu a kafin cin abinci da angama, ko shiga bandaki, ki nuna musu girmama manya ko ina sukaje wanan zesa duk inda yaranki suka shiga bakida fargaba, uwar gida alokacin da akai baki kada kibari yaranki ana magana suna kallan bakin mutane ko suna tsomala baki acikin zance, wanan ba dabi a ce mai kyauba, yar uwa idan yaranki zasu futa kada ki manta da tuna musu addu, ki yawaita bincika ya yaranki suke karatu sunayi ko kuwa, kina sawa suna biya miki agida kinaji,ki yawaita bincika dakinsu ko jakarsu ta makaranta domin tsaro, kisa ido zirga zirgarsu da abinda zasu shigo miki dashi cikin gida, kada kibari suyawaita shiga makota barkatai, kada kibari su dinga yawo ko ina ba kangado, ki nuna musu tausayi da tausayawa mahaifansu, da kuma jinkansu, kina yawan jansu ajiki kina jin damuwarsu ba kiji awani wajeba, ki shaku dasu sosai. Lura da yara acikin gida da kula da tarbiyarsu, yana daga manya manyan matakai na dorewar aure har abada, domin kuwa mahaifinsu zeji dadi, kuma ze kara gamsuwa da  cewa hakika ya auro mace ta gari me tarbiyantar da yayanshi, hakan ze jawo miki kima da mutumci a idon megida, tareda dankon soyaiya mekarfi atsakaninku, bama iya shi kadaiba harda mutane, domin idan kika tarbiyantar da yaranki, to hakika ki haifar da alumna tagari wacca za a amfanu dasu, kuma ayi alfahari dasu.

0 Response to "Zaman Aure a Wannan Zamani"

Post a Comment