-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Yadda Ake Zama da Muguwar Kishiya

Yadda Ake Zama da Muguwar Kishiya

Yadda Ake Zama da Muguwar Kishiya

 • 1.karki shiga hakkinta ko ya za’ayi, kiji tsoron Allah.
 • 2.ki sama ranki bata isa tayi maki komai ba face abunda Allah ya kaddara(ki rike Imani).
 • 3.ki kasance mai bin dokan miji akoda yaushe.
 • 4.Tsaftan jiki, gida, yara ki zamo gwana.
 • 5.Karki yarda tasan abun da ke bata miki rai(KO RAI YA BACI,SHIGE DAKI KIYI KUKA,KI YI WANKA KI DAU KWALLIYA)
 • 6.Karki taba kai kararta gurin miji.
 • 7.kizama kullun acikin fara’a(BA’A DAKEMA KISHIYA).
 • 8.Kizama Kamar doki a gado (Itakuma nunamata miji bai damekiba)
 • 9.Ki mata marhaba a farkon haduwanku(KO AN SAMU MATSALA, ZA’ACA BAKI KITABA TUN FARKO)
 • 10."yayanki natane, karsu zamo kishiyoyinki.
 • 11.Intamiki magana, karkiyi gaggawan ansata, bada kamar sec 30,kinga kin yi tunana kuma zaisa tana shakkanki(AJI)
 • 12.IYA GIRKI BABBAN MAKAMI NE.
 • 13.Ki zamo mai tattali bamai rowaba(DABARA) Ki cireta a ranki(BA ZAMANTA KIKEBA)
 • 14.Kizama yar kwalisa a kullun(Under 12).Kar a gana ranar girkinki da akasinsa.
 • 15.Ki rage yawan hira(KE BA RADIO BACE).
 • Ranan kwananki ke actor ce, ran nata boss(Rakashi da kiss ma zafi inzai tafi can). Karki nuna kishinki a fili.
 • 16Inya kiraki da sunanta, amsa,zai rasa abunda ya furta(IN YAKIRATA DA NAKI MASIFA)ita ga sarkin yaki.
 • 17.karkina magananta da wasu(BATA DAMEKI BA)
 • 18.SHAGWABA amma a DAKA.
 • 19.komin zafin abu,baki ba dambe ko cacarbaki da ita(KE TSARARTACE?)
 • 20.YAR UWA MIJI SAI SIYASA.


DOMINKI NE DA MIJINKI

ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ

ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﻭﺳﻠﻢ

Kishi wani abu ne mai kyau idan aka saka shi a wurin da ya dace, yakan zama mummuna idan ya zarce yadda ake buqatarsa, kamar dawa da ake kamu da ita a sha, idan aka jiqa kwanakin suka wuce sai ta zama giya, ko ruwan kwakwa da yake zama bammi da sauransu, kishin maza zai zo a wajen Miji na Qwarai bayan na gama da Mata ta Gari.

Mace ta gari takan nisanci mummunan kishi domin yakan rage qaunarta a zuciyar mijin ba tare da ta sani ba, wata matar takan yi kishi da uwar mijinta, wata da har da 'ya'yan da ta haifa ma ba wai 'ya'yan kishiya ko ita kanta kishiyar ba, irin wannan kishin yakan 6ata gida ne gaba daya, ya 6ata rayuwar aure da ta maigidan da 'ya'yansa har da ita kanta matar.

A dan iya shekarun da na yi, na ga matar da ta kashe kanta sabo da kishi, wai ba za ta zauna da kishiya ba, na ji wace ta nemi ran mijin Allah ya qwace shi, na ga wace ta nemi sabautashi maqwabta suka kai masa dauki, na ji wace ta zuba wa kishiyar da 'ya'yanta fetur za ta saka wuta Allah ya qwace su, na ga wace ta saka aka kori mijin daga wurin aikinsa, na ga wace take addu'ar Allah ya talautar da mijin don kar ya iya aure, wata ta sa an kashe kishiyar, wata ta nemi an haukatar da ita, wata ta nemi sakin matar, wata ta sayar da lahirarta gaba daya don kawai wani dadi maras tushe a duniya, kai ni na ga wace ta saka 'ya'yan kishiyarta a gaba, ba ta qaunar jin alherinsu, duka wadannan suna ganin abin da suke yi daidai ne.

Irin wannan ya sa magabatanmu - Allah ya saka musu da alkhairi - maganarsu a ranar buden kai ta fi qarfi wajen hana mummunan kishi, shi ya sa Abdullahi bn Ja'afar RL ya yi wa 'yarsa nasiha a ranar kaita daki da cewa "Inai miki kashedi da kishi domin mabudin saki ne, kul da yawan zargi don yakan kawo qiyayya, ki saba da tozali"

Kishi yakan wargaza gida ne, shi ya sa ya zama dole a wajen mace ta gari ta nesance shi, macen da ta kamu da wannan cutar ta kishi za ka riske ta kullum a cikin tsoron cewa wata za ta zo ta qwace mata shi, shin me wancan take da shi da ita ba ta da shi? Me wancan ta ke yi da ita ba ta iya ba kuma ba za ta koya ba? In budurci ne shekara Daya ta yi yawa za ku zama uwaye, amma ke kin sanshi sama da ita, kin daje gidan da 'ya'yan farko ashe ba ke za ta yi kishi da ke ba me ya sa kike kishi da ita?

Haqiqa kishi ba qaunar miji ba ne, kawai shakka ne da tsoro na rashin mijin, wato galibi mata ba su da sakankancewar zuciyar mijin a kansu, don haka za su kadaita hankalinsa a kansu ko da arziqi ko da tsiya, matan Annabawa da sahabbai sun yi kishi, amma na son a ce mijin ya amfana da su ne kawai, na neman yardar mijin ne a lahirance, kowa tana qaunar samun lada, shi ya sa wata ta iya kyauta da kwananta don ba shi ne matsalarta ba, aljanna take nema tare da manzon rahama, ko kin fahimci Hausata????

0 Response to "Yadda Ake Zama da Muguwar Kishiya"

Post a Comment