-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

YADDA ZAKI HADA YAM BALLS

YADDA ZAKI HADA YAM BALLS

YADDA ZAKI HADA YAM BALLSAbubuwan bukata;

1. Tafasashen Doya

2. Dakakken Attarugu 

3. Kofi ko kifin gwangwani

4. Bayan kamshi

5. Kwai

6. Albasa

Yadda zaki hada;

Dafarko zaki samu doya iya yawan da kikeso ki fere ta ki yanka ta daidai sai ki dauko tukunyarki ki saka yankakkiyar doyanki ki saka gishiri ki daura a wuta. Idan ya tafasa ya dahu sai ki sauke ( kada ki bari doyarki ta dafe). Idan ta dahu sai ki tsameta da ruwan, ki dauko turmi sai ki jajjaga doyarki tayi laushi, idan tayi laushi sai ki samu bowl ki juye dakakkiyar doyarki. Bayan kinyi wannan, sai ki dauko dakakkiyar tarugunki da albasa, tafarnuwa, maggi, gishiri, da kuma sauran kayan kamshinki ki ki zuba, ki dauko kifinki shima ki zuba akai sai ki cakudasu duka tare da doyarki ki tabbatar sun cakudu sosai. Bayan sun cakudu sai ki dinga diba kina gutsurawa dai dai girman da kikeso sai ki mulmulasu kamar kwallo ki ajiye gefe akan tire. 

Daga nan sai ki dauko tukunyarki ta suya ki zuba mai aciki (groundnut oil) ki daura a saman wuta ki yayyanka albasa aciki ki barta ta soyu tayi brown sai ki kwashe albasar ki dauko hadin doyarki da kika mulmula ki saka shi a cikin hadin kwai da kika kada ki juyashi aciki ya raba koina sai ki jefa a cikin man suyarki ki barta ta soyu tayi brown, sai ki kwasheta

Shikenan yam balls dinki ta hadu sai ayi serving, zaki iya hada ta da ko wane irin sauce kike so kuma zaki iya cinta hakanan. Acid lpy


0 Response to "YADDA ZAKI HADA YAM BALLS"

Post a Comment