LABARI MAI DADINJI:Yan Kasuwa Suna Ta Karyar Da Farashin Buhun Siminti
LABARI MAI DADINJI:Yan Kasuwa Suna Ta Karyar Da Farashin Buhun Siminti.
Bayan biyo wata sanarwa daga kamfanonin fitattun Yan Kasuwa biyu a Najeriya, Aliku Dangota, Abdulsamad isiyaka rabiu Mai BUA, dangane da sauko da farashi ga Yan Kasuwa masu sari daga kamfani, kan kowani buhu 1 naira dubu 2000, sai kuma Dan kasuwa ya ji da Kudin dakon kayansa.
Biyo bayan hakanne, ake sanar damu ce wa, e zuwa halin yanzu wasu Yan Kasuwa a fadin Najeriya, sunata karya farashi, kama daga sauran simintin da yayi raguwa a wuraren kasuwancin na su, ana iya samun kowami buhu 1 a kan naira dubu 4400, zuwa da 4200 sabanin a baya akan kowani buhu Naira dubu 5000, 4800.
Hakan ya kara bude wata sabon faifai ne, kafin su Yan kasuwan su garzaya domin siyo sabon simintin da ke dauke da farashin kamfani a kan kowani buhu 2000 daga kamfani.
Shin ya Yan kasuwar garinku suke sayar da buhun siminti akan kowani buhu 1...
Daga Barrista Nuraddeen Ismaeel
0 Response to "LABARI MAI DADINJI:Yan Kasuwa Suna Ta Karyar Da Farashin Buhun Siminti"
Post a Comment