-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Kalaman Soyayya 2022/2023

Kalaman Soyayya 2022/2023

Kalaman Soyayya 2022/2023

Shin kana daya daga cikin Samari Masu neman Budurwa wadda zasu aura? Ko kana shan Wahala Wurin tsayar da budurwa da kake so ka aura,?

Nasan Soyayya itace take Ranka Wannan yasa kake ƙaranta Wannan Rubutun.

To inda Kana Soyayya kuma kana cikin Samari Masu yin Soyayya Yana da kyau Duk Saurayi Yasan Cewa Budurwa Sai da Kalaman Soyayya

Idan baka iya yimata Kalaman Soyayya to za,a Barka A baya Wurin Soyayya, Wannan Ita Magana ta Gaskiya,

Domin sau dadama ansha amshe ma saurayi Budurwa ta Dalilin rashin iya kalaman soyayya.


Wannan ne yasa Muka Tace, Muka Darje, Muka tsara muku Kalaman Soyayya Masu Dadi da Ratsa jikin Masoya.


Gasu a nan kasa Asha Karatu Lafiya.


Abubuwa kaɗan ne suke da daraja a wurina cikin wannan duniyar, ɗaya daga cikin su shine Murmushi ki, my priceless gift.

Gari ya Waye, sabuwar rana ta fara, Ina Farin ciki da Nishadi saboda ina da ke a cikin rayuwata.


Ina jin Soyayyar ki Wata Kyauta ce agareni da ban taba samun kyauta irin ta ba a rayuwata, my super lady.


Na dade ina kallon taurarin samaniya yayinda naga wacce tafi kowacce haske, saina naga bakowa bace nike ganiba sai ke masoyiyata! So gamon jinine, haqiqa sonki ya zamo jinin jikina!


Ki kwantar da hankalinki masoyiyata babu

wata a zuciyata sai ke kadai!


Congrats to me, saboda na Samu Mafi kyawu, Kulawa da Yarinyar da take Saurin Fahimta ta, kuma kece, my love


Yarda da amincewarki gareni, sune zasu

tabbatar da soyayyarki ta gaskiya a gareni!


Yau nayi mafarki, Kin kawo mini ruwa mai sanyi tare da wani a hannun ki, wannan abun kuwa shine soyayya ta dana baki, ki riƙe shi kada ki sake.


Farin ciki baya dorewa a rayuwa sai tare da bakin ciki, dan haka kowane hali nike bazan taba mantawa dake ba masoyiyata!


Da Farko Ina Miki Sallama Irin Wacce Na Saba Miki a Kullum, Sannan Ina Miki fatan Alkhairi irin wanda na saba a kullum, kin tashi lafiya, Ya zuciyar ki take? Ta kasance lafiya, ko ta kasance kullum cikin tinani na? Ba sai kin bani amsa ba, bugun zuciyarki zai sanar dani.


Nakan raba dare ina mai roqon Allah don

neman biyan buqata, ko kinsan kece abu na farko da nike roqo samu!


Gari ya waye, hasken rana ya fito, nima kuma na fito domin cigaba da noma gonar soyayyarki dana saba a Kullum, ina fatan irin dake Zuciyar ki ya kasance dai dai da irin wanda nake shukawa, Domin samun yabanya mai albarka tsakani na dake, Soyayyar ki tasa ni yin hudar da ba tare da garma ba.


Yanayin sanyi kan sa mutum ya takura, tare da lullu6a da qaton mayafi amma ni duk sanyin da ake idan na tunaki sai naji tamkar yanayin zafi! Kamar yadda kowacce bishiya kanyi rassa a sama, kuma tayi saiwa a qasa, haka sonki ya mamaye dukkan jikina, idan na kalleki sai nayi farin ciki, idan naji tattausan muryarki, sai nishadi da walwala tare da annashuwa gami da farin ciki su mamaye zuciyata!


Da akwai wasu tarin tsintsaye da suke wuni suna tattauna batutuwa a kan irin matsayin da na baki a cikin zuciya ta. Zan so ki ji irin abun da suke cewa, domin kuwa a lokacin ne za ki tabbatar da irin son da nake yi miki. Ina Son Ki! 


Kamar yadda kowacce bishiya kanyi rassa a sama, kuma tayi saiwa a qasa, haka sonki ya mamaye dukkan jikina, idan na kalleki sai nayi farin ciki, idan naji tattausan muryarki, sai nishadi da walwala tare da annashuwa gami da farin ciki su mamaye zuciyata!


SO shi ne abun da ya dun’kule zuciyoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba za ki bari wani d’an ‘karamin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? Ina son ki. Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Ki Huta Lafiya.


Akan ki zan iya komai banda Mutuwa, domin ina Son na kasance dake har abada, Nayi rayuwa dake mai kyau mai tsafta, Ina Miki barka da safiya Tare da fatan Zaki Wuni lafiya tare da farin ciki, Ki sani Ina Tare dake kuma Ina Qaunarki.


Ina neman wata kalma wadda babu wanda ya santa. Ina neman wata kalma da zan furta miki cewa…..ke ta daban ce, ke kyakkyawa ce, kin zarce sauran mata. Zuciya ta da taki ba za su ta6a rabuwa ba har abada. Ina son ki


Abun da na ke ji a dangane da ke gaskiya ne kema na san kin san da haka cewa ina son ki, a duk lokacin da kika bar ni ba zan iya motsawa ko da nan da can ba, wannan shi ne abun da zai faru da ni a duk lokacin da na rasa ki.


1 Response to "Kalaman Soyayya 2022/2023"