-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

MENENE GSI RECOVERY

MENENE GSI RECOVERY

MENE NE GSI RECOVERY



Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar da ka’idoji kan tsarin nan na Global Standing Instruction, (GSI) wanda zai baiwa bankuna damar kwace kudaden wadanda suka kasa biyan rancen da suka karba a wasu bankuna. Babban bankin ya ce ka’idar GSI da aka samu ita ce inganta dawo da rance ta bangaren banki.

Tun daga ranar 1 ga watan Agusta, cibiyoyin hada-hadar kudi masu lasisi za su iya cire rance da suka ba mutum wadanda suka kasa biya daga duk wani asusu mai alaka da BVN.

Wannan yana nufin cewa idan kuna da rance tare da banki A kuma kun makara akan biyan ku, bankin zai iya cirar duk wani asusun ku da ke wasu bankunan, ko na mutum ɗaya ne ko na haɗin gwiwa - don dawo da rance.

Babban bankin na CBN ya ce an samar da wannan manufar ne domin bunkasa al’adar biyan bashi da rage rancen da ba a biya ba a tsarin banki, da kuma sa ido kan masu kasala wajen biyan rancen.

Karin bayani 

Wasu mutane sun dogara ne da sakon da suka gane na ciri musu kudi da aka yi Na #GSI_RECOVERY suna ganin kamar cewa bashin Covid-19 ne da aka basu suka fara cirewa toh gaskiya ba bashin Covid-19 bane idan kace bashi a wani banki ka kasa biya har lokacin daya yakamata ace ka biya bashin kake biya shine gwamnatin tarayya tayi doka game da wanda suka kasa biya zaa iya bin su duk asusun ajiyar da suka saka kudaden su domin kwace kudin da Suka gaza biya .

Ni kaina Ahmed El-rufai Idris na karbi bashi a #WemaBank kusan mafi yawancin ma'aikatan gwamnati suna karbo bashi daga bankunan don magance wata hidimar yau da gobe, kuma na kasa biyan bashin akan lokaci babban banki najeriya shine suka biyo ne Bankin #GTBANK suka kwace sauran kudin da ban biya su ba .

Duk masu yada irin screenshot din nan suna cewa ita ce shaidar su na cirar kudi da akayi ga wanda suka karbi bashin gwamnati ba gsky bane Nirsal Microfinance babu wanda suka cirar wa kudi daga asusun ajiyar sa .Ina fatan zaku fahimci bayanin nan nawa .

Daga:  Ahmed El-rufai Idris


0 Response to "MENENE GSI RECOVERY"

Post a Comment