-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Gwamnatin jahar Gombe ta kaddamar da shirin tallafin Ng-cares

Gwamnatin jahar Gombe ta kaddamar da shirin tallafin Ng-cares

Gwamnatin jahar Gombe ta kaddamar da shirin tallafin Ng-cares 

Gwamnatin jahar Gombe ta kaddamar da shirin tallafin Ng-cares a jiya alhamis a karamar hukumar Yamaltu Deba, Shirin wanda ya samo asali daga gwamnatin tarayya NG-CARES Shiri ne na musamman da gwamnatin tarayya ta shirya da hadin gwiwan babban bankin duniya (World Bank) domin farfado da tattalin arziki da kuma rage radadin talauci wanda cutar COVID.19 ta janyo wa. 

Wannan shiri dai,  gwamnatin tarayya ta tanade shi ne domin taimakon talakawa da masu kananan karfi, samar da abinci , da kuma taimakon kananan masana'antu da kuma kananan yan kasuwa gami da manoma domin wadatar abinci .

Gwamnatin Najeriya ta samu taimako ta hanyar rance (bashi) na dala miliyan dari bakwai da hamsin ($750 million) domin tallafawa duk wanda abun ya shafa. 

Ita gwamnatin Najeriya kuma sai ta tsara abun ta yanda ta rabawa Jahohi 36 na kasar dala miliyan ashirin-ashirin ($20 million) ta kuma bawa babban birnin tarayya, Abuja dala miliyan Sha biyar ($15 million), wanda kuma Jahohin su zasu biya gwamnatin tarayya ita kuma gwamnatin tarayya sai ta biya babban bankin duniya wato "World Bank". 

Atakaice dai shi wannan shiri na GO-CARES shiri ne na gwamnatin tarayya da kuma babban banki duniya wanda kuma ita jahar Gombe zata samu dalar amurka miliyan ashirin ($20 million) kamar yanda gwamnatin tarayyan da kuma babban Bankin Duniyan suka tsara, wanda a kudin Najeriya kudin zai kama  Naira Biliyan Sha hudu da miliyan dari biyu ne (N14.2 Biliyan).

gwamnatin jahar Gombe dai ta cire NG ne kawai daga NG-CARES ta kuma sanya na ta GO sai ya koma GO-CARES. Amma dai wannan shiri ne na gwamnatin tarayya da hadin gwiwan babban bankin duniya, sune suka kirkiro.


0 Response to "Gwamnatin jahar Gombe ta kaddamar da shirin tallafin Ng-cares"

Post a Comment