Manhajar Whatsapp ta tsaya cik da aiki a Najeriya - shin sakonninka na shigowa?
Manhajar Whatsapp ta tsaya cik da aiki a Najeriya - shin sakonninka na shigowa?
Manhajar Whatsapp ta tsaya cik da aiki a Birtaniya da Najeriya wasu sassan duniya.
Masu amfani da manhajar, wadda mallakar kamfanin Meta ce, sun ce sun fara ganin matsalar ce tun kafin ƙarfe 8 na safe agogon GMT a ranar Talata.
Fiye da mutum 12,000 ne suka wallafa ƙorafi kan hakan cikin ƙasa da awa ɗaya, a cewar sashen fitar da bayanai na manhajar.
Mutane da dama sun yi ƙorafi a shafukan sada zumunta cewar ba za su iya aika saƙonni ba
A Najeriya ma mutane da dama ne Whatsapp dinsu ya daina aiki, inda har wasu suka dinga kashe wayoyi suna kunnawa da zaton matsalar daga wayoyinsu ne.
Akwai mutum biliyan biyu da ke amfani da manhajar WhatsApp a faɗin duniya.
Kuma manhajar na ɗaya daga cikin waɗanda aka fi amfani da su a Birtaniya da ƙasashe irin Najeriya.
Copy: BBChausa
0 Response to "Manhajar Whatsapp ta tsaya cik da aiki a Najeriya - shin sakonninka na shigowa?"
Post a Comment