Karin Magana - Hausa
Friday, May 27, 2022
1 Comment
Karin Magana- Hausa
A
- A bakin tsoho goro kan tsufa
- A bakin wawa ake jin Magana
- A bari ya huce shi ke kawo rabon wani
- A bar kaza cikin gashinta
- Abin ba dadi, mahaukaci ya tauna kasha
- Abin bai dace ba, an ga Malami da gatari
- Abinda babba ya gani a zaune, yaro ko ya hau rimi ba zai gan shi ba
- Abinda ruwan zafi ya dafa, in an hakura, ruwan sanyi ma saiya dafa
- Abinda ya bata a duniya in an je lahira a ganshi
- Abin da ya kori bera ya fada wuta, yafi wutar zafi
- Abin da sake, an bai wa mai kaza kai
- Abin da sake an bai wa mai rogo bawo
- Abin da yawa, mutuwa ta je kasuwa
- Abin da Allah Yayi, Annabi sai ceto
- Abinda sauki, mutuwar bako a gari
- Abin da ka gani a gidan Kaura yana na Goje
- Abin da zuciya ya dauka, gangan jiki ma dole ya dauka
- Abin da baki ya daura, hannu bay a kwancewa
- Abin mamaki, mai karfi na bara
- Abin mamaki furar sayarwa a akushi
- Abin mamaki kare da tallan tsire
- Abin mamaki mai gari gwauro talaka da mata hudu
- Abin mamaki bay a karewa, rakumi ya shiga kuratandu
- Abin mamaki matar falke ta haifi jaki
- Abin nema ya samu, matar dan doka ta haifi barawo
- Abin nema ya samu, matar falke ta haifi jaki
- Abokin kirki ya fi mugun Dan uwa
- Abokin cin mushe ba’a boye mashi wuka
- Abin mamaki baya karewa, rakumi ya shiga kuratandu
- Abin nema ya samu, matar dan sanda ta haifi barawo
- Abin ya girma, kashe kwarkwata da tabarya
- Abin rabo ne, kuturu ya kama tarwada
- Abin fada na mai baki ne
- Abu a rufe mai raba zumunci
- Abu kamar wasa, karamar Magana ta zama babba
- Abu uku su ne maganin zaman duniya, tawakkali, dangana da hakuri
- Abu namu maganin a kwabe mu
- A bugi juji domin a ji karar gwazarma
- Abokin kirki ya fi mugun dan uwa
- Abokin sarki, sarki ne
- Abokin kuka ake gaya wa mutuwa
- A ci baa sayar ba, kwai ya fi doki
- A ci a rage, shi ne ci
- A cikin ido ake tsawurya
- A daga sama an yi wa wada sata
- A dafa a daka a tankade sai kalwa
- A dade ana yi sai gaskiya
- Adinga zuwa rafi wata rana a fasa tulu
- A duke ka a hana ka kuka
- Addu’a maganin annoba
- A dubi ruwa a dubi tsaki
- A jamu akai an ba uwar makaho kasha
- A jefar da kwallon mangwaro a huta da kuda
- A gayawa wani riginginin farin wata, agola kafi masu gida
- A aiki kare ya aiki wutsiya
- Aiki da hankali yafi aiki da agogo
- Aikin bakon raggo, raggo bakon aiki
- Aikin banza hutun jaki da kaya
- Aikin banza jefa agwagwa a ruwa
- Aikin banza zani da aljuhu
- Aikin banza bille a ciki
- Aikin banza talaka ya grime sarki
- Aikin banza yin kiba a kunne
- Aikin banza kiwon makahon kare
- Aikin banza kare da gudun laya
- Aikin banza sauri ba wurin zuwa
- Aikin banza makaho da waiwaye
- Aikin banza harara a duhu
- Akuya ko bata haihuwa tafi kare
- Akuya tayi wayo da yankakken kunne
- A kan wanke tukunya domin tuwan gobe
- Allah ke gyara tuwon makauniya har a ci ba kuda ba gashi
- Allah ke ci da maraya ko da mai uba bai so ba
- Allah suture bukwi in ji kishiyar mai doro
- Allah gatan kowa
- Allah na taimokon wanda ya taimaki kanshi
- Allah shi ke baiwa maraya ko da mai uwa bai so ba
- Allah Ya ci da na gari ba mugu ba
- Allah Yayi aure da mara kwabo
- Allah Ya gyara rimi cediya ta daina fushi
- Allah Ya wadarai naka ya lalace rakumin dawa yaga na gida
- Allah Ya kai yaro matsiyin babba
- Allah Ya bamu lafiya baba yaga tsirara
- Allah Ya kai damo ga harawa ko bai ci ba yayi birgima
- Allah Ya ba na zaune albarkacin na tsaye
- Allah Ya tsare gatari ga noma
- Allah Ya hada mu da mai son mu koda mugune
- Allah Ya fishemu da hawa dokin zuciya
- Allah Ya ba mai rabo sa’a
- Allah Ya hana kunya ranar gaskiya
- Allah Ya kawo kudi talauci ya ji kunya
- Allura a cikin ruwa mai hikima kan tsinta
- Allaura a cikin teku mai daukanta sai mai dace
- Alkawari kayane in a dauka sai an cika
- Alamar rago tana ga daurin bante
- Alamar karfi tana ga mai kiba
- Albarcin kaza kadangare ke shan ruwan kasko
- Albasa bata yi halin ruwa ba
- Alheri gadon bacci ne
- Alheri dan dankone ba ya faduwa kasa banza
- Alheri ne bakon gishiri a shekara ana lashewa
- Alhaki kuykuyo ne mai shi yake bi
- Almajiri tsutsune in ya ci sai ya tashi
- Amfanin abun ado daurawa
- Amfanin sani aiki da shi
- Amarya bata laifi koda ta zagi ‘yar masu gida
- An bar kyau tun ranar haihuwa
- An bar jaki ana dukan taiki
- Anci moriyar gangan an jefar da kware
- An dade ana gafara ga sa ba’a ga kaho ba
- An daga sama anyi wa wada sata
- An ki cin biri an ci dilla
- An raba hankali na biyu ance ya sha fura a je gona
- An rabu ba kare bin damo
- An sha kanwa kwarnafi ya kwanta
- Ana barin halas dan kunya
- Ana babbakar giwa wa ke ta zomo?
- Ana bikin duniya ake na kiyama
- Ana dariya mai tauna kan koshi
- Ana fakewa da guzuma ana harbin karsana
- Ana ganin wuyan biri ake daureshi a kwankwaso
- Ana gudun gara an fada zago
- Ana rabaka da kiwon akuya kana kyalla ta haihu
- Ana rabaka da kaya kana nade gammo
- Ana sara ana duban bakin gatari
- Ana son wawa, haihuwarsa ne ba’a so
- Ana yabon ka sallah, ka kasa alwala
- Ana yi da kai yafi ba’a yi, sarki ya koma mai anguwa
- Ana zaton wuta a makera, sai gashi a masaka
- Annurin fuska kaurin hanji
- An gara jakan mafaurata
- Aci ba’a sayar ba kwai yafi doki
- A cikin ido ake tsawurya
- Anyi asarar kanwa tunda wake ya lalace
- Anyi ba’a yi ba ba ance tsirkiyada fatan kunkuru
- A ramawa kura aniyarta
- Arha cefane kunu daga ruwa sai tsamiya
- Arha kamar jamfa a jos
- Arha maganin mai wayo
- Arha wanzami ya samu kan mai saiko
- A rashin kira Karen bebe ya bata
- A rashin farin wata tauraro ke haske
- A rashin sani kaza ta kwana kan dami
- A rashin sani bako ya sha ruwan wanka
- A rashin tayi akan bar arha
- A rashin tuwo akan ci wake a kwana
- A rashin uwa ake uwar ɗaki
- A ruwa ake dadewa ba a wuta ba
- Arziki rigar kaya kana ja yana ja
- Arziki rigar kaya ga dadi ga suka
- An sha ruwan gwangwala a kara tsayi
- A sa a baka ya fi a rataya
- Asalin birni kauye ne
- A tambayi me kundumi labarin kitse
- A taru a kashe mahaukacin kare
- Ayi wanda za’a yi bera ya zubar da garin kyanwa
- Ayi a hankali kada a sha ruwa da haki
- Ajiya maganin wata rana
- A kwana a tashi jariri ango ne
- A kwana a tashi yaro tsoho ne
- Akwai ranar kin dillaci randa rigar mai gari ta bata
- “A yi abunda za’a yi” ramamme ya zagi maye
- B
- Ba sauran waka, an yanke harshen zabiya
- “Ba samun duniya ba” wurin da za’a zauna a ji shine injin dan tsako
- Ba’a bari, a kwashe duka
- Ba’a fasa randar daki ba’a shigar da na waje ba
- Ba’a fafe gora ranar tafiya
- Ba’a fushi da yin Allah
- Ba’a gane kyaun gini sai anyi yabe
- Ba’a gaggawar fara’a
- Ba’a jan ragama da rigima
- Ba’a kada miya tun dawa na rumbu
- Ba’a kin ta mutane ance bazawara ta koma gidan mijinta
- Ba’a kin mutane ance barawo yayi gudu
- Ba’a koyan karatu ran tukuri
- Ba’a sarki biyu a gari daya
- Ba’a shan zuma sai an sha harbi
- Ba’a shan zuma sai da wuta
- Ba’a sayan jaki don a ci sai don daukan kaya
- Ba’a san maci tuwo ba sai miya ta kare
- Ba’a sake wa tuwo suna
- Ba’a shiga sharo ba shanu (mind your business )
- Ba’a raba hanta da jini
- Ba’a riga malam masallaci
- Ba’a raina zakin gwandan daci don ba’a bata ruwa
- Ba’a hada gudu da susan duwawu
- Ba’a hada gudu da susan katare
- Ba’a hana mabada rago fata
- Ba’a karbe wa yaro garma
- Ba’a maida hannun kyauta baya
- Ba’a mugun sarki sai mugun bafade
- Ba’a nunawa kurciya baka
- Ba’a saurin yabon dan kuturu sai ya girma yatsun sa
- Ba’a wasan wuta a gidan kara
- Ba’a wuce makadi da rawa
- Ba’a yi wa biri burtu
- Ba’a yin nitso a masaki
- Ba’a yanka karfe sai da karfe
- Ba bako ruwa ka sha labara
- Baka cin zamanin ka ka ci na wani
- Ba cinya ba kafar baya
- Ba dan tsayi akan ga wata ba
- Ba domin tuwo akayi ciki ba
- Ba dukan ruwan sama ke da wuya ba , ruwan ganye
- Ba fada da malam ba, asari ake tsoro
- Ba gagararre sai bararre
- Ba iya kwanciya aka fi kare ba sai dai abun rufa
- Baka do gadon mutun amma kana da gadon batun sa
- Ba ji ba gani auren kurma da makaho
- Ba maraya sai rago
- Ba mai yi sai Allah
- Bani na kashe zomon ba rataya aka bani
- Ba shiga ba fita an ba mahaukaciya tsaron kofa
- Babban goro sai magogin karfe
- Babban kaya sai gammo
- Bako raba ne, yakan zo ya wuce
- Bako ba sallama wawa ne
- Bakon munafuki bana mutun daya bane
- Bakar inuwa gwamma ranar daki
- Bakin jinin mazuru mai kaza zagi, mara kaza zagi
- Bakin Karen masoyi yafi farin ragon makiyi
- Bakin tukunya mai fidda farin tuwo
- Bakin rijiya ba wajan wasan makaho bane
- Bakin da Allah Ya tsaga baya hanashi abinci
- Baki shi kan yanka wuya
- Balbela baki bin kare sai shanu
- Ban sa a ka ba in ji barawon taguwa
- Banga alama ba, ance wa kuturu ya gama lafiya
- Ba rabuwa da gwani ba, sai dai maida gwani kamar sa
- Bara nayi wake, bana nayi harawa
- Barawon rakumi daga daddawa ya fara
- Barewa baza ta yi gudu ba danta yayi rarrafe
- Bari neman jini ga babe, Allah bai yi shi da jini ba
- Bari murna Karen ka ya kama zaki
- Bashi hanji ne yana cikin kowa
- Ba’a yin rawa ba juyi
- Bayan wuya sai dadi
- Bayan ci zama sai gumi ne
- Ba kullun ake kwana a gado ba
- Ba kira mai ya ci gawayi?
- Ba mutuwan ake tsoro ba, sabo
- Ba wahalalle sai mai kwadayi
- Ba za’a ji mutuwar sarki a baki na ba
- Ba za’a ci kwado da yaro ba sai ya wanke hannunsa
- Baza ka ari bakina ba ka ci mun albasa ba
- Ba zama an saci dan barawo
- Banza a banza kare a karofi
- Banza girman mahaukaci, karami mai hankali ya fishi
- Banza bata kai zomo kasuwa
- Ban ci kasuwa ba, rumfa ba zai danne ni ba
- Barin kashi a ciki baya maganin yunwa
- Bikin faran kaza balbela ba gayya bace
- Bikin magaji baya hana na magajiya
- Bin na gaba bin Allah
- Biri da gatari a gona abin tsoro
- Bishiya mai ‘ya’ya ake jifa
- Biyan bukata yafi dogon buri
- C
- Can ga su gada zomo yaji kiran farauta
- Can kake adon mai gona
- Ciki da gaskiya wuka bata huda shi
- Ciki mai manta kyautan jiya
- Cinikin duniya diban nono
- Cinnaka baki san na gida ba
- Cin wake na yara kumburin cikin manya
- Cin dadi ai sabo ne
- Cin danko harda su kaza
- Cin tuwon kishiya ramako
- Cin loma yafi jiran malmala
- Cin abinci dare daya kumburin ciki
- Ciwon da kare yayi idan dan akuya ne sai wuka
- Ciwon ‘ya mace sai ‘ya mace
- Ciwo ba mutuwa ba sai kwana ya kare
- Cin hakkin sama sai rakumi
- Ci naka in ci nawa, ba rowa bane halin zama ne
- Ci gaban mai ginin rijiya,yana zurfi ana shiga hatsari
- D
- Da ba dan mun san asalin angulu ba, da nace daga masar take
- Da babu gwara ba dadi
- Dabara baya daura kaya sai igiya
- Da biyu an buge biri da rani
- Da biyu an bugi akuyar kishiya
- Da dan gari akan ci gari
- Da dama sarki a bisa jaki
- Da ganin kura kasan zata ci akuya
- Da ganin dan kunama zai yi harbi
- Daga ganin dutsen zuma, kasan daga dadi take
- Daga baya an yi sadaka da bazawara
- Da haka muka fara, kuturu yaga mai kyasbi
- Da itace mai kama ake kota
- Da kamar wuya a gasa kaza a yar
- Da kamar wuya gurguwa da auren nesa
- Da kukan zuci gwara na fili
- Da kyar na kai yafi da kyar aka kamani
- Da na gaba ake gane zurfin ruwa
- Da muguwar rawa, gwamma kin tashi
- Da sanin ango aka yi wa ‘yan buki duka
- Da sannu auduga zai zama zare
- Da sabon gini gwamma yade
- Da sabuwar rijiya gwamma yasa
- Da sauran tsalle an daura wa kwado garwashi
- Da sauran kuka an daurawa jaki kaya ba taiki
- Da tsirara gwara bakin bante
- Da tsohuwar zuma ake magani
- Da rarrafe yaro kan tashi
- Da ruwan ciki ake jan na rijiya
- Da rigimar ciki gwamma na waje
- Da uba ake ado ba da riga ba
- Da wuya ake gane fushin mai tsinin baki
- Da walakin goro a cikin miya
- Da wawanci gwara gidadanci
- Da wasa ake fada wawa Magana
- Da yayyafi kogi kan cika
- Da zafi zafi akan bugi karfe
- Dadi mai sa zabiya guda
- Dadin zama sai bare, wuyar zama sai dan uwa
- Dadin zama ke kawo bege
- Dadi na da gobe saurin zuwa
- Dadin duniya yana tsawo ana kara hallaka
- Dadewa a bauta ‘yanci ne
- Daidai ruwa daidai gari
- Daji ba’a sa mata kyaure
- Daki mai duhu, mara gaskiya ke tsoron shiga
- Dan adam mai wuyan gane hali
- Dan baiwa ‘yar albarka
- Dan banza yashi ne ko an dunkula shi baya dunkuluwa
- Dan hakin da ka raina shi ke tsole maka ido
- Dan kuka mai jawa uwarsa jifa
- Dan kuka baya zama dan tsamiya
- Dan jinjirin jimina gagara shaho dauka
- Dan jinjirin kura, kashe ki tausayi barinki takaici
- Dan tsako samo ki ki dangi
- Dan fari man gyada ne
- Dan kishiya rikon hakuri
- Dan uwa rabin jiki
- Dan masara ana goyon ka kana gemu
- Dami ya tsinke a gindin kargo
- Dama yaya lafiyar kura balle tayi hauka
- Daminan ta za tai kyau, daga bazara ake gane ta
- Daminan bana ba kamar ta bara ba, kwado ya fada ruwan zafi
- Damo sarkin hakuri
- Da na sani keya ce a baya akan barta
- Dattijo baka kukan aski
- Daudar gora kowa zai sha ta
- Dinyar makaho ta nuna a hununsa
- Dillalin wada shi ya san kudin jariri
- Dogayen kunnuwa ba zasu sa ji ba
- Dogaro ga Allah jari ne
- Dole ne a ce wa mijin Iya Baba
- Dole ne zuwa biki da muni
- Dole sai an yi kaciya ga yaro
- Dole ne a bambanta dan duma da na kabewa
- Dole ne a bambanta aya da tsakuwa
- Dole ne a bambanta zare da abawa
- Dole kare ya mutu da haushin kura
- Dole gyada ta yi mai, in ta ki ta sha matsa
- Domin munafuki gari bai kin wayewa
- Don ganin hadari ba a zubda ruwan buta ba
- Don mugun nufi ba a dinkin lifidi
- Dokin mai baki ya fi gudu
- Dokin da na san i ba ya yaki
- Don hannun ka ya rube, ba ka yankewa ka yar
- Don kai ake hula, har kunne ya samu
- Duniya ba gaskiya, barawo ya rasa shaida
- Duniya budurwar wawa
- Duniya mai ido tsakar ka
- Duniya zaman ‘yan marina, kowa da inda ya fuskanta.
- Duniya mace da ciki, ba a san abinda zata haifa ba.
- Duniya juyi-juyi, kwado ya fada ruwan zafi
- Duniya juyi-juyi mai doki ya koma kuturi
- Duniya rawar ‘yan mata, na gaba ya koma baya
- Duniya kamun kifi, kowa ya kamo ya sa a goransa
- Duniya ba lafiya, tunda ba’a kashe mutuwa ba
- Duniya rumfar kara ba ta da wuyar rushewa
- Duniya gidan kashe ahu wanda ya kasha taro yay i barna/zari
- Durkusa wa wada ai ba gajiyawa ba ne.
- Duddugar kaya, ta fi kayar zafi
- Dutsen tsakiyar ruwa bai san ana rana ba
- Duk abin da ya ci doma ba zai bar awai ba
- Duk abin da aka jefa sama, kasa zai fado
- Duk abin da mutum ya shuka shi zai girba
- Duk abinda ya taba hanci, idanu ruwa suke
- Duk abin da lauje ya yanka, ciyawa ne
- Duk abinda ka gani a gidan sarki, ya na kasuwa
- Duk dan da ya hana uwarsa bacci, shi ma ba zai runtsa ba
- Duk daya ne, makaho yayi dare
- Duk daya ne, mara sallah ya je gidan bamaguje
- Duk dadin madi, zuma ta fi shi
- Duk dacin gaskiya shan ta ya fi shan kwaryar zuma
- Duk dukiyar ka, kiyayi mai nema
- Duk in da wani ya tafi tsirara da sanin mai riga ne
- Duk inda ka ga hanya, in ba gari ya nufa ba, rafi ne
- Duk kyan takalmi, sai an taka shi
- Duk mai nashi ba ya kunyata
- Duk mai jinkiri, baya nasara
- Duk mai musun damina, ya saurari kukan kwadi
- Duk mai rai mamaci ne
- Duk nama ne, jakin maguzawa ya mutu
- Duk tashin tsuntsu, sai sama ta ga bayan shi
- Duk wanda bai ji bari ba, ya ji hoho
- Duk wanda yaki ji, ba zai ki gani ba
- Duk wanda ya ce wutar kara ta kwana, shi ya kwana bai runtsa ba.
- Duk wanda ya ga zara, zai ga wata
- Duk wanda ya raina tsayuwar wata, ya hau ya gyara
- Duk wanda yace bayanka na da kashi ka taba goya shi
- Duk wanda yace zai hadiye gatari, a rike masa kota
- Duk wanda yayi zagi a kasuwa, ya san da wanda yake yi
- Duk wanda ya tuna bara, bai ji dadin bana ba
- Duk wanda yake son rawa, ya koya wa dansa kida
- Duk wanda aka gani da tabarma, yana neman wurin shinfida ne
- Duk wanda ya ji haushin duniya, ya gaji da ita ne
- Duk wanda hannunsa ya kirga riba, wataran zai kirga faduwa
- Duk wanda ya daure kura, ya san yadda zai kwance ta
- Duk wanda ya zubar mini da tsamiya, zan zubar masa da nononsa
- Duk wanda yayi maka kan kara, kayi mashi na itace
- Duk wanda yayi noma ya huta da awo
- Duk wanda ya so musanya, ya raina nashi ne
- Duk yadda ake yi da jaki, sai ya ci kara
- Duk zafin tukunya dole a sauke
- Duk zurfin ruwa akwai yashi a ciki
- F
- Fada wurin ban kashi
- Faduwa ta zo daidai da zama
- Fadan da ya fi karfinka, maida shi wasa
- Fadi alheri ko ka yi shiru
- Fata na gari lamiri ne
- Fatara mai tada tsohon bashi
- Farar aniya laya ce, wanda ya zo da bakaya sanya abinsa
- Farin wata raka wawa
- Farin wata sha kallo
- Farin cikin barawo ya sami kofa a bude
- Fawa ta gagari ‘yan fawa, balle ‘yan fince
- Filin sukuwar doki ba a gurguwar jaka bane
- Fushin masoyi ya fi dariyar makiyi
- Furar jiya ce ta kasa tsami
- G
- Gaba damisa baya sayaki
- Gaba da gabanta, aljani ya taka wuta
- Gaba ta kai ni gobarar titi
- Ga doki har doki, amma kofaton na sakaina ne
- Ga fili ga mai doki
- Ga kanya ta nuna amma biri ya makance
- Ga koshi ga kwanan yunwa
- Ga maciji ba a nuna ja
- Ga mari ka tsinka jaka?
- Gado ba bakon tsirara ba ne
- Gadar zare rashin sani ke sa a bita
- Gadon Ali sai fanna, ramin kura sai ‘ya’yanta
- Gafiya tsira da na babinki
- Gane min hanya, makaho ya so tseg
- Gangara maganin makiyi
- Gangan dutse maratayin zare
- Gani ya kori ji, yadda koko ya fi kunun zaki
- Ga ni ga Allah barawo a hannun mata
- Gani da ido maganin tambaya
- Gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah
- Ganin gidan kansa kare ya zagi kura
- Gani ai ba ci ba
- Ganin zumar wani, kada ta sa ka zubar da madacinka
- Ganyen doka daya ya fi na dorowa dari
- Garin banza a farau farau din banza yake karewa
- Garin neman kiba an sami rama
- Garin gudun targade an sami karaya
- Garkuwa mai tare harbi
- Gaskiya daci gare ta
- Gaskiya matakin nasara.
- Gaskiya ta fi tafin hannu cike da zuma
- Gaskiya tafi kwabo
- Gaskiya dokin karfe, duk wanda ya hau ba zai yi nadama ba
- Is it true that the end justifies the means? <> Gaskiya ne kwalliya ta biya kuɗin sabulu? [3]
- Gatari da wuta mai wuyan rataya
- Gero ya saba da ruwa tun ba a surfa ba
- Gidan maki-gudu sai da kara kan nuna
- Gida da yawa maganin gobara
- Gida biyu maganin gobara
- Gindin kura ya saba da raba
- Girma aka fi dauro, ba tsaba ba
- Girman kai rawanin tsiya
- Girma da arziki shi ya sa ake jan sa da abawa
- Girma da arziki ke jan rakumi ba akala ba
- Girma ya fadi, rakumi ya shanye ruwan kaza
- Giwa ta fadi kowa ya yanka rabon sa
- Gobara daga kogi maganin ta Allah
- Guntun gatarinka yafi sari ka bani
- Gudu samun sarari
- Guga ba ki tsoron rami
- Gurgu ya kama barewa mai kafa ya kasa
- Gurnanin damisa Karen gida ke tsoro
- Guda ba a yin ta da yare
- Gwani ba ka arziki sai suna
- Gwanin wani wawan wani
- Gwandar dawa, ga ruwa ga zaki
- Gwamma kwado da gaya
- Gwamma barnar ruwa da na wuta
- Gwano baya jin warin jikinsa
- Gyaran fuska ya fi gyaran gona
- Gyara kayanka ba zai zamo sauke mu raba ba
- H
- Habaicin kura na mai akuya ne
- Hatsari ne abota da wawa
- Hadarin sama maganin mai kabido
- Hadin kai ya fi hadin baki
- Hadin kai shi ne karfi
- Haihuwar guzuma, uwa kwance, da kwance
- Hakorin hatsin tukunya, bas hi da wuyar karewa
- Hakuri maganin zaman duniya
- Hakuri jarin mai shi
- Haka da nade-nade, dan wake ya ga tubani
- Hakorin dariya shi ke cizo
- Hali zanen dutse, ba mai shafewa
- Hali ya rigaya mai horo
- Halin mutum sai Allah
- Halin mutum jarinsa
- Hanci bai san dandanon gishiri ba
- Hankaka kowa ya ga bakin ki, zai ga farin ki
- Hankaka mai da dan wani naki
- Hankali mudu auna shi ake yi
- Hange baya kawo nesa kusa
- Hanya ta fi gata
- Hanyar ruwa gangare
- Hanya mai hada zumuntar dole
- Hana wahala sai Allah
- Hannu da yawa maganin kazamar miya
- Hannu daya ba ya daukan jinka
- Hannun wani bai yi wa wani tagumi
- Hannun Bambara ya fi na dodon gona
- Hangen kitse ake wa rogo
- Hangen dala ba shiga birni ba ne
- Hanyar lafiya a bi ta da shekara
- Hankali ya fi wayo
- Hantsi ba hatsi hatsari
- Harbi gad an jaki gado
- Hassada ga mai rabo taki ne
- Hasken wata baya dai-dai da na rana
- Hausa ai ba dabo ba ce harshe ne
- Hauka dangi-dangi, kowa da irin nasa
- Hauka ja, hular dara ba tuntu
- Haushin kare, ba ya hana kura shiga gari
- Hayaki mai fidda na kogo
- Hayaki ba ya boyewa ko da a gidan marowaci
- Hikima kashin kwance, wanda bai iya ba, bata jikinsa
- Himma ba ta ga rago
- Horo ba kisa ba, gyaran hali ne.
- I
- Icen taba, Allah na ruwa tana bushewa
- Idan kura na maganin zawo ta yi wa kanta
- Idan aka bi salsala, jinin kaska na saniya ne
- Idan aski ya zo gaban goshi ya fi zafi
- Idan basira ta kare wa kare, sai ya daina haushi ya koma tunkuyi
- Idan balbela ta biya, zabuwa ta je da zanen ta
- Ido ba mudu ba, amma ya san kima
- Idan bori gaskiya ne, a fada rijiya
- Idan da alkawari ruwa ba zai ci gwani ba
- Idan da kwadayi da wulakanci
- Idan da rai da rabo
- Idan dajarar kaza ta fadi, har kwan da ke cikinta
- Idan hankali ya bata, hankali ke gane ta
- Idan ido ya mutu kwalli baya tada su
- Idan kai na da tsoka, kowa ya taba ya ji
- Idan kare na sunsunar takalmi, zai dauka ne
- Idan ka ga godiya da sirdi, wani ta kayar
- Idan ka ga baki da jini, na mai gardama ne
- Idan kunne ya ji, gangan jiki ya tsira
- Idan mafadin Magana wawa ne, mai ji ba zai zamo wawa ba
- Idan makaho ya rasa ido, sai ya ce yana wari
- Idan maciji ya sha wuya, in an yi walkiya, sai ya kai sara
- Idan mutum ya je gari, ya ga kowa da jela, shima ya nema ya sa
- Idan wani ya ki ka da wuni wani zai so ka da kwana
- Ido wa ka raina? Wanda na ke gani kullum
- Idan wukarka na da kyau, ba za ka gwada a jikinka ba
- Idan yaro makaho ne, babba mai jagora ne
- Idon da ya ga sarki ba ya tsoron galadima
- Ikon Allah, na zaune ya fadi
- Ikon Allah sai kallo
- Ilimi garkuwan dan adam
- Ilimi gishirin zaman duniya
- Ilimi mai yaye jahilci da duhun kai
- In Allah Ya taimake ka, ka taimaki na baya gare ka
- In Allah Ya ba ka ka gode sai ya kara maka
- In an gaji ko a rana a huta
- In an bi ta barawo, a bi ta ma bi sawu
- In an bugi kura a ka, an kara ma ta karfi ne
- In an ciza sai a hura
- In ana dara, fidda uwa ake
- In ana ta kai ba a ta kaya
- In ana fada ba a duban rauni
- In ana son ka da laifi, ko ruwa ka ashiga sai a ce ka tada kura
- In ajali ya kira ko ba ciwo sai an je
- In ba karamabani ba, me ya kai doki mahauta?
- In ba rami me ya kawo maganan rami?
- In ba ki da gashin wance, me ya sa zaki yi kitson wance?
- In ba ruwanka cikin Magana, ka bi ta da shiru
- In baka shan fura, bari damun ta
- In baka isa ba ka isa da kanka
- In baka son mutum, baka hana shi dariya
- In baka san gari ba, saurari daka
- In ba ka da kudi, me ya sa za ka kira mai alewa?
- In ba ka iya kyauta ba, ka bai wa mai baka
- In bera na da sata daddawa da wari
- In da duniya tana da gaskiya da ba a bar mazari tsirara ba
- In dambu ya yi yawa ba ya jin mai
- In duka yayi yawa, na ka ake tarewa
- In duniya ta ki mutum, sai kunkuru ya tsere wa karensa
- In ganga ta cika zaki, ta kusa fashewa ne
- In gemun dan uwanka ya kama da wuta, shafa wa naka ruwa
- In gemun dan uwanka ya kama da wuta, ka taimaka a kashe
- In gara ta ci tukunya, mai gora ya rataye abinsa
- Ingarma ke gudu, kura sai wahala
- In ka bi daga –daga na kurya kan sha kashi
- In ka ji gora na rawa ba cikakkiya ba ce
- In ka ji gangami da labari
- In ka iya ruwa ba ka iya laka ba
- In ka iya ruwa ba ka iya yashi ba
- In ka na son sauri aiki yaro inda yake so
- In ka na cin kasa, kiyayi ta shuri
- In ka ga kurma na gudu, ka bi shi, ganau ne
- In ka ga dan kunne a rumbu, idan ba a shiga ba an leko
- In ka ga kura da rana, me ya sa za ka bari ta cije ka?
- In ka ga ruwa a ido, daga ka yake
- In ka ga kuda daga dauda ta ke
- In ka ga ki gudu sa gudu bai zo ba
- In ka ga maciji a mike, ba za ka ce zai yi sara ba
- In ka san wata, baka san wata ba
- In ka sha rana wani zai sha inuwarka
- In kasuwa ta ki, sai ka kasa barkono a ce ba yaji
- In kunne ya ji gangan jiki ya tsira
- In kana da kyau ka kara da wanka
- In kida ya sauya, sai rawa ya sauya
- In kwana ya kare, ba tsimi ba dabara
- In man shanu ya lalace, sai a toya yaki kanshi
- In maye ya manta, uwar diya ba za ta manta ba
- In maciji ya sari mutum, in ya ga tsumma sai ya gudu
- In mai gado ya zo mai tabarma sai ya nade
- In makaho ya ce bai ganin rana, ba ya sauya komai
- In makaho y ace a yi wasan jifa, ya taka dutse ne
- In nayi maka rana, kada ka yi min dare
- In nono na da dadi, bumba na da gardi
- In rakumi da girma, kayansa ma da yawa
- In ruwa yayi ruwa, kunkuru ma wurin fakewa zai nema
- In rana ta fito, tafin hannu baya kare ta
- In sayar da akuya, ta zo tana ci mini danga?
- In ta yi ruwa rijiya, in ta ki masai
- In tukunya ta tafasa, ba ta barin gefe
- In ungulu ta biya bukata, zabuwa ta je da doronta
- In wata ya yi fari a kasa zai nuna
- In za ka gina ramin mugunta, gina shi gajere
- In za ka yi Magana da kurma, sai ka zungure shi
- In zamani ya dinka riga, ta ishi kowa
- Ina akuya za ta da kayan taiki?
- Ina amfanin badi ba rai?
- Ina ruwan kifi da kaska?
- Ina ruwan kallo da gajiya?
- “Ina ji a jika” kabiyar mahauci
- Ina tukunyar damo, ina na guza? Duk daya ne
- Inda ba kasa, nan ake gardamar kokuwa
- Inda biri ya san ashana, da ya kona gari
- Inda aka san darajar goro, ake masa tanadin ganye
- Inda baki ya karkata, nan miyau kan zuba
- Inda ba ci ba sha, ruwa magani ne
- Inda badon wari ba, tafarnuwa ta fi zinari daraja
- Inda fata tafi taushi akan bi ta da jima
- Inuwar giginya, na nesa ke shan sanyinta
- Inuwar bagaruwa ga sanyi ga kaya
- Iska na wahalar da mai kayan kara
- Itatuwa abincin giwa in ta ki ta kwana da yunwa
- Iya rai iya buri
- Iya rai iya gani
- Iya ruwa fid da kai, mai fid da kanshi sai gwani
- Iya yi ci-rani ba miji
- J
- Ja da baya ga rago ba tsoro bane shirin fada ne
- Ja ya fadi, ja ya dauka
- Ja maganin mushen doki
- Jahilci ya fi duhun dare
- Jahilci ya fi hauka wuyar warkewa
- Ji da kai kamar bulalar maye
- Jifan mahaukaci yakan fada wa mai tsautsayi
- Jikan jatau, bakin mutum ya ga fari
- “jiki magayi” shan tabar mai koyo
- Jita-jita karatun bamaguje
- Jimina ko ya yi cara, ba za a kirashi zakara ba
- “jiya ba yau ba” tsohuwa ta ga tatakwashi
- Jinkirin tuba karamin kafirci ne
- Jin labarin gwani, ya fi ganin raggo
- Jin kunyar maras kunya asara ne
- Jumma’a da za tayi kyau tun daga labara ake gane ta
- Jure fari sai tofa
- Juyi tara sai wake
- K
- Ka ki ni dubu su so ni
- Ka so makiyinka, sai ya rasa mafita
- Ka bar ganin griman kuka, bagaruwa Ita ce babba
- Ka da zomo biyu su gaza miya
- Ka da cibi ya zama kari
- Ka da reshe ya juye da mujiya
- Ka da allura ta tono garma
- Kada ka sake ruwa ya cika a wankin kalwa
- Ka da ka yi saka da mugun zare
- Ka da ka riga malam masallaci
- Ka da mage ba yanka ba
- Ka da hangen hadari ya sa a yi wanka da kashi
- Ka da ka zama kanywa uwar gami
- Ka da kunkuru yayi wa bushiya kafa
- Kato da gora maganin zauna gari banza
- “kamar da kasa” inji mai ciwon ido
- Kanari mai dadin kuka, duk wanda ya ji sai ya waiga
- Kadangaren bakin tulu a kashe ki a fasa tulu, a bar ki, ki bata ruwa
- Kaikayi koma kan mashekiya
- Ka kiyayi furfura, ko da ta arne ce
- Kainuwa dashen Allah, ba dashen mutane ba
- Kafa baya zuwa inda zuciya bata so
- Kafar ungulu mai bata miya
- Kafin ka ga biri, biri ya gan ka
- Karfen aska sai zababbe
- Karambanin akuya gaida kura
- Karen bana shi ke maganin zomon bana
- Karfe daya ba ya amo
- Karkatacciyar kuka mai dadin hawa
- Da Kai da kaya, duk mallakan wuya ne
- Kama da wane ba ta wane
- Kara da kiyashi daukar maras sani
- Karen da ba ka ciyar da shi bai jin kiranka
- Karya fure take ba ta ya’ya
- Karatu farkonki madaci karshenki zuma
- Kagara gari ya waye ke kawo tsawon dare
- Karshen lalacewa, namiji da guda
- Kallo ya koma sama, shaho ya dauki giwa
- Kare yayi haushi hakoran shi sun zube
- Kare mai zalama, a ba shi kan giwa
- Kayan nama ba zai kasha kuraba
- Karambanin bako a kori barawo ya kai gudummawa
- Karamin sani kukumi ne
- Karamar zuci, gwauro da turaka
- Karamin goro ya fi babban dutse
- Kasuwa a kai miki dole
- Kashin kare ba ya taki
- Kasha baya samar da jini sai tsoka
- Kazar kwanci me kwakwazo
- Kaza tana taka ‘ya’yanta badon ki ba, sai don suyi kwari
- Kaza mai ‘ya’ya ke tsoron shirwa
- Kaza ba ta da nono, Allah ke ciyar da ‘ya’yanta
- Kere na yawo zabo na yawo watarana a hadu
- Koshin wake na ruwa ne
- Karshen alewa kasa ne
- Karya linzamin shaidan
- Kidan jajibiri baya tada hankalin kare
- Kitse mugun nama bai nuna ba ya kashe wuta
- Kifi na ganin ka mai jar koma
- Kifin fadama ba ya gasa da na gulbi
- Kishi kumallon mata, in ya motsa sai an haras
- Kibiyar aljali sulke ba ya tsare ta
- Kiwon kai ya fi kiwon dabba
- Ko a kwara da tsibiri
- Ko biri ya karye zai hau rumbu
- Ko ba a gwada ba linzamii ya fi karfin bakin kaza
- Ko ba a yi don mai gayya ba a yi don mai gona
- Ko da girgiza kurna ta fi magariya ‘ya’ya
- Ko da kudinka, sai da rabonka
- Ko da washi gatari ba zai yi wa dutse komai ba
- Ko shamuwa ta sha ruwa ba za ta zama shirwa ba
- Ko gobe ruwa na maganin dauda
- Ko yaro a goye, ya san kura
- Komai dadin karya, gaskiya ta fi ta
- Komai dadin kida shiru ya fi shi
- Komai dadin guda, ba a yi ma asara
- Komai daki ya samu albarkacin kofa ne
- Komai gudun barewa a hannun mai dawa zata kwana
- Komai hasken farin wata, dare abin tsoro ne
- Komai kankantar tsuntsu, ba za a ci shi da gashi ba
- Komai kasaitan agola ba zai yi gado ba
- Komai na duniya kararre ne, ban da ikon Allah
- Komai nisan gari akwai wani a gabansa
- Komai nisan gari, masoyi baya ganin nisan sa
- Komai nisan jifa, kasa zai fado
- Komai nisa dare gari zai waye
- Komai saurin ungwarzoma ta bari a haihu
- Komai wuya da mai jin dadi
- Komai iya surfe ba za ‘a daka dutse ba
- Komai lalacewar masa, ta fi kashin shanu
- Komai laushin gari ba zai hana a tankade ba
- Komai ramar giwa ta fi Kwando goma
- Komai yawan kitse baya huda hanji
- Koma ya ji ban da barkono a ido
- Komai ya yi farko zai yi karshe, ban dan Idon Allah
- Komai yayi fari yana da nagarta, ban da kurkunu
- Komai yayi zafi, zai yi sanyi
- Komai ya sami shamuwa, watan bakwai ne ya ja masa
- Komai zaka fadi, fadi gaskiya komai ta ja maka ka biya
- Komai zafin abinda kake ci, wuta ta fi shi
- Komai zafin ruwa, yana kasha wutar kara
- Kowa da irin kiwon da ya karbe shi makwabcin mai akuya ya sayi kura
- Kowa da masoyinsa, jaki ya ga toka
- Kowa ya dogara ga Allah, kada ya ji tsoron mahassada
- Kowa ya bar gida, gida ya bar shi
- Kowa ya daka ta rawar wani, ya rasa turmin daka tasa
- Kowa ya daka ta bado, ruwa ya ci shi
- Kowa ya iya allonsa, ya wanke
- Kowa ya ci ladan kuturu dole ya yi mashi aski
- Kowa yayi hakuri za a yi da shi
- Kowa ya ci zomo ya ci gudu
- Kowa ya ce zai kona rumbunsa, ya san inda toka ke daraja
- Kowa ya debo da zafi bakin sa
- Kowa ya hadiye tabarya, ya kwana a tsaye
- Kowa ya raina gajere bai taka kunama ba
- Kowa ya sayi rariya ya san za ta zubda ruwa
- Kowa ya sha inuwar gemu baya makogwaro
- Kowa ya goya kare ya san yadda zai yi da bakin
- Kowa ya tuna bara bai ji dadin bana ba
- Kowa yayi kwalliya ya na son yabo
- Kowa ya kwana lafiya shi ya so
- Kowa ya ga gidanka ka ga nasa
- Kowa ya so uwa, ya so danta
- Kowa yayi da kyau, ya ga da kyau
- Kowa yayi fari ya gama kyau
- Kowa ya hana ka dakin kwana, dole da safe ya gan ka
- Kowane mai rai ajizi ne
- Kowane kwarya da abokin burminta
- Kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi
- Kowane gauta ja ne, sai dai bai ji rana ba
- Kowane bakin wuta da nashi hayaki
- Kosawa da arziki jahilci ne
- Kora da hali ya fi kora da sanda
- Kuturu ba bakon miki ba ne
- Kuda wajen kwadayi a kan mutu
- Kudi masu gidan rana
- Kudin cuta, na mai magani ne
- Kukan kurciya jawabi ne, mai hankali ke ganewa
- Kukan ciki ya bambanta da na gwaiwa
- Kulba na barna ana cewa jaba ne
- Kula da kaya ya fi ban cigiya
- Kuliya manta sabo
- Kunnen giwa ya fi karfin talla
- Kunne ya girmi kaka
- Kura bata san kudin akuya ba
- Kura da shan bugu gardi da kwashe kudi
- Kura, ga tsoro ga ban tsoro
- Kura kin cin naki kin ci na dangi
- Kura ta san gidan mai babban sanda
- Kushe da hasssada ba su hana bawa rabon sa
- Kushewar badi sai badi
- Kwai a baka ya fi kaza a akurki
- Kwace goruba a hannun kuturu ai ba wuya
- Kwaryar kira jure tarkace
- Kwarya ta bi kwarya, in tabi akushi ta fashe
- Kwarya dole ta fito ranar shika
- Kwado ke nan ba da cizon dan kowa
- Kwadayi, mabudin wahala
- Kyaun da, ya gaji ubansa
- Kyaun da, ya fi ubansa
- Kyaun tafiya, dawowa lafiya
- Kyanwa a garin wasu damisa ne
- Kyanwan lami ba kuka ba yakushi
- Kyaun kwado aci da yaji
- Kyauta ba ya hana arziki
- L
- Labarin dare, a tambayi kura
- Labarin gizo ba ya wuce koki
- Labarin zuciya, a tambayi fuska
- Laraba ta bawa ranar samu
- Laifi ba shi da ubangiji
- Laifin wani ba ya shafar wani
- Laifi tudu ne, ka taka naka ka hangi na wani
- Lafiyar namiji gadon bayansa
- Lafiya uwar jiki, babu mai fushi da ke
- Laifin babba rowa, laifin yaro kwiya
- Laifin kura dubu, banda satan akuya
- Lallai, wata sabon gani ne
- Lokacin abu a yi shi
- Linzami da wuta maganin sangartaccen doki
- Linzami ya fi karfin bakin kaza
- M
- Maciyinka ba ya ganin ramarka
- Mafarin hauka, tsirta yawu
- Madoki kusa maciji nesa
- Madugu uban tafiya ne
- Magana ba madogara, yin kwalli da tabarya
- Makaho na da ido amma ba na ganin gari ba
- Magana ba kaya ba ne, in ka yi sai a yi maka
- Maganar fari shi sarki kan kama
- Magana zarar bunu ce, in ta fita ba a mayarwa
- Magana baya fasa kasha, yakan bata zuciya
- Maganin biri, Karen maguzawa
- Magana ai jari ce
- Magori, wasa kanka da kanka
- Mai abin fada ba ya fada
- Mai arziki ko a kwara ya sai da ruwa
- Mai akuya ya bi dare, balle mai kura?
- Mai bunu, bay a zuwa gudummawar gobara
- Mai cinikin shan zuma, in reshe bai karye da shi ba, kwarya ta fashe masa
- Mai cininkin sara, shi ke sanin faduwar gatari
- Mai cinikin karya, yay i biyan gaskiya
- Mai cin dambu, ba a ce masa ga ruwa
- Mai daki shi ya san inda yake zuba
- Mai dan kwikwiyo shi ke da kare
- Mai dokan barci, ya bingire da gyangyadi
- Mai farautar kura, ba ya zuwa da kare
- Mai gyara ba ya barna
- Mai gudun gara ya fada zago
- Mai hali ba ya barin halinsa
- Mai hankali shi ke gane sawun gwauro a kasuwa
- Mai hankali shi ke bai wa kaza ruwa da damina
- Mai hankali shi ke kyautata wa bako
- Mai hankali ke gane furfurar tunkiya
- Mai ido daya ba zai yi nadama ba, sai ya ga makaho
- Mai ido da rami da wuri yake kuka
- Mai ido a ka ba a nuna mashi sama
- Mai kyauta ba ya rasawa
- Mai kyau moran kowa
- Mai kaza a aljihu, ba ya jimirin as
- Mai kaza a akurki ba ya jimirin as
- Mai kaya shi ke tsoron fashi
- Mai karambani shi ke biyan bashin kaka
- Mai laya kiyayi mai zamani
- Mai madi ke talla, mai zuma sai a same shi a saya
- Mai neman gada, in ya ga akuya ya huta
- Mai nema na tare da samu
- Mai roko surukin mai rowa
- Mai rai ba ya rasa motsi
- Mai raina kadan barawo ne
- Mai rabon ganin badi ko ana ha maza ha mata sai ya kai
- Mai rabon ganin badi ko ana ruwan masu, sai ya kai
- Mai rabon shan duka baya jin kwabo sai ya sha
- Mai rawar kai ba ya digirgire
- Mai rigar tsumma baya shiga gonar karangiya
- Mai son kuka, an jefe shi da kashin awaki
- Mai son dan tsuntsu shi ke bin sa da jifa
- Mai tarko baya ta da kara
- Mai takama da madi ya koma shan zuma
- Mai uwa a murhu, ba ya kwana da yunwa
- Mai uwa a murhu, ba ya cin tuwonsa gaya
- Mai waina da ruwa, balle ta samu mai?
- Mai zuciya ake gaya wa biki ba mai kudi ba
- Mai da ruwa rijiya ba laifi ba ne
- Masanin dare duhu ne
- Masu kumatu su ke da yawu
- Masha ruwa magirmi
- Matambayi ba ya bata
- Matar mutun kabarinsa
- Matar na tuba ba ta rasa miji
- Matar shige ba ta daraja
- Matan zamani ba tukwane ba, balle a kwankwasa a ji wanda ta fi kwari
- Mahakurci mawadaci
- Maras gaskiya ko cikin ruwa ya yi jibi
- Maras son jini ba zai je mahauta ba
- Maras kunya ke cin tuwon biki har ya kare
- Makaho bai san ana ganin sa ba, sai an zungure shi
- Maso ganin dare, ya bi kura
- Maso abinka ya fi ka dabara
- Maza gumban dutse ne
- Man kadanya ba zai zauna a tandu ba
- Me ya kai fura zani? In ba kazamiyar damu ba
- Me ya hada kifi da kaska?
- “Me aka yi” an ga mahaukaciya ta shiga rawa
- “Me ake jira” gwari ya yi toshi
- Me iska za ta yi da kayan kara?
- Me na ci na ashan zanyi ramakon azumi?
- “Me zan ce” zanin aro ya kone?
- Me kuturu zai yi da zoben tsintuwa? Sai dai ya ba da cigiya
- Mu tafi a hankali, mu yi guzuri da katon sanda
- Muje mu gani, maganin mai karya
- “Muje zuwa” mahaukaci ya hau kura
- “Mulkin mallaka” biyan bashi da dan kishiya
- Munduwar wuya, ana son zarewa ana tsoron jin ciwo
- Mugu shi ya san kawancin mugu
- Muguwar miya ba ta karewa a tukunya
- Mugun dafi a bar wa macizai
- Mugunta fitsarin fako
- Mun gaji da kyau hali muke nema
- Munafunci dodo yakan ci mai shi
- “Muna wasa ne” gwari ya ba da magani an mutu
- Mummunan farko yakan yi kyakkyawan karshe
- Mutunci madara ne, idan ya zube ba a kwashewa
- Mutunci ya fi kudi
- Mutuwa rigar kowa
- Mutuwar yawa kaka
- Mutuwar uwar adashe ba karshen adashe ba ne
- Mutuwar zuciya gai da makiyi da safe
- Mutuwa karar kwana, fashi barnar aiki
- Mushen gizaka, ta mutu amma ta na ba yara tsoro
- Na shiga ban dauka ba, ba ta fidda barawo
- N
- Naka naka ne, ko ya ci namanka ba zai tauna kashinka ba
- Naci kamar kwarton kusa
- Naci ai damben kuturu ne
- Na taba ki da alheri, kishiya ta taba kishiya da bakin wuta
- Na ji dadi shi ne gari ban a saba ba
- Na gaban wuta shi ke jin duminta
- “na ga abinda ya ishe ni” in ji kishiyar mai mata tara
- Nagari na kowa mugu sai mai shi
- Namiji barkono, sai an dandana ake sanin yajinsa
- Naman sallah ko wanda ba shi da gida zai ci
- Nan gani nan bari farar tumfafiya
- Nasara na wajen Allah
- Na zaune gwanin kokuwa
- Na zaune bai ga gari ba
- “Na zo ke nan” shigar sojan Badakkare
- Noma tushen arziki
- Noma yanke talauci
- Noma na duke tsohon ciniki
- Nuna sani a kasuwar jahilai, wauta ne
- Nuna yatsa, ba shi ake kira nuni ba
- Nuni a cikin nishadi
- R
- Ra’ayi kukan jaki ba a iya hanawa
- Ra’ayi riga, kowa da irin ta sa
- Rabon akuya tsari, farau-farau sai mai gata
- Rabon kwado baya hawa sama
- Rabo ajali ne
- Raba bawa da arziki sai Allah
- Raba da da mahaifi sai Allah
- Raba ni da cusa kai ba kwarjini
- Rai dangin goro ne, ya na son ruwa
- Raina kama ka ga gayya
- Raina da kuna, kaza ta yi shekan dari
- Raon Malam ga kitse, ga arha
- Rago aka sani da tunkuyi ba kare ba
- Rakumin dawa ba’a hawan shi ba a dora masa kaya
- Ramakon gayya tafi ta gayya zafi
- Ramin karya kurarre ne
- Ramin shuka ba zurfi gare ta ba
- Ran sarki ya dade, bay a hana shi mutuwa
- Rana mudun aiki ne
- Rana ba ta karya sai dai uwar diya ta ji kunya
- Ranar wanka ba a boyon cibi
- Ranar yanka ba a boye wuka
- Rashin hakuri shi ya sa ake me aka shuka?
- Rashin sani ya sa makaho taka sarki
- Rashin sani Karen gwauro ya kori bazawara
- Rashin hakurin ‘ya mace, ta haihu a gidan iyayenta
- Rashin sani ya fi dare duhu
- Rijiya ta ba da ruwa guga ya hana
- Rijiyar mai hassada, wawa ke shan ruwanta
- Rijiya gaba dubu, duk wanda ya gina ki ya bai wa Allah
- Rigakafi ya fi magani
- Rigen zuwa fada ba shi ne ganin sarki ba
- Rigen zuwa kasuwa ba shi ne riba ba
- Rimi adon gari
- Rikon mahaukaci sai sarki
- Roki maroki ka ga rokkakiyar rowa
- Rufin asirin mai loma, ka da a yi walkiya
- Runbun tunani bakin ciki ne yakan cika shi da tokar tunanin
- Rumfar kara ba ki boye hayaki
- Ruwa ba sa’an kwanda ba ne
- Ruwa ba ya tsami banza
- Ruwa da dorina da kada bako ke wanka cikinta
- Ruwan dare gama duniya
- Ruwa iya wuya maganin mara son wanka
- Ruwan tsami ba ya kauri
- Ruwa ya kare wa dan kada bai gama wanka ba
- Ruwa shuka ya kauda na sassabe
- Ruwan ido ba zai yi kwaben kasa ba
- Ruwan wuta mai jiran bacin rana
- Rufe ido ba makanta ba ne
- Rufin asiri sai Allah
- S
- Sa’a wanda ta fi manyan kaya
- Sa’a ta fi sammako
- Sabo da yi, guda a gidan mutuwa
- Sabo da yi gawa da gatsine
- Sabo da kaza ba ya hana yanka ta
- Sabo da maza jari ne
- Sai an gwada akan san na kwarai
- Sai an huda kasa akan samu ruwa
- Sa kai, wanda ya fi bauta ciwo
- Sakaina gwanin iya ruwa
- Sai hali ya yi daidai ake abota
- Sai an ji dadin gwanda ake tanadin irinta
- Sai bango ya tsage, kadangare ke samun wurin shiga
- Sai an sha wuya akan tuna Allah
- Sa rai da ci shi ke kawo jin yunwa
- Sarfa gandun baiwa
- Sarautar Allah, kare a bakin zomo
- Sara da sassaka, ba ya hana gamji tofo
- Sarki goma zamani goma
- Sarkin yawa ya fi sarkin karfi
- Sakin na hannu kama na guje kamun gafiyar baidu
- Sallah ta wuce ta bar wawa da bashi
- Sallah mai biki daya rana
- Samu ya fi iyawa
- Samun shiga, barawo da sallama
- Sama ta yiwa yaro nisa, sai dai ya tada kai ya yi kallo
- Sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba a je ba
- Sannu ba ta maganin harbin kunama
- Sanin asali ya sa kare cin alli
- Sanin gaibu sai Allah
- Sanin asirin ciki sai hanji
- Saniya da shafa ake tatsarta
- Sana’a goma maganin gasa
- Sanin darajar toka, ke sa mutum kona rumbunsa
- Sandar girma ba a zunguri da ke sai nuni
- Sandar jifan kura da safe ake dauko ta
- Sandar da aka kori tsiya da ita ba a yarwa
- Sawun giwa ya take na rakumi
- Sauri ya haifi nawa
- Sau daya gyadar makaho ya kone, na biyu ya ci abinsa danye
- Saurin fushi shi ke kawo dana sani
- Sauki, ture zabo kwashe kwai
- Sauki baya hana riba
- Sata a gidan barawo rance ne
- Sata hali ne, mai yinta komai wadata sai ya yi
- Sayen na gari mai da kudi gida
- So duka so ne amma son kai ya fi
- So mai hana ganin laifi
- Son Allah ya fi taron dangi
- Son kira, kamar bazarawa
- Son kowa, kin wanda ya rasa
- Son jiki kamar gyambo
- Son jiki kamar mage
- Son maso wani cuta ne
- Son zuciya bacin zuciya
- Soyayya gamon jini ne
- Soyayya ta fi kudi
- Shari’a kamar kayan aras take, ba ta son garaje
- Sharia’a sabanin hankali
- Shashanci yin gaba da bako
- Shinfidar fuska ta fi shimfidar tabarma
- Shan ruwa ba ya hana mutuwa
- Shakuwa, mai neman rai
- Shagwaba, tarwada da kukan kishin ruwa
- Shegen kaya, dare akan bi da shi
- Shiru ka ke ji, an aiki bawa garin su
- Shiru ka ke ji, mai kalangu ya fada rijiya
- Shure-shure ba ya hana mutuwa
- Shiga da fita ba ya yi wa azure komai
- Shirin zaune ya fi na tsaye
- Suna linzami ne, mai shi yake bi
- T
- Taba ta bambanta da garin goro
- Tabarmar kunya, da hauka ake nade ta
- Ta faru ta kare, an yi wa mai dami daya sata
- Ta faru ta kare, an bai wa mayya karbar gaisuwan mutuwa
- Ta faru ta kare zanin aro ya kone
- Tafiya da gwani mai dadi, idan gwanin bai lalace ba
- Tafiya mabudin ilimi
- Tafiya sannu kwana nesa
- Tallar turmi ba a sayar ba sai kaya
- Ta Malam ba ta wuce amin
- Tambarin talaka cikinsa
- Tauraruwa mai wutsiya ganinki ba alheri ba
- Takalma lafiyar kafafu
- Takalmin kaza, mutu ka raba
- Takanda ai ba kasha ba ne
- Takaici mai sa babba kuka
- Tashin hankali cire wando ta ka
- Tasha ba ta haihuwa sai yaye
- Ta yaro kayu take ba ta karko
- Tun daga gida, damara ya kwance
- Tulu shi ke yawo, randa na zaune
- Tun ran gini ran zane
- Tunani mai sa amarya kuka
- Tuntuben kashi, idan ba a ji rauni ba rayuwa ta baci
- Tuntuben harshe, ya fi tuntuben kafa zafi
- Tururuwa bata gudun abin kunya
- Turmin tsakar gida sha lugude
- Tsabta cikon addini ne
- Tsakanin Dan Adam da kudi
- Tsintacciyar mage bata mage
- Tsintsiya madaurin ki daya
- Tsautsayin takaba, auren majinyaciya
- Tsalle daya shi ke jefa mutun rijiya
- Tsare gida mutuncin dandi
- Tsoro na daji, kunya na gida
- Tsokanar fada ne an cewa gwauro yaya iyali?
- Tsugune bata kare ba, an sayar da kare an sayi biri
- Tsakuwa a ruwa sai gwani
- Tsuntsun da ya kira ruwa, shi ruwa kan doka
- Tsumagiyar kan hanya, fyadi yaro, fyadi baba
- Tsuntsu mai wayo a wuya ake kama shi
- “To wanka na ke”, mahaukaci ya fada rijiya
- Tuwon kasa ba zai yi maganin yunwa ba
- Tuwon tulu mai wuyan kwashewa
- Tuwon kasa na kare ne, tuwon nama sai kura
- Tuwon girman miyan sa nama
- Turbar sama sai tsuntsu
- U
- Ungulu ba kazar kowa ba ce, don ba a saka ta a akurki
- Ungulu ta koma gidanta na tsamiya
- Uwa ta fi uba, ko da uban sarki ne
- Uwar raggo ake wa barka
- Uwargida sarautar mata
- W
- Wata sabon gani
- Wanda bai ji kunyar hawan jaki ba, ba zai ji kunyar kayar da shi ba
- Wanda bai ci arzikin wani ba sai ya mutu matsiyaci
- Wanda bai sami tarbiya a gida ba duniya za ta koya mashi
- Wanda bai yi sharan masallaci ba, ya yi na kasuwa
- Wanda kunama ya harba, in ya ga kyankyaso sai tsalle
- Wanda rakuminsa ya bata ko akurki sai ya leka
- Wanda ruwa ya ci ko takobi aka bas hi zai kama
- Wanda ya yi nisa ba ya jin kira
- Wanda ya jira kahon kare ya makara
- Wanda ya kai ya komo, shi ke sai da ruwa a kogi
- Wanda ya ci zomo, dole ya yi aman-gashi
- Wanda ya ci zomo, ya ci gudu
- Wanda ya san matsalar abinci, shi ke tanadin hatsi
- Wanda ya ki neman ilimi, jahilci zai kashe shi
- Wanda ya riga ka barci, zai riga ka tashi
- Wanda ya ki shan ruwan kwano, ba zai shiga rijiya ya sha ba
- Wanda ya saba zama a murhu, wataran zai kone
- Wanda ya yi hakuri da kunun maraice, yakan ga tuwon yamma
- Wanda ke inuwa bai san wani na rana ba
- Wanda ya daure kura shi ya san yadda zai kwance ta
- Wandon karfe, kowa ya sa ya kwana a tsaye
- Wanka da gari baya maganin yunwa
- “Wani abu haka”, wai gwanin rawa ya fadi
- Wani ma ya yi rawa balled makadi?
- Wani hani ga Allah baiwa ne
- Wani kaya sai amale, jaki ba zai iya ba
- Wani irin dare ne jemage bai gani ba?
- Wani tsuntsun na gudun ruwa, agwagwa a ciki ta ke kwana
- Wanzami ba ya son jarfa
- Waka bakin mai ita ta fi dadi
- Wake daya mai bata gari
- Wake ya nuna damo ya makance
- Wai kwana nawa ne? maye yayi amariya
- Waiwaye adon tafiya
- Wargi wuri yakan samu
- Wawa shike rena mafari
- Wayo ya san na ki
- Wayon aci ne aka kori kare daga gindin dinya
- Wukar fiddar giwa ba kaifi gareta ba sai girma
- Wuyar noma kunyar fari
- Wutsiyar rakumi ta yi nesa da kasa
- Wuni da Malami ya fi shekara da jahili
- Wuya mai sa a kwana bayan suruka
- Y
- Yaba kyauta tukwuici
- Yabon gwani ya zama dole ko da makiyi ba ya so
- ‘Yan mata adon gari
- Yara manyan gobe
- Yaro tsaya matsayin ka inka ki ka gane kuren ka
- Yaro ko yana wasa da kare ya kiyayi damisa
- Yaro bai san wuta ba sai ya taka
- Yaro da gari abokin tafiyar manya
- Yaro man kaza, in ya ji rana sai ya narke
- Yaro da rarrafe kan tashi
- Yaro wutar kara ne sai da kulawa
- Yaro a goye bai san nisan tafiya ba
- Yaro ya san kura, da ganin birni ya san ya fi garinsu
- Yaro bata hankalin dare ka yi suna
- Ya kamata kwalliya ta biya kudin sabulu
- Yau da gobe sai Allah
- Yau gareka gobe ga wani
- Yau fari gobe baki birgiman hankaka
- Yautai mugun tsuntsu
- Yawan shekaru ba shine wayo ba
- Yawa mai sa masu zare jan dutse
- Yawan mutune sune kasuwa, ba tarin rumfuna ba
- Yawan gaisuwa ya fi yawan fada
- Yawon dare bana dan akuya ba ne
- Yawon duniya shigar zungurun kadangare
- “Yaya na iya da raina”, mummuna ya ga matar aure
- ‘Ya’an marke kun nuna kun waste
- “Yay azan yi da abin da ya gagari wuta” in ji kishiyar konanna
- Yi nayi, bari na bari, shine aure
- Yi na yi, bari na bari, shine biyayya
- Z
- Zafin nema ba ya kawo samu
- Zancen banza Magana ba iko
- Zancen banza, zakara ya taka wuka
- Zance da dan gari ilimi ne
- Zakaran da Allah ya nufa da cara, ana muzuru ana shaho sai ya yi
- Zakaran ka rakumin ka
- Zakara mai neman suna, bada kwaya ka ci tsakuwa
- Zakara a rataye ba ya cara
- Zalama, a ci kasuwa da kai ka koma kale
- Zalbe mai cinikin kasada
- Zaman duniya hakuri, makiya su fi masoya
- Zaman lafiya ya fi zama dan Sarki
- Zama da munafuki sai dole
- Zama wuri daya tsautsayi, inji kifi
- Zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin kai
- Zato zunubi ko da ya zamo gaskiya
- Zarton yankan dutse ba a masa washi
- Zo mu zauna zo mu saba ne
- Zo mu ci tuwo yafi tuwon dadi
- Zomon daji shi ya san hanyar tserewa kare
- Zomo ba ya fushi da makashin sa sai maratayin sa
- Zomo ba ya kamuwa daga zaune
- Zumunta a kafa take
- Zuciya mai sa dana sani
- Zuciya ke gani, ba ido ba
- Zuciyar mutun birnin sa
- Zuwa da wuri, ya fi zuwa da wuri-wuri.
- Subcategories & Pages in category "Karin Magana"
- Subcategories
- This category has only the following subcategory.
- R
- Resources/Hausaland Tales from the Nigerian Marketplace
- Pages in category "Karin Magana"
- The following 46 pages are in this category, out of 46 total.
- A
- A yi a gama ta fi tak'ama gobe a komai
- B
- bai taka karya ya karya ba
- bayan ci zama tsegumi tafiya rashin kunya
- bbchausa verticals/039 proverbs reflect who we are
- C
- ci maka tuwo a ƙwarya
- D
- da sauran rina a kaba
- Da wasa ake gayawa wawa magana
- duk wanda yayi zagi a kasuwa yasan da wanda yake yi
- G
- garma
- gurbin ido ba ido bane
- gyara kayanka baya zama sauke mu raba
- H
- hakkin da ka raina shi zai tsone maka ido
- Hannu d'aya ba ya d'aukar d'aki
- hannunka mai sanda
- hawa makahon doki
- I
- itacen gidanmu, inuwa na gidan wani
- J
- jari
- Juma'ar da za tayi kyau tun daga Laraba ake ganeta
- justified
- K
- kada a yi tuya a manta da albasa
- kai labari
- kamar da gaske, karuwa taga noman dan koli
- karin magana
- komai ya yi farko zai yi k'arshe
- kowa da mutanensa, jaki ya ga toka
- Kowa ya bar gida, gida ya bar shi
- Kulba na barna ana cewa
- kura ga kwadayi ga tsoro
- kura tana ƙoƙarin ta kai bango
- kwalliya ta biya kud'in sabulu
- M
- Mai ci da uwa, bashi kukan sudi
- mai tarkon tsuntsaye, baya daga kara
- P
- proverbs
- R
- Ranar biyan bukata rai ba abakin komai yake ba
- rigakafi yafi magani
- rijiya tabada ruwa guga tahana
- ruwan dare
- S
- sawun keke ba'a gane gabanka
- T
- taya ni figa, uwar kishiya ta zama kaza
- tsalle daya ake yi a shiga uku, a kuma yi dubu a kasa fita
- tsintsiya madaurinki daya
- tsintsiya maɗaurinki ɗaya
- Tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka
- W
- Waiwaye adon tafiya
- wuce gona da iri
- Z
- zafin nema baya kawo samu
Fashi baki akan Karin magana kafin ayi daran akai kwandi
ReplyDelete