Real Madrid ta cefano Tchouameni ne bayan ta gaza samun Kylian Mbappe a ƙarshen kakar da ta gabata
Real Madrid ta cefano Tchouameni ne bayan ta gaza samun Kylian Mbappe a ƙarshen kakar da ta gabata
Aurelien Tchouameni: Real Madrid ta sayi ɗan wasan Monaco
Real Madrid ta kammala ɗaukar matashin ɗan wasan tsakiya na Faransa daga ƙungiyar Monaco kan yarjejeniyar shekara shida.
Ƙungiyoyin biyu sun sanar da cinikin, inda Real ta ce za ta ƙaddamar da ɗan wasan mai shekara 22 ranar Talata bayan an kammala duba lafiyarsa.
Tchouameni ya buga wasa 35 a gasar Lig 1 ta Faransa ga Monaco a kakar wasa da aka kammala, inda ya ci kwallo uku da taimakawa wajen cin biyu.
Kazalika, ya buga wa ƙasarsa Faransa wasa 11 tun da ya saka mata jasi a watan Satumba.
Rahotanni sun ce Real za ta biya yuro miliyan 80 da kuma tsarabe-tsarabe da suka kai miliyan 20 - yuro miliyan 100 ke nan jumilla.
An yi ta alaƙanta Tchouameni da Liverpool, da Manchester United, da kuma Paris St-Germain.
Wasu rahotannin ma sun ce ɗan wasan har ya amince wa Liverpool kafin daga baya ya ƙulla yarjejeniya da Real.
Madrid ta cefano Tchouameni bayan ta gaza samun Kylian Mbappe a ƙarshen kakar da ta gabata.
Copy Daga Shafin BBChausa
0 Response to "Real Madrid ta cefano Tchouameni ne bayan ta gaza samun Kylian Mbappe a ƙarshen kakar da ta gabata"
Post a Comment