-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Kalaman Fira Tsakanin Masoya

Kalaman Fira Tsakanin Masoya

 Kalaman Fira Tsakanin Masoya

Barka da wanan lokaci, ya zoborodon zuciyata dake zoborodo lamirjen tsantsar kaunaka araina, ina fatan kana lfy mai martaba nasan zakai tunanin meyasa nakira ka  da mai martaba, kakai na kirakane domin kai kadai ne ke mulkin acikin zuciyata, bama iya mai martababa,  kai sarkine agareni dake iya sarrafa duk wata gaba dake yabanka da kaunar ka kaine gaba kuma ja gaba acikin rayuwata, kalmar ina sonka bazata taba wadatarwa da nuna ina sonkaba,  ina kaunarka fiye da yadda nake furtawa abakina, bazan rayu imbabu kaiba, domin kazamo wani bangare na jikina, Wanda idan babu kai babuni, kamar yadda ba a raba hanta jini,  duk lokacin da akace baka cikin rayuwata ze fiyemin sauki ace ina kabari, ina fatan ace mafarki na yazama gaske Wanda nakeyi akoda yaushe, da farin cikin dazanyi babu misaltuwa, haduwa dakai wani babban gamda katarne na samun wata babbar kyauta, da kowane yake samuba, nidai nayi sa a da masoyin gaskiya, na kwarai  wanda  ko wace mace  take burin samu. 

Azahiri da badini na kaine gwani, kuma ako ina nake duk inda naje nasan dakai, kana nan araina bana mantawa dakai, nice wacca ta shiga zuciyarka ta zauna zama daram ba futa, kuma bamai iya fidda ni duk tsananin wuya, kasani na kece raina awajan kawaye, har bana shakka saboda ina dakai. Soyaiyar dake tsakaninmu nida kai  tamkar da da uwa, shakuwar danai dakai yasa koda bakanan idan na tuna noka sena rinka ganinka a idona Kaine kadai zanyiwa dukkanin kalamai na domin kai na tanada, kuma Kaine nabaiwa dukkanin mukamaina domin kai kada ka cancanta, kuma Kaine nabaiwa dukkanin mukallaina ka rike domin na yadda dakai dukkan samari a kasanka suke basu kaika ba, idan har kananan to ba wanda nake gani sekai  domin basukai na tsaya na kallesuba sekai, basu kaika ba bazasu  taba kaiwa kamar ka ba ,Kaine na farko nakarshe agurina na daya, hadina dakai hadin Allah ne  wane wani  yace ze raba, ina kara godiya ga Ubangiji daya samin sonka acikin raina, fatan kasancewa tare dakai har abada hubbyna ina sonka.

0 Response to "Kalaman Fira Tsakanin Masoya"

Post a Comment