-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Menene TikTok

Menene TikTok

 Ma'anar TikTok A YauJawabin BBChausa Game Da Ma'anar TikTok

TikTok: Yadda shafin sada zumuntar ya zama matattarar samari da ƴan matan arewa

Shafin sada zumunta na Tik Tok ya samu karɓuwa sosai a wurin samari da ƴanmata a arewacin Najeriya. Kusan a iya cewa ma yana daga cikin shafukan sada zumunta da ke samun ƙaruwar masu amfani da shi.

Babu mamaki a lokacin da kuke shawagi a shafin Instagram ko Twitter, kun ci karo da wani bidiyo mai ɗauke da alamar TikTok da wata budurwa ko saurayi suna ta bin waƙar Hausa ko ma ta turanci. Babu mamaki ba ku taɓa ganin budurwar ko saurayin ba, amma kun ga sun burge ku musamman yadda bidiyon ba shi da tsawo — ɗan gajere ne amma ya ƙayatar.

Wataƙil ma wannan ne ya sa ku ma kuka sauke manhajar TikTok a wayoyinku don ganin wainar da ake toyawa a wannan shafi mai miliyoyin bidiyo.

Mafi yawa masu amfani da shafin TikTok matasa ne masu neman nishaɗi — wato ku su nishaɗantar ko su nishaɗantu. Shi ya sa ma kusan duka bidiyon da ke wannan shafi yana ɗauke da waƙa ko rawa ko kwaikwayo ko kuma duka.

To matasa a arewacin Najeriya ma dai ba a barsu a baya ba wajen amfani da shafin TikTok

A shafin TikTok akwai maudu'i daban daban kamar yadda yake a shafin Twitter da Instagram.

Wannan na nuna rarrabuwa ko salo na bidyon, wato akwai maudu'i wato hashtag kamar #Hausa da #Hausavideo da #comedy #viral da dai sauransu ba kamar Twitter ba da maudu'i ke nuna wani taƙamaimai labari.

Don haka idan kuka shiga TikTok kuma kuna neman bidiyo da aka yi da Hausa, kuna iya amfani da #Hausavideo ko #Hausa wajen gano dubban bidiyo a harshen Hausa.

Karɓuwar da bidiyon TikTok suka samu ya sa duk shafin sada zumunta da ka shiga, za ka gansu. Kuma da yake shafin na ba da damar adana bidiyo cikin hanya mai sauƙi, masu amfani da shafin ba sa ɓata lokaci wajen 'saving' da aika waɗannan bidiyo.

Haka kuma, yin bidiyo a TikTok na da matuƙar sauƙi, bugu da ƙari ga ɗaruruwan waƙoki da fina-finai da 'filter' iri iri wanda mai amfani da shafin zai iya zaɓa don ƙarawa bidiyonsa armashi. Ma'ana, ana iya haɗa bidiyo nan take a cikin shafin ba tare da wani ɓata lokaci ko neman wata manhaja da za ta haɗa bidiyon ba

A shafin TikTok akwai abin da ake kira 'challenge' wanda ya zama kamar bai wa masu amfani da shafin wani ƙalubale ne.


Wato a kan ƙirkiro salon yin wani abu kamar waƙa ko rawa ko salon magana ko wasa da dai sauransu, sannan a ƙirkiri # da ke nuna ana ƙalubalantar masu amfani da shafin su ma su yi irinsa kuma su ɗora a shafinsu.

Wannan yana matuƙar ƙara tunzura samari da ƴanmata wajen wallafa bidiyo kala kala duk da cewa dai ba kyauta ake bai wa wanda ya shiga gasar ba amma ya kan samu 'likes' da ƙarin 'followers' kuma hakan zai ƙara masa suna a shafin.

Misali akwai #slowmotionchallenge da #slowmochallenge da #slowmowalk wanda ke ƙalubalantar masu amfani da TikTok su yi wani salon rawa inda za su yi sauri sauri sannan su yi sannu sannu.

Kuma za su dora duk waƙar da suka ga dama a kan bidiyon.

An yi amfani da wannan maudu'i a shafin fiye da sau miliyan 3 a faɗin duniya.

Kwalliya na taka muhimmiyar rawa a amfani da TikTok.

Sau da yawa za budurwa ta caɓa ado kamar za ta biki, amma bidiyo kawai za ta ɗauka a TikTok musamman a wannan zamanin na kwalliyar fankeke da janbaki da zana gira.

Za ta kafa ɗaurin dankwali nan da ake yayi na 'Zahra Buhari' mai zuwa har goshi, sannan sai ta tabbatar dinkinta na gani na faɗe ne.

Su ma samarin ba a barsu a baya ba, don kuwa sai sun tabbata sun sanya ɗinkuna ko dai wata sutura ta zamani da ake yayi sannan su nadi bidiyon.

Ma'ana dai sai an dau wanka ake hawa TikTok

Bugu da ƙari, ya zamar wa wasu sana'a, don kuwa a cikin masu amfani da shafin akwai waɗanda su ke da dubban mabiya, wato followers kuma bidiyoyinsu na samun masu kallo da yawa.

Waɗannan su ake kira 'influencers' wato masu faɗa a ji a wannan shafi.

Kamfanoni kan biya su kuɗi don su yi masu tallar hajarsu ganin cewa suna da mabiya da yawa, kuma kamfanonin kan ba su abun da suke samarwa kyauta.

Misali, kamfanin samar da kayan kwalliya kan bai wa wata kwangilar tallata janbakin da kamfanin ke samarwa ta hanyar yin bidiyo da zai nuna wa mabiyanta yadda janbakin ke da inganci.

Masana harkokin kimiyya sun ce matasan yanzu sun fi son samun bayanai, wala Alla na ƙarin ilimi ne ko na nishaɗi, ta hanyar bidiyo.

Babu mamaki shi ya sa TikTok ya samu karɓuwa sosai a wurin matasan.

Sannan yadda bidiyoyin suke a jejjere, da an gama kallon wannan sai a faɗa wani ba tare da tsaiko ba, ya taimaka wajen samun karɓuwarsa.

Ana iya cewa TikTok ya zame wa matasa wani keɓeɓɓen wurin baje kolinsu ba tare da tsawatarwar 'manya' ba.

Wuri ne da suke cin karensu babu babbaka, kuma suka aminta da shi don ɗebe kewa da haɗuwa da sa'o'insu waɗanda ke da mahanga guda.


Menene TikTok?

TikTok ya samo asali ne daga kasar Sin, mallakar wani kamfani na kasar Sin da ake kira Bytedance (wanda aka dauki daya daga cikin mafi yawan farawa nasara a duniya). Ya fara zama sananne ne a ƙarƙashin sunan Musical.ly kafin su yi maimaitawar ban mamaki. Hakan yasa wasu mutane har yanzu suka rikita biyun.

A takaice, TikTok yana game da ƙirƙirar gajeren bidiyon 15-na biyu waɗanda kida ke raɗawa (komai daga waƙoƙi daga shahararrun masu fasaha zuwa ƙananan shirye-shiryen bidiyo daga fina-finai da kuma nuna talabijin).

Abin mamaki, shi ke nan. Mutane suna kirkirar waɗancan bidiyon kuma suna raba su akan TikTok. Tabbas, Hakanan zaka iya ƙara matattara daban-daban, yin wasu zane mai ban sha'awa, kuma ka sami fasaha da gaske. Amma da gaske duk yana girgiza zuwa yadda sauƙi ne a fara amfani da TikTok.

A lokaci guda, tare da duk saukinta, app ɗin zai iya zama kamar ma yana da rikitarwa. Yana da babban hadadden abubuwan abubuwan wasu ayyukan kamar Vine, Snapchat, da Spotify - duk an cakuɗe su cikin ƙawance guda.

0 Response to "Menene TikTok"

Post a Comment