-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Bayani Game Da Bashin Da Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Bawa Daliban Najeriya

Bayani Game Da Bashin Da Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Bawa Daliban Najeriya

Bayani Game Da Bashin Da Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Bawa Daliban Najeriya 

 Shugaban kasar Najeriya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya sakawa dokar bai wa daliban Najeriya dake manyan makaratun da suka fito daga gidajen masu karamin karfi damar samun rancen kudi wanda babu kudin ruwa a ciki. 


DALIBAN DA SUKA CHANCHANCI KARBAR BASHIN; 

1, Kafin ka cancanci samun rancen sai da farko ka samu gurbin karatu a wata babbar makaranta ta jiha ko ta tarayya, walau jami'a ko kwalejin kimiyya da fasaha ko kwalejin ilimi ko kuma makarantar koyon sana'ar hannu. 

2, Bashin zai kasance na biyan kudin makaranta ne kawai za'a baka. 

3, Dole ne kudin da kake samu ko kuma iyayenka suke samu ya kasance kasa da naira dubu 500 a shekara. 

4, Dole ne dalibi ya gabatar da masu tsaya masa, akalla mutum biyu wadanda za su kasance ma'aikatan gwamnati da suka yi shekara 12 a aiki.

5, Dalibi zai iya gabatar da lauya wanda ya kai shekara 10 da aiki ko kuma wani ma'aikacin shari'a.

6, Idan dalibi a makarantar da ba ta gwamnati yake ba ba zai samu wannan rasnce ba.

7, Babu maganar wariya ko nuna bambanci ga wani dalibi bisa jinsi na mace ko namiji ko addini ko wata nakasa. 


JERIN DALIBAN DA BA ZA'A BAWA BASHIN BA

1, Idan ya kasance ka ci bashin Bankin Ilimin a baya kuma ka ki biya.

2, Idan har wata makaranta ta taba ko kuma wata kotu ta taba samunka da laifin rashin gaskiya ko zamba, to ba ka cikin wadanda za su ci moriyar tsarin.

3, Idan an taba kama ka da laifin da ya danganci miyagun kwayoyi, wannan ma zai hana ka samun rancen.

4, Idan har wani daga cikin mahaifanka, walau uwa ko uba ba su biya bashin da aka ba su ba na dalibtar to ba za a ba ka ba. 

5, Yadda za ka biya bashin

Yana daga cikin aikin Bankin Ilimin ya rika bibiyar wanda aka bai wa bashin ya san lokacin da zai gama karatun, da aikin yi wa kasa hidima har zuwa samun aiki domin tabbatar da mutum ya fara biya a lokacin da ya dace.

6, Bankin zai hada kai da inda kake aiki domin tabbatar da ana yankar kudin da ya kamata a rika sanya wa a asusun da ya ba ka bashin.

7, Duk wanda aka bai wa bashin zai fara biya shekara biyu bayan kammala aikin yi wa kasa hidima (NYSC).

8, Za'a rinka yankar kashi 10 cikin dari na albashinka ana biya.

9, Idan aikin kanka da kanka kake yi, wato ba a karkashin wani kake aikin ba, to gwamnati za ta rinka karbar kashi 10 cikin dari na yawan ribar da kake samu a duk wata, inda za ka rika kai kudin da kanka bankin; Kwana sittin da zamanka mai sana'ar kai za ka mika bayanan harkokin kasuwanci ko aikin naka, misali bankinka da wajen da kake zaune da abokan sana'ar da wadanda suke da hannun jari a ciki da sauran bayanai. 

10, Idan ka ki biyan bashin za a iya yi maka hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari ko tarar naira dubu 500 ko kuma a hada wa mutum duka biyu. 


DOKOKIN DA BASHIN YA KUNSA;

1, Karkashin dokar za'a kafa Bankin Ilimi na Najeriya, wanda shi ne zai rika tsarawa da sa'ido da kuma aiwatar da bayar da bashin karatun.

2, Bisa tanadin sabuwar dokar, dalibi zai iya samun bashin ne ta hannun ma’aikatar ilimi ta kasar, kuma ba zai fara biyan bashin ba sai ya samu aiki bayan kammala karatu da kuma hidimar kasa ta shekara daya (NYSC) ba.

3, Dalibai za su iya neman bashin ta hanyar makarantun da suke, inda makarantun za su shige musu gaba.

4, Za'a tantance dalibi a ga ko ya cancanci karbar bashin.

5, Dokar ba za ta amfani duk dalibin da zai yi karatu a wajen Najeriya ba, ko kuma mai karatu a makarantar da ba ta gwamnati ba. 

Wa 'yan nan sune cikakkun bayani Dalla-dalla game da yadda Gwamnatin Tarayya zata bawa daliban rancen kudi da babu kudin ruwa a cikin su. 


Marubuci: Comr Abba Sani Pantami, 


0 Response to "Bayani Game Da Bashin Da Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Bawa Daliban Najeriya"

Post a Comment