-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Sabbin Zafafan Kalaman Soyayya 2023

Sabbin Zafafan Kalaman Soyayya 2023

Sabbin Zafafan Kalaman Soyayya 2023

Kamar yadda muka saba kawo muku sabbin zafafan kalaman soyayya a kowace shekara, yau ma mun kawo muku sabbin zafafan kalaman soyayya 2023

A wannan karon mun kawo kalaman soyayya masu dadi, da kalaman soyayya na zamani, da kuma kalaman soyayya masu kara dankon kauna. 

Hakika so wani linzami ne da ke jan dukkan gangar jiki zuwa inda ya so, ki sani ya ke sarauniyar mata so da kaunarki sun mamaye dukkan illahirin sassan jikina ya zama linzami, ina rokonki da ki jani a hankali har zuwa fadar zuciyarki domin ki nada ni sarki a fadarki 

Ya ke haske da ke haskaka dukkan rayuwata, ya ke fitila da ke yaye dukkan dubu a gareni, ki kasance sanyi domin domin kawar da dukkan wani sauyin yanayi da ka iya shigowa rayuwata

Tattaunawa Tsakanin Masoya

Masoyina don Allah Karka manta dani koda ace bana darai kaimin alkawari zaka runka yawan tunawa dani, domin  banida wani tamkar ka, ka rikemin Alkawarin masoyina, akoda yaushe burina asa mana rana nazama matarka, zan zamo me biyaiya agare ka, zan kasance tare dakai aduk inda kake, duk inda kaje, zan zauna dakai koda kuwa a bukka ne,ina kuma godiya ga Allah daya bani mai kyawun tarbiya,Wanda ya zamo tirmi sha daka, hakiki, ka zamo min kariya, baka gazawa ga duk wasu bukatuna, nima duk abinda kake so zan maka, abinda ka sani zanyi ba jayaiya domin ka wuce haka, bazan taba son wani da na miji kamar kaiba, akanka zan iya komai kuma na shirya na bada komai. samun irinka da akwai wahala hubyna, ba zana jure ganin bacin ranka ba ko wani ya tabaka, ashirya nake na bada komai nawa akanka, kai kadai nake  dashi muradina kuma kai kadai nake kulawa babu kowa akalbina sekai rabin raina, ka zamo ni na zama kai mun zamto daya, tamakar jinin da yake gudana ajiki wanda Indan babu shi ba mutum, hakika ka cikemin gurbin abinda nai rashi daga rayuwata, kaunarka tasa nakeson abinda kake so koda banaso, haka nake kin abinda kake ki koda ina so, ina tsantsan ji dakai, ko cuta nake Kaine magani,

0 Response to "Sabbin Zafafan Kalaman Soyayya 2023"

Post a Comment