-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Dalilanda ke hana mace samun miji da wuri

Dalilanda ke hana mace samun miji da wuri

Dalilanda ke hana mace samun miji da wuriDAGA DALILAN DA SUKE JANYO WA MACE JINKIRIN AURE ! 


Cuta, musamman kamar cutar Aljanaye, da kuma asiri. 


KARATU, wata burin ta kenan ko na iyayenta ko danginta shine tayi karatu mai tsawo. 


KADDARA, wata ita kuma jarrabawar ta kenan kuma daga wurin UBANGIJIN ta bai kaddara mata aure da wuri ba, kuma hakan alkhairi ne a gare ta. 


Wasa da dama, wata jinkirin aurenta na rataye da wasa da dama ne da son ZUCIYA na ta ko na iyayenta, sai tayi karatu ko tayi aiki da sauran su.


Akwai rashi, wata kuma tsananin rashi ne miji kuma sai ya nuna bai iya jira har sai sun samu abun aurar wa, wata kuma rashin da talauci yayi tsanani maza ko kulata ma ba sa wani yi. 


Wata kuma tawaya take da shi abisa halittar ta, kokuwa irin dai haka nan ba ta da kyau dss, wani abun ba zai furtu ba, ina fatan kun gane? 


Wata kuma a farkon yanmatancin ta ko a makaranta tayi wasa da maza, me nake nufi ba ta kama kanta ba, ta zamo ballagaza, duk wanda yazo neman auren ta ba shaida mai kyau, duk da in ta tuba ta gyara shikenan UBANGIJI mai afuwa ne, amma yanayin bakin mutane da sauran su kuma akwai wata dabi'a ta mutane ko da ta tuba in sun dinga nanata abinda ya wuce wannan ba daidai bane.


Da dai wasu dalilai.


Daga karshe abinda za'a ja hankalin yanmata musamman masu tasowa shine, darajar mace ta zamo mai Kyakkyawar dabi'a da kuma ilmi sa'annan ta koyi sana'a, sai kuma tayi aure a wannan lokacin da ake ribibin ta domin in ya wuce za ta zamo ba kowanne namiji bane yake da muradin auren kamarta kuma zai zamo mafi rinjaye ne cikin maza. 


Riko da sana'a da ilmi yana da kyau zai taimake ki wajen ko buɗe islamiyya kina karantarwa ko kina karantar da boko ko kina sana'ar ki, zai kara miki kima da daraja a YANMATANCI da gidan miji. 


Kuna daukar darasi abisa kuskuren wasu da suka tafka ya zamo musu matsala sai ku kiyaye kuma ku roki ALLAH dacewa a duniya da lahira. 


Daga karshe iyaye masu sauran ra'ayin hana yara aure ko saboda karatu wannan abu ne da Yakamata a duba duk yarinyar da ta nuna aure take so ku sani yarinya ce ta kirki wata sai dai ta kama Bin maza ko aikata madigo da sauran su.


Kuma a lura ya'yan masu kuɗi da kuma boko ko masu mulki su ma yanzu sun sassauto daga wannan ra'ayin aurar da ya'yan su suke su kammala karatu a gidan miji ko su ba su jari, wasu kam ma su suke neman musu mazan su basu aiki ko jari domin babu abinda yafi daraja da mutunci kamar mace a gidan mijinta kuma kwanciyar hankalin iyaye ne, ku lura da kuma ko irin salon matar shugaban kasar mu A'isha Buhari lallai ciki akwai abin koyi kuma akwai riko da Kyakkyawar tarbiyyar Muslunci iyaye da kakanni, in za kuce dama  ai ta samu akwai yarta da ta aurar tun kafun hawa mulki yar karama daidai gwargwado. 


Wani lokacin wata za ka ga nutsassiya ce jinkirin da kuma wasu burace-buracen shi ya janyo ta ga fadawa wata hanyar. 


Ku lura da kuma har yan boko akida da suke aure YANMATA da suke aura yan daidai, Yakamata mata mu yiwa kanmu wa'azi mu fahimci gaskiya mu natsu a cikin gaskiya daman dole watarana zuciya taji kamar ba ta so kuma karbarta shine kwanciyar hankali da dacewa na rayuwa duniya da lahira, in aka ki ta nadama za'a faɗa.


Ko matasan mu da suke zuwa aiki birane za ka ga fa dayawan su ana ba su mata acan har da wasu alkawura amma sai su dawo gida su zaɓi yarinya yar dai-dai yar ma secondary wata diploma suje su aura su tafi da ita, su kaita suna lallaba rayuwa, wani ya sanyo ta makaranta wani ko ya sama mata yar sana'a a gida, wani kuma aiki wani kuma ta zauna ta kula da tarbiyyar yara da aurenta. 


Yakamata mu natsu sosai muyi nazarin rayuwa, ko da mu munyi kuskure, kar mu bari ya faɗa akan kannen mu ko ya'yan mu.


Duk wanda wannan rubutu ya bata wa rai yayi hakuri, ya yafemun. 


Assalamu alaikum. 


1 Response to "Dalilanda ke hana mace samun miji da wuri"