Yadda Zaki Hada Miyar agushi watau egusi soup , Miyar ridi wanda aka fi sani da sesame soup, Miyar ogbono watau ogbono soup, Miyar dankalin turawa, Miyar shuwaka
Yadda Zaki Hada Miyar agushi watau egusi soup , Miyar ridi wanda aka fi sani da sesame soup, Miyar ogbono watau ogbono soup, Miyar dankalin turawa, Miyar shuwaka.
Assalamu Alaikum,
Barkanmu da dawowa wannan shafi mai albarka dafatar Kun ilimantu da salon miyar da na kawo maku a shafin da ya gabata watau miyar kabeji hadi da nama.
A yau zan kawo maku kalolin miya guda biyar da ya mata ko wace mace ace ta sansu kuma ta iya sarrafa su. Ku biyoni domin ganin wannan salo da koyon yadda zaki hada miyarki tayi kyau ta kuma kara maki daraja a idon maigida.
Kalolin miyar da zan kawo maku a yau sune kamar haka;
1. Miyar agushi watau egusi soup
2. Miyar ridi wanda aka fi sani da sesame soup
3. Miyar ogbono watau ogbono soup
4. Miyar dankalin turawa
5. Miyar shuwaka.
1. Miyar agushi (Egusi soup)
Abubuwan bukata;
Agushi
Ganyen ugo
Stock fish
bushashen kifi
ganda
Maggi
Manja
attarugu
albasa
Naman saniya ko rago
Daddawa
Spices
Da farko zaki jajjaga attarugunki da albasa guri daya sai ki sa manja a wuta yayi zafi sai ki zuba attarugu, albasa da daddawarki ba da yawa ba. Ki soyasu kadan sai ki kawo egusinki ki xuba a ciki ki cigaba da juyashi har sai manja ya ratso jikin agushin ki ya taso sama sai ki kawo ruwan tafashen namanki ki xuba ki juyashi sosai sai ki rufe.
Sai ki dauko gandarkiki dama kin riga kin dafata sabida tayi laushi, Sai ki bude tukunyarki sai ki xuba gandar aciki ki kara ruwan zafi ki juya ki rufe bayan wasu mintina sai kisa naman ki sai ki juya bayan minti kadan kisa stock fish da busashen kifin ki ki juya ki rufe ki barshi y kara dahuwa sai kizuba maggin da kika tanada da kuma cray fish dinki dakakke ki juya sosai ki rufe. Xaki iya kara dafaffen ruwa kadan sai ki rufe ki barshi na tsawon mintuna kadan sai kisa spices dinki ki Kawo ganyen ugwu dinki da kika wanke ki tsane shi sai ki xuba ki barshi yayi minti biyar 5 sai ki sauke.
Shikenan miyar ki ta dahu, sai kiyi serving. Zaki iya hadda miyar da abubuwan kamar tuwon shinkafa ko na gari, Eba, sakwara, kafa, idan kuma kina raayi zaki iya hadashi da masa ko fankasau.
2. Miyar Ridi (sesame soup)
Abubuwan bukata;
Ridi (wasu sunfi saninshi da kantu)
Nama
Busashshen kifi
Albasa
Attarugu
Ugwu ko Alayyahu
Maggi
Gishiri
Thyme
Spices
Manja
Yadda zaki hada;
Da farko zaki wanke ridinki wadatacce ( ana son yanwan shi yakai kamar kofi day ) kishanya shi ya bushe. Bayan ya bushe Sai ki raba biyu, ki nika rabi, ki soya rabi har sai yafara kamshi, sai ki sauke kar yayi baki. Bayan wannan sai ki tafasa namanki ki saka maggi da spices saiki soya kayan miyarki acikin mai, zaki iya amfana da kowane kalan mai kikeso kiyi amfani dashi) saiki zuba namanki wanda kika tafasa ki sanya har da ruwan da kika tafasa naman acikin kayan miyar saiki sanya busashshen kifin ki, sai ki zuba ciki ki rufe tukunyarki ki barta ta dahu har na tsawon mintuna 15-20 saiki yanka ganyenki ki xuba ki barshi zuwa kamar minti biyar sai ki sauke. Shikenan miyar ki t dahu sai anyi serving.
Shima wannan miyar zaki iya hadata duk abunda kikeso ki hada.
3. Miyar Ogbono (ogbono soup)
Abubuwan bukata;
Nama
Danyen Kifi da busasshe
Ogbono
Ganda
Kayan miya
Man ja
Maggi da gishiri
Curry da tafarnuwa
Yadda zaki hada;
Da farko zaki tafasa namanki da gishiri, tafarnuwa, da albasa. Bayan ya dahu sai ki soya man ja amma kadan, ki zuba markadadden kayan miyarki a kai, su ma ba da yawa ba. Idan ya soyu sai ki zuba dakakken crayfish dinki cokali biyuu zuwa uku haka, sai ki zuba busasshen kifinki da kika gyara, ki zuba ruwa a kai. Bayan ta dahu zaki iya sa baking powder kadan dan tayi yauki sosai, dama kin sulala danyen kifi kin bare, kin cire kayar, kin gutsuttsura, shi ma sai ki zuba, ki rufe zuwa minti biyar ko goma shike nan miyar ki ta dahu, sai a sauke ayi serving.
Wannan miyar
4. Miyar dankalin turawa (potato soup)
Abubuwan bukata;
Dankalin turawa
Karasa
Kifin gwangwani ko danyen kifi
tumatir
attaruhu
albasa
gishiri da maggi
curry
Mai (man gyada ko manna)
Yadda zaki hada;
Da farko zaki markada kayan miyarki tumatir, attaruhu da albasa, saiki dora mai a tukunya yayi zafi saiki zuba markadanki. Bayan haka sai ki fere dankalnki ki yanka gida biyu a tsaye,sai ki kankare karas dinki ki yanka shi shima a tsaye. Idan kayan miyanki ya tafasa saiki zuba dankalinki a ciki kisaka maggi, gishiri da curry. idan dankalin ya dahu saiki zuba kifinki a ciki da karas saiki rage wuta ki barshi ya yi minti biyar zuwa takwas haka. Idan karas din yayi laushi saiki sauke. Shikenan miyar ki ta hadu sai serving.
Zaki iya hada wannan miyar da duk abunda kikeso ki hada dashi, aci lpy.
5. Miyar shukawa (bitter leaf soup)
Abubuwan bukata;
Nama
Shuwaka
Gyada ko agushi
Busasshen kifi ko na gwangwani
Albasa
Tafarnuwa
Kayan miya
Curry
Maggi da gishiri
Man ja
Dafarko dai zaki wanke shuwakarki da kanwa ko ki tafasa ta ki wanke ki cire dacin yanda za ki iya ci. Bayan kin wanketa, sai ki wanke namanki ki yanka albasa ki sa maggi da tafarnuwa da gishiri ki dora a wuta ki tafasa shi ya dahu da kyau. Idan ya dahu sai ki sauke ki soya sama sama acikin man da zakiyi miyi dashi. Bayyan ya soyu sai ki kwashe, sai ki dauko shuwakarki da kika nika ki kwabata da ruwa ki soyata tareda albasa a cikin mai, idan ta soyu sai ki jajjaga kayan miyarki, sannan ki soya su acikin manki. Idan kayan miyar ki sun soyu sai ki zuba ruwa ki sa maggi da tafarnuwa da citta, ki juye namanki da kika soya tareda kifinki da kika wanke, sai ki rufe ya dauko tsawon mintina goma zuwa shabiyar.
Idan miyarki ta kwaikwaya sai ki zuba shuwakarki da kika wanke, sannan ki juyashi sosai sai ki rufe ya kara minti biyar a saman wuta. Shikenan miyarki ta dahu sai ki sauke.
Zaki iya ci da duk rin tuwon da kike bukata, aci lpy.
A nan zan kawo maku karshen wannan salo namu na yin miya tareda fatar kun ilimantu kun gane yadda zaku hada waddan nan miya a saukake. Ku biyoni a shafi mai zuwa a inda zan kawo maku salo iri iri na sarrafa lemon sha a sawkake.
Nagode.
0 Response to "Yadda Zaki Hada Miyar agushi watau egusi soup , Miyar ridi wanda aka fi sani da sesame soup, Miyar ogbono watau ogbono soup, Miyar dankalin turawa, Miyar shuwaka"
Post a Comment