-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Jarumai 10 da sukafi kudi a Kannywood 2023

Jarumai 10 da sukafi kudi a Kannywood 2023

Jarumai 10 da sukafi kudi a Kannywood 2023



(1). Ali Nuhu

Ali Nuhu jarumi ne kuma darakta ne a masana'antar Kannywood, wanda aka fi sani da Sarki Ali, ambasada ne na akalla kamfanoni guda bakwai a Najeriya cikinsu akwai Glo, Omo, Samsung da dai sauransu.

Bayan kungiyar Kannywood da Ali Nuhu yake taka rawa akwai kuma kungiyar Nollywood dake kudancin kasar nan wadda

dan wasan yake nuna bajintarsa a can. Jarumin yayi fina-finai a kamfanin Kannywood sama da guda dari, irinsu Jinin Jikina, Matar Aure, Gani Gaka, Mansoor, Adamsy, Dawo Dawo daidai sauransu.

Sannan kuma jarumin an nuna shi a fina finan Nollywood irinsu, Last Fight to Abuja, Memories of my Heart, Beautiful

Soul, Hamza, Brothers Apart, Widow Tears, Royar Treasure da dai sauransu.

Wannan dalili ne yasa jarumin ya zama na farko a cikin jaruman da suka fi kudi a masana'antar ta Kannywood.


(2). Adam A Zango

Adam A Zango mawaki ne kuma jarumi wanda aka fi sani da Prince Zango, Yana da wani katafaren gida a jihar Kaduna, yana kuma da masoya da yawan gaske.

Adam A Zango ambasada ne na kamfanin MTN, a shekarar 2016 Adam A Zango ya wallafa wani rubuta a shafinsa na Instagram cewar ya bar fim, inda ya ce zai koma bangaren waka da shirya fina-finai, sai dai kuma wani labari ya fito daga makusantansa cewa yayi amai ya lashe, Zango yayi fina finai shima sama da guda dari irinsu Nas,

Gwaska, Basaja, Gamdakatar da dai sauransu. Wannan ne ya sanya jarumin Adam A Zango ya zama na biyu a cikin jerin

jaruman.


(3) Rahama Sadau

Rahama Sadau (born 7 December 1993) is a Nigerian actress and filmmaker. She was born and raised in Kaduna. Awards: Best Actress (Kannywood) (2014), Best Actress (Kannywood) (2015), Best African Actress (2017)

(3). Dauda Kahutu Rarara

Dauda Kahutu Rarara wanda aka fi sani da Rarara, mawaki ne na siyasa, wanda yake da kusanci da manyan 'yan siyasa na kasar nan, an bashi mukamin babban darakta na mawakan shugaban kasa Muhammadu Buhari a lokacin yakin neman zaben shugaba Buhari a shekarar 2019, Wannan suna da kuma daukaka da Dauda Kahutu Rarara yayi shine yasa ya zama mutum na uku a cikin jerin wadanda sukafi kudi a kungiyar ta Kannywood.


4. Nura M Inuwa

Nura M Inuwa mawaki ne a bangaren soyayya, yana daya daga cikin masu kudin kungiyar Kannywood, yana fitar da wakoki

masu yawan gaske kowacce shekara, kyakkyawa ne, kuma shine na hudu a cikin jerin jaruman.


(5). Halima Atete

Halima Atete jaruma ce a masana'antar Kannywood, ita ce ta biyar a cikin jerin wadanda suka fi kudi a kungiyar ta Kannywood, sannan kuma ita ce ta daya a cikin jarumai mata.


(6). Sani Musa Danja

Sani Musa Danja wanda aka fi sani da Sani Danja shine ya zo matsayin na shida a cikin jerin jaruman, jarumi ne kuma mawakin siyasa, yana da wani katafaren gida a babban birnin tarayya Abuja.


(7). Sadiq Sani Sadiq

Sadiq Sani Sadiq wanda aka fi sani da Gambo Uban Tani, yana daya daga cikin wadanda suka fi kowa iya kwalliya a cikin

jaruman Kannywood, sannan ya karbi lambar yabo ta gwarzon dan wasa a kungiyar, hakan ya sa ya zama na bakwai a cikin jerin jaruman.


(8). Nafisa Abdullahi

Nafisa Abdullahi ita ce ta zo ta takwas a cikin jerin jaruman da suka fi kudi a kungiyar ta Kannywood, sannan kuma ita ce ta biyu a cikin jarumai mata a kungiyar.


(9). Hadiza Gabon

Hadiza Gabon jaruma ce ita ce kuma ta zo ta tara a cikin jerin jaruman sannan kuma ita ce ta uku a cikin mata, Tana daya daga cikin manyan jaruman da suke son ganin sun taimakawa al'umma.


(10). Aisha Aliyu Tsamiya

Aisha Aliyu Tsamiya wacce aka fi sani da Aisha Tsamiya, kyakkyawa ce ta gaban kwatance tayi fina-finai masu tarin yawa, ita ce ta samu nasarar zuwa ta goma a cikin jaruman sannan kuma ita ce ta zo ta hudu a cikin jarumai mata na masana'antar ta Kannywood.

0 Response to "Jarumai 10 da sukafi kudi a Kannywood 2023"

Post a Comment