-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Illolin Yanke Fatar Tushen Farce

Illolin Yanke Fatar Tushen Farce

Illolin Yanke Fatar Tushen Farce.



Akwai wata siririyar fata mai kama da farar leda da ke ɗamfare a kan farce. Wannan fata mai kama da farar leda tana tohowa ne tsakanin farce da fatar jiki da ta yi wa tushen farce ɗamara.


Wannan fata wace ake cewa "cuticle" a turance tana da muhimmancin gaske ga lafiyar farce da jiki baki ɗaya. Domin fatar na da ɗabi'ar leda ne wajen hana danshi, lema, ko wani ruwan sinadari shiga zuwa tushen farce. A taƙaice, wannan fata ita ce ke bai wa tushen farce kariya daga duk wani baƙon abu da zai iya kutsawa zuwa tsakankanin farce da fatar yatsa, kamar ƙwayoyin cutuka, lema, danshi, ko wani sinadari ko kemikal.

Sai dai, mutane da yawa na ganin wannan siririyar fata ba ta da wani amfani inda mutane ko masu yankan farce ke kai maƙura wajen ƙwaƙwalo ta tun daga tushe yayin yankan farce a ƙoƙarin tsabtace farce domin ya yi kyau fes. Wani lokacin ma ana yanke ta ne tare da fatar da ta yi wa tushen farce ɗamara ko guru.

Daga cikin haɗarin sa reza ko almakashi a kankare ko a ƙwaƙwalo wannan fata daga tushe akwai haifar da ɓaraka ga tushen farce, hakan kuma zai kawo shigar ƙwayoyin cutuka kamar bakteriya, fangai da sauransu, waɗanda ke haddasa ciwon yatsa, lalacewar farce, da ciwo ko riƙewar gaɓɓan yatsa.

Masana na ba da shawarar yanke ko kankare fatar ne kaɗai a inda ta tashi ko ta ɓaro daga farce da kanta, wato idan ta mutu kenan, maimakon ƙwaƙwalo ta tun daga tushenta.

~~@physiotheraphy hausa

0 Response to "Illolin Yanke Fatar Tushen Farce"

Post a Comment