-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Matsaloli Dake Tattare da Auren Namiji Mai Mata Da Yara da kuma hanyoyin magancesu

Matsaloli Dake Tattare da Auren Namiji Mai Mata Da Yara da kuma hanyoyin magancesu

Matsaloli Dake Tattare da Auren Namiji Mai Mata Da Yara da kuma hanyoyin magancesu

Maza ma ana barinsu da yara kamar yadda ake barin mata zaurawa dasu.

Wasu mazan sukan rabu da matansu ko dai matan suce bazasu tafi da yaran mijin ba, ko shi mijin yace bazata tafi masa da yara ba. Wasu kuwa mutuwa ake yi a barsu da yaran.

Irin wadannan mazan idan sun tashi aure suna sone suga sun auro matar da zata kulan musu da yaran nan dake gabansa musamman idan yara ne. Shi yasa duk macen da take son auren irin wannan namiji to ta kwana da sanin cewa: 

Dole ne ki tabbatar da cewa kin yi shawara da manyanki da kuma nazari ke kanki na iya rayuwa auren a hakan.

Shawarwarin da zaki samu daga wajen magabatanki zasu miki amfani matuka.

Yanada da kyau ki fahimci irin yaran da zaki zauna dasu, ma'ana wani irin tarbiya aka basu a baya. Domin ta haka ne zai taimaka miki wajen gano yiwuwar iya aurensa ko hakura da auren nasa.

Kada ki manta su irin wadannan maza duk irin soyayyar da zaki nuna musu muddin bazaki kular musu da 'ya'yansu ba bazaku jitu ba. Don haka kada ki duba soyayyar da kike masa kadai, auna da wanda kike yiwa yaran nasa shine zaman lafiyarki idan kunyi aure.

A irin wannan yanayin bama lalle bane yaran nasa suyi maraba dake daga farko ba. Amma yadda zaki yi mu'amala dasu shi zai sa suji suna kaunarki. Don haka ki saka aranki zaki iya fuskanta tirjiya daga wajensu a farkon shigowarki.

Haka nan idan kina son more aurenki babu ruwanki da abunda ya raba mijin da zaki aura da uwar yaransa. Sai dai yana da kyau ki samu alaka na fahimta da ita ganin idan kina da matsala da ita daga wajen tana iya shirya miki abubuwan da zai iya shiga tsakanin ki da yaran yazo ya shafi zamanki da mijin. Don haka kiyi nazarin matan nan nasa idan a gari daya kuke bazata zamemiki matsala ba bayan aurenki.

Dole kuma zaki zama mai hakuri. Domin irin wannan mazan idan sun shigo gida hankalinsu na wajen yaransu har sai sun gama hidima dasu kamin su waiwayoki. Sau tari idan dai yaran suna tare daku bazaki samu kulawar da kike so ba har sai idan sunyi nisa.

Wadannan wasu kalubale ne da suke tattare da auren namiji mai yara a gabansa da ya kamata kisansu, kiyi shirinsu, kamin ki tinkaresu.

0 Response to "Matsaloli Dake Tattare da Auren Namiji Mai Mata Da Yara da kuma hanyoyin magancesu"

Post a Comment