-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Yadda Ake zama Da Miji Mai Tafiye Tafiye

Yadda Ake zama Da Miji Mai Tafiye Tafiye

Yadda Ake zama Da Miji Mai Tafiye Tafiye

Farko dai shi miji Mai tafiye tafiye har ga Allah bashida dadi domin a lokuta da dama zaka nemeshi ka rasa sannan zakaji a ranka shikenan kullum mutum baya Zama a gidansa kullum Yana kan hanya zakiji duk kin damu Amma hakan bashine mafita ba yar uwa idan Allah ya baki miji mai tafiye tafiye ba bacin rai Zaki rikayi a kullum ba hakuri zakiyi kuma wannan hakurin shine kawai zakiyi kici nasara sannan ki dinga yimasa addua a kullum da fatan alkhairi Allah ya bashi abinda yaje nema kuma ya dawo miki dashi gida cikin koshin lafiya idan yyi tafiya kafin ya dawo ki gyara gidanki ki gyara jikinki Kiyi lalle Kiyi kitso idan kinada yara ki shirya su tsaf suyi kyau yanda Mijinki zaiji dadi idan ya gansu Kiyi masa  girki mai dadi sannan idan yayi tafiya ko Yana kan hanya duk bayan awa daya ki kirashi kiji lafiyarshi da kuma inda yake sannan ki dinga daukar wanka Kiyi pictures ki dinga tura masa harda sexy ones hakan zaisa yaji ba wata da yake shaawar gani idan bake ba sannan zaiji Kamar ma ya fasa tafiyan ya dawo gida...kawai dai yabar gidane Amma gangar jiki kawai ya fita da ita amma ruhinsa Yana gidan sannan kada ki nuna masa bakiji dadi ba a lokacinda zaiyi tafiya ki nuna masa farin cikin ki sannan Kiyi fatan alkhairi a gareshi wadannan abubuwan ne kawai zakiyi ki zauna da Mijinki lafiya Amma sai kinyi hakuri gaskiya kuma ai tafiye tafiyen da yakeyi domin ku yakeyi so that a samu abinda zai rufa muku asiri na yau da kullum Allah yasa mu dace.

0 Response to "Yadda Ake zama Da Miji Mai Tafiye Tafiye"

Post a Comment