-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

YADDA AKE ZAMA DA KISHIYOYI BIYU KO UKKU

YADDA AKE ZAMA DA KISHIYOYI BIYU KO UKKU

YADDA AKE ZAMA DA KISHIYOYI BIYU KO UKKU

MENENE KISHI?  Kishi wani abune  dake zuciya wanda ke nuni da qi akan tarayya kan wani abin so. Sannan kishi halitta ce wacce ubangiji ke halittar bayinsa da ita namiji ko mace,ba'a canza ta,sai dai yakan bawa wani da sauki wani kuma a bashi me zafi.To duk inda bawa ya samu kansa aciki sai ya zama mai haquri da taka tsantsan musamman bangaren mata.Da yawa mata kan Gaza mallakar Kansu in an zo batun kishi.

Kishi halal ne. Mutukar zai taimaka wa mace wajen neman yardar Allah ta hanyar zage damtse wajen yawaita ladabi da biyayya da kyautata wa mijinta, kuma kishi yakan zo da ma'anar "GASA" KO TSERE DA JUNA" atsakanin matayen dake karkashin namiji guda. 


Kowacce takan yi kokari wajen ganin ta kula da hakkokin mijinta fiye da sauran abokan zamanta, domin samun cikakkiyar soyayya daga gareshi, kasancewar ita zuciyar 'dan Adam an horar da ita ne bisa son mai kyautata mata, da kuma Qin mai munana mata.

Ya yan uwana mata ina kira a garemu da mu riki kishiya a matsayin yar uwa. Domin a tunani na abokiyar zama ce da kuma taimakon kai idan kin dace.


Abin lura anan shine zai iya yiyuwa baki da lafiya ko kuma wani lalura wanda zaki bukaci taimakon gaggawa, itace mafi kusa dake kafin ki nemi wani.


In nace taimakon gaggawa ina nufin inke ma'aikaciya ce kuma kina da ya'ya kinga zaki iya barinsu a gida kije ki dawo batare da tunanin zata azabtar dasu bayan idonki ba.


Ko baki da lfy zata taimaka ta wani fannin . Ga lura da yara  dafa abinci uwa uba kula da maigida dama sauran bukatun yau da kullum.


Lallai kishiya ba tada dadi  amma in mun dauka da zafi. Don anawa hangen inkin zauna lfy da kishiya kema kanki zaki fi jin dadi da samun kwanciyar hankali domin baki  da wani tunanin munafuncin da za'a kulla miki a wurin maigidanku.


Matammu na daukar abokiyar zamansu ne a matsayin abokiyar gaba koda kuwa ba su ma san ta ba ba su taba zama da ita a wuri guda ba, wata gwara mutuwarta ma da kishiya, ba ta da wata magana mai dadi game da ita koda ba su taba ganin juna ko ma'amalla tare ba. Ita kawai kishiyar za ta cutar da ita, ko za ta kore ta, ko za mayar da 'ya'yanta bare.

.

Irin wadannan surutan ke zagawa su kai kunnen amarya har ta fara daukar mataki kafin ma ta shigo gidan, don ta ji cewa ga abinda uwargidarta ke fada a kanta. Qila ma uwayenta su qara mata da nasu in ba an sami gidan qwarai ne ba. Asalin amarya kan shigo ne ba ta san komai ba, ba ta ma san yadda za ta yi ba.

.

Duk abinda da aka gaya mata da shi za ta zo kuma a kansa take sai in ta ga sabanin haka, wanda wannan kuma yakan dan dauki lokaci kafin a tabbatar.


1.Jahilci: mata da yawa sun jahilci hikimomin da suka sa Allah Ya yi umarni a 

Qara aure, kamar rage yawan zawarawa da 'yammata, da kuma yawaita zuri ar 

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, domin da za su kalli wannan 

da kishinsu ya ragu.

2. Mummunan zato: yawanci uwar gida ta na tarbar amarya da mummunan zaton 

cewa za ta rainata, haka ita ma amarya ta kan zo da mummunan zaton cewa ba za 

su yi zaman lafiya ba da uwar gida, wannan sai ya sa daga zarar sun hadu babu 

wuya sun yi rigima. Amma idan da ace kowacce za ta tarbi kowacce da 

kyakykyawan zato, har ta ga kamun ludayinta da ba'a samu matsala ba. 

3. Rashin adalci daga wajen namiji, yawanci maza su kan karkata zuwa amarya, 

wannan sai ya haddasa fitina, saboda uwar gida za ta ce ba ta yarda ba, sai dai abin 

da ya kamata mata su fahimta shi ne, babu yadda za'a yi namiji ya hada mata biyu ukku ko hudu

face sai ya fi son wata daga ciki Amma Kuma hakan bazaisa a danne haqqin wataba aba wata ba daga, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya 

zauna da mata tara kuma ya fi son nana A'isha, har ma mutane sun fahimci haka, 

wannan ya sa idan za su yi masa kyauta, sukan kirdaji ranakun da yake dakinta, 

don sun san kyautarsu za ta fi karbuwa a ranar, don haka idan kika ga mijinki ya fi 

son kishiyarki, ki yi masa uzuri kar ki tada fitina, sai dai sharia ta hana rashin 

adalcin ya fito a hidimomin yau da kullum. 

4. Munafukai, masu cece-kuce, idan da ace kishiyoyi za su daina daukar gutsuri tsoma, ta yadda idan suka ji magana za su tabbatar da ita kafin su yi hakunci ga 

kishiyarsu, da hakan ya rage kawo matsaloli. 

Idan har wadannan matsalolin za su warware, ina ganin za'a samu kishi mai tsafta.

Ita kishiya ko guda dayace sai kinyimata karatun kanta balle biyu ko ukku ko wacce da halinta ko wacce da abinda ke ranta zuwa gareki dole sai kinyi taka tsantsan karki kuskura ki fadama wata maganar wata karki zama mai hadin fada atsakaninku kizauna da kowa da zuciya daya Kar asameki cikin masu karamar magana karki cutar da kowa cikinsu kedai ki kiyaye abinda mijinki yakeso da Wanda bayaso kiriqa diyansu tamkar diyanda Kika Haifa da cikinki karki kuskura don kinyi fada da kishiyarki ki hada da diyanta Sam wannan ba aikin hankali bane sannan Ya zama wajibi ga duk matar dake son rabauta alahira ta kiyayi zurfafa kishi (wato baqin kishi) wanda ke makantar da zukata ya raba mutum da imaninsa. Da zarar kinji alamar hassada azuciyarki game da abokiyar zamanki, ki nemi tsari daga sharrin Shaidan, sannan kiyi mata addu'ar alkhairi. Nan take zakiji hassadar tabar zuciyarki.

0 Response to "YADDA AKE ZAMA DA KISHIYOYI BIYU KO UKKU"

Post a Comment