-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Yadda Ake Cire Shiga Shafukan Batsa A Waya

Yadda Ake Cire Shiga Shafukan Batsa A Waya

Yadda Ake Cire Shiga Shafukan Batsa A Waya

A addinance dai kowa yasan kallon video na batsa haramunne, haka kuma kallonsu yana cutar da lafiyar idanu da kuma gur6ata zuciya tare da saka raunin imani da tsoron Allah.

Muna cikin wani zamani wanda yahudawa suke amfani da cigaban da aka samu na amfani da yanar gizo suna gur6ata mana tarbiyar ƙanne da yara dama mu kanmu 'din baki 'daya, ta hanyar bu6e website website masu dauke da bidiyoyi na batsa wanda mu addininmu ya haramta mana kallansu, su kuma suna samun maƙudan ƙu'da'de ta wajen.

Ba'a iya maza kallon bidiyoyin batsa ya tsaya ba, harda mata kuma hakan yana 'daya daga cikin abubuwan da suke bada gudunmuwa sosai wajen lalata mana tarbiya. Wa'iya-zubillah, Allah ka ƙara tsare mu, Amin.

Hanyar da zaka iya bi domin haramta ma wayarka ko wayar ƙaninka kota ƙanwarka, kota yaranka samun damar kamo wa'dannan website 'din shine...

Da farko zaka shiga cikin google search na wayar, ko kuma browser 'dinda take a saman wayar, sai ka rubuta google.com sai ka danna (go) wato search.

Bayan ya bu'de zaka ga bayanai sun fito da yawa, sai ka duba daga hannun hagunka zaka ga wasu layi-layi guda 3 da suka jera, sai ka shiga cikinsu.

Suma idan suka bude sai ka tafi wajen da aka rubuta "settings", wanda shine na uku a hoton dake sama, sai ka shiga ciki.

Idan ya bude zaka tsaya ka duba da kyau akwai inda aka rubuta "Safesearch Filters(?)" a ƙasanshi zaka ga wasu za6uka guda biyu, na farko shine "Show explicit results" na biyu kuma "Hide explicit results" sai ka maida za6inka akan na biyun wato "Hide explicit results".

Daga nan shikenan sai ka tafi zuwa can ƙasa inda zaka ga an rubuta "Save" da kuma "Cancel" sai ka danna save 'din, shikenan ka gama.

Shikenan ka rufe duk wani website na batsa a cikin wannan wayar dakayi haka akanta ba zafa ƙara kamosu ba koda anyi search bazasu fito ba, amma idan akwai browser guda biyu ko uku sai kayi ma ko wacce haka.

Allah ya ƙara tsaremu damu da 'yan'uwanmu tare da dukkanin musulmi daga fa'dawa tarkon she'dan da she'danun mutane, Allah ka tsare mana imaninmu aduk inda muke, ka nisanta mu daga aikata dukkan wani aiki wanda baka so. Amin.

0 Response to "Yadda Ake Cire Shiga Shafukan Batsa A Waya"

Post a Comment