-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Mata 10 da Suka fi Kowa Kudi a Kannywood 2023

Mata 10 da Suka fi Kowa Kudi a Kannywood 2023

Mata 10 da Suka fi Kowa Kudi a Kannywood 2023

Najeriya itace kasar da tafi ko wace kasa yawa a faɗin Africa inda kididdiga ta bayarda cewa kasar Najeriya nada yawan jama'a fiye da miliyan dari buyu 200,000,000 hakan ya bawa kasar damar samun ciniki a duk hada-hadar kasuwanci da akeyi a ƙasar. Al-kalumma sun bayyana cewa ƙasar nada yawan kabilu fiye da dari uku da hamsin, saidai yare uku ne akafi yawanyi a kasar inda a hausance ake kiranshi da "WAZOBIA" wato yaren Yarbanci wato Yoruba, Yaren Hausawa wato Hausa da kuma Yaren Inyamuranci wato Igbo. a ƙasar kididdiga ta bayyana cewa Hausa itace yare da yafi yawan jama'a a ƙasar.

Kasantuwar Hausa yare mafi yawa a ƙasar hakan ya bayarda damar samun nasarar ga duk dan kasuwarda ke jin harshen, sana'ar fim ko wasan kwaikwayo na daya daga cikin Sana'o'i da bada riba da kuma daukaka a ƙasar Najeriya, a ƙasar akwai manya-manyan masana'antun fim ko wasan kwaikwayo da sukayi fice inda suka hada da NOLLYWOOD da Kuma KANNYWOOD. 

Kannywood masana'anta ce dake amfani da harshen hausa domin fadakarwa, ilimamtarwa da kuma nishadantarwa acikin wasan kwaikwayo, masana'antar nada kwararrun Furodusoshi, Daraktoci, Jarumai maza da mata da duk wani bangaren dake aiki a masana'antar domin isarda sako zuwaga yan kallo.masana'antar kannywood nada cibiya ne a kanon dabo dakea ƙasar.

Bazamu cikaku da sururtu ba zamuje ne kai tsaye domin amsa maku tambayarku da muke samu a ko yaushe wato "Mata 10 da Suka fi Kowa Kudi a Kannywood" nasan zakuyi murna sa kuma farin ciki idan muka amsa maku wannan tambayar. Shin kai masoyi kallon fina-finan kannywood ne? Idan amsar taka ta kasance "YES" to biyo mu acikin wannan kasidar tamu mai albarka mai taken Haskenews.


Rahama Sadau

Idan ana maganar masana'antar kannywood to babu kawa dole ne a zayyana sunan wannan jarumar duba da irin ci gaba da kuma nasarori da wannan jarumar ta kawowa masana'antar, haka kuma baza'a cire sunan taba idan ana maganar mata mafi kyawo a masana'antar bata kare ba idan ana maganar Mata 10 da Suka fi Kowa Kudi a masana'antar al-kalumma sun nuna cewa Jaruma Rahama Sadau sune sahun gaba.

An haifi jarumar a ranar 7 ga watan Disamba na shekara ta alif dari tara da casa’in da uku (7 December 1993) a unguwar Sarki dake cikin garin Kaduna a Najeriya. Rahama Sadau ta shiga a masana’antar Kannywood a shekarar 2013, Jaruma Sadau ta samu fice bayan fitowar ta a wani shiri mai suna “Gani Ga Wane” tare da Jarumi Ali Nuhu.


Fati Washa

Jaruma Fatima Abdullahi wadda akafi sani da Faty Washa na daya daga cikin kyawawan mata a masana'antar kannywood, jarumar tayi fice sosai da kuma nuna kwarewa aduk shirin fim da ta fito, al-kalumma sun bayyana cewa jarumar nada kananan shekaru kuma batayi aureba wato allurace cikin ruwa... Ayau idan ana maganar Mata 10 da Suka fi Kowa Kudi a masana'antar kannywood to tabbas jaruma Faty Washa sune a sahun gaba.

An haifi jaruma Faty Waha  a ranar 21 ga  watan Fabrairu, 1993, a jihar Bauchi, jarumar tayi fice ne a wani shiri data fito a tsakiyar manyan jarumai irinsu Adam A. Zango da Jamila Umar Nagudu.


Nafisa Abdullahi

Nafisa Abdullahi Jaruma ce mai dunbin masoya duba da irin kwarewa da takeda ita dakuma nagarta acikin masana'antar jarumar ta kara farin jini a shekarar 2020 zuwa yanzu inda ta taka rawa a cikin kayataccem shirinnan na fitaccen Darakta Malam Aminu Saira. A shekarar 2022 an maye gurbin Jaruma Nafisa Abdullahi da Jaruma Fati Washa bisa ga wasu dalilai. Wani abin burgewa sa jarumar shi ne fara'a da kuma son jama'a dake yi. Jarumar nada lamba acikin jerin matan kannywood 10 da sukafi kudi a wannan shekarar.

An haifi Nafisa a ranar 23 ga watan January a shekara ta dubu daya da dari Tara da casa'in da buyu 1992. Nafisa ta fara harkar fim  tana da shekaru goma sha takwas 18, fim din da ya fito da ita shine "SAI WATA RANA" a 2010 karkashin FKD PRODUCTION Na fitaccen Jarumi, Furodusa kuma Darakta Ali Nuhu.


Hadiza Gabon

Hadiza Aliyu wadda aka fi sani da Hadiza Gabon An haife ta daya 1 ga watan Yunin shekara ta 1989 a Libreville dake kasar Gabon, Na shafe shekaru a masana'antar kannywood banga jaruma da take burgeni kamar jaruma Hadiza Gabon, Gabon nada kwarewa wajan isarda sako zuwaga yan kallo fiye da sauran jarumar a wajena.

Jaruma Gabon ta samu shiga masana'antar ne bayan ta bar kasarsu Gabon zuwa jihar Adamawa, daga baya kuma ta tashi daga Adamawa ta koma Kaduna. Domin shiga a cikin masana'antar kannywood tare da dan uwan ta. Jarumar ta samu damar ganawa da Ali Nuhu kuma ta nemi taimakonsa na ya kaddamar da ita a matsayin 'yar fim. Hadiza ta fara fitowa ne a shekarar 2009, cikin wani shiri mai suna "Artabu". Ayau jarumar na daya daga cikin mata goma 10 dakeda arziki a masana'antar.


Aisha Tsamiya

Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya da akafi sani da Aisha Tsamiya an haife ta a shekarar 1992 a ƙaramar hukumar Nasarawa ta jihar Kano. Idan an neman jarumar masu kamun kai da kuma nagarta to tabbas babu makawa Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya su ne a sahun gaba, Tsamiya nada burin zama fitacciya a masana'antar kannywood sai dai kash akwanannan jarumar tayi Aure.

Aisha tsamiya ta zama matsayi na goma a shahararren film din salma, hakika har yanzun Aisha tsamiya tana daga cikin matan da tauraruwar su ta dade tana haskawa a masana'antar kannywood. Jarumar ba fim kawai takeba Daraktacw kuma Furodusace. Duk da jarumar tayi aure bazamu iya cire sunantaba daga cikin Jarumai mata da suka fi kowa kudi a masana'antar kannywood duba da irin alherinda yakeyi ga al'umma.


Maryam Booth

Jaruma Maryam Ado Muhammad wadda akafi sani da Maryam Booth, an haifi Maryam a watan OKtoba ranar 28 a shekarar 1993, Zainab Booth itace mahaifiya ga jarumar, duba da zamani masana'antar na bukatar hazikan jarumai irinsu kuma jajirtacci. Baya ga harkar fim kuma, Maryam na da kamfanin kayan kwalliya na ta mai suna MBooth Beauty Parlour.

A yau idan ana maganar jarumai wadanda ke haskakawa a masana'antar kannywood to tabbas Maryam Booth sun sahun farko, duk da zalunci da wani yayiwa jarumar na nuna hoton tsiraicinta hakan baisa tayi kasa a gwiba wajan fitoda sakonninda takeso ta isar acikin masana'antar. Jarumar ta fara harkar fim tana da shekaru 8 a duniya. Duba da irin kwarewar Kasuwanci da jarumar takeda hakan ya bata damar shiga cikin sunayen mata 10 da keda kuɗi masana'antar.


Jamila Nagudu

Jamila Umar Nagudu da akafi sani da Jamila Nagudu na daya daga cikin fitattun jarumai a masana'antar kannywood, jarumar tayi fice matuka wajan isarda sako zuwaga yan kallo musamman a shiri na bargwanci. An haifata ne a ranar 10 ga watan Agusta.  Malam Aminu Saira shi ne ya fito da jarumar inda ya sanya ta a wani film na shi mai suna 'Jamila da Jamilu.

Jamila Nagudu na daya daga cikin jaruman kannywood da suka taba yin aure da kuma keda yara amma hakan baisa tayi kasa a gwiba wajan taka "role" da ake bukata a wajantaba. Jarumar nada fara'a da kuma son jama'a. Hakan ya bata damar samun dubban masoya maza da mata. 

Duba da irin matsayi da kuma nasarori da jarumar ta samu a masana'antar muka lissafa ta acikin jerin Mata 10 da Suka fi Kowa Kudi a Kannywood.


Hafsat Idris

Jaruma Hafsat Ahmad Idiris amma anfi saninta da Hafsat Idris na da kyawar siga da kuma kula da jiki duba da irin 'yayanda jarumar keda. An haifi jarumar ranar 14 ga watan Julin shakarar alib 1987 a garin Shagamu dake jihar Ogun a Najeriaya. Iyayen jarumar “yan asalin Jihar Kano ne dake Najeriya. Tun kafin shigar jarumar a masana'antar kannywood Hafsat Idris yar kasuwanci wadda ta kware sosai a kasuwanci na zamani inda take tallata hajarta a instagram.

Hafsat Ahmad Idris ta fara fim ne a shekarar 2016 inda ta fito acikin shiri mai suna Barauniya, da bannan Darakta kuma Furodusa Ali Nuhu. Hafsat Idris ta mallaki kamfanin samar da finafinan Hausa mai suna Ramlat Investment. Sai dai akwanannan wasu hotuna suka bulla na auren jarumar. Hafsat Idris na daya daga cikin mata masu arziki a masana'antar kannywood.


Mommy Gombe

Maimunah Abubakar wacce aka fi sani da Momee Gombe ko Mommy Gombe kamar yadda wasu ke rubutawa, Momee Gombe sabuwar jarumar ce data shigo a cikin masana'antar kannywood da kafar dama. A halin yanzu jarumar tayi nasarar fitowa acikin fina -finai fiye da ashirin.  Jaruma Momee Gombe an haifeta ne a 28 gawatan yuni 1997 inda a halin yanzu tanada shekaru 24 ga haihuwa.

jarumar tayi nasarar shiga fim ne ta hayan shahararren furodusa Auwal Mu'azzam kamar yada ta bayyana acikin wata fira da akayi da ita. Duba da irin rawarda jarumar ke takawa tun alokacin da ta fara shirin fina-finan kannywood musamman wannan sabon shiri mai dogon zango na Darakta kuma Furodusa Ali Nuhu wato "ALAQA" hakan ya bata damar shiga cikin jerin sunayen mata mafi kuɗi a masana'antar kannywood.


Maryam Yahaya

Maryam Yahaya, an haifi Maryam Yahaya a ranar 23 ga watan yuni shekara ta 1997 jarumar nada farin jini sosai a wajan masoya kallon fina-finan hausa ma kannywood, jarumar tayi fama da rashin lafiya sosai amma a yanzu haka Jaruma ta warke kuma ta ci gaba da gudanarda kasuwancinta na fim.

Jarumar ta samu nasarar lashe matsayin kyakkyawar yar wasa mai kwazo a gasar City People Entertainment Awards a shekarar 2017, hakan ya bata damar zama jaruma a cikin wasan kwaikwayo na City People Entertainment Awards a shekarar 2018. Wasu daga cikin fina-finan da Jarumar ta fito Gidan Abinci, Barauniya, Tabo, Mijin Yarinya, Mansoor, Mariya, Wutar Kara, Jummai Ko Larai, Matan Zamani, Hafiz, Gidan Kashe Awo, Gurguwa, Mujadala, Sareenah. Hakane yasa muka zayyana jarumar acikin jerin sunayen mata 10 da keda kuɗi a masana'antar kannywood.

0 Response to "Mata 10 da Suka fi Kowa Kudi a Kannywood 2023"

Post a Comment