-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Mene ne AfriGo "Nigerian National Domestic Card Scheme"

Mene ne AfriGo "Nigerian National Domestic Card Scheme"

Mene ne AfriGo "Nigerian National Domestic Card Scheme"

Babban bankin Najeriya ya kaddamar da wani katin cinikayya na cikin gida mai suna AfriGo, wanda 'yan kasar za su rika amfani da shi domin yin dukkan hada-hadar kudi a fadin kasar.

Sunan tsarin da turancin Ingilishi "Nigerian National Domestic Card Scheme".

Yayin kaddamar da katin, gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ya ce za a rika biyan dukkan cajin kudi kan cinikin da aka yi da katin da Naira ne, sai dai idan ya shafi hada-hada da kasashen waje.

Mista Emefiele ya ce "Katin AfriGo alamar martaba ce ga Najeriya, kuma zai ba mu damar sauwaka wsa 'yan Najeriya tsadar da suke fuskanta wajen cinikayya a ciki da wajen kasar."

Ya kara da cewa 'yan kasar na iya ci gaba da amfani da katunansu da bankunan kasar suka ba su, sai dai ba za a ci gaba da biyan kudin caji da dalar Amurka ba kamar da

Source: BBCHausa_ https://bbc.in/3XEiyr3

0 Response to "Mene ne AfriGo "Nigerian National Domestic Card Scheme""

Post a Comment