Anga Messi yana rawa a wurin wani shagali
Anga Messi yana rawa a wurin wani shagali
Lionel Messi ya kamu da cutar Covid-19, kamar yadda Paris Saint-Germain ta sanar, kwanaki kadan bayan da aka ga fitaccen dan wasan yana rawa a wani shagali a Argentina. Haskenews rahoto.
Dan wasan mai shekaru 34, ya yi amfani da hutun hunturu na wasan kwallon kafa na Faransa tare da matarsa, Antonela, kuma an dauki hoton bidiyon yana jin dadin kansa a wani shagali a kasarsa.
Wani bidiyo a Tiktok ya nuna Messi da matarsa suna nishadi a wani shagali a Rosario, Sante Fe.
Yanzu, babbar kungiyar Faransa ta tabbatar da cewa ya kamu da kwayar cutar kuma ya ware kansa. Uku daga cikin abokan wasan Messi kuma suma sun kamu, ciki har da Sergio Rico, Juan Bernat da Nathan Bitumazala .
Tauraron dan wasan na Paris Saint-Germain ya buga wasan karshe a wasan da suka tashi 1-1 da FC Lorient a ranar 22 ga watan Disamba kafin a tashi daga gasar Ligue 1 a lokacin bukukuwa kirsimeti.
Wasan kungiyar na gaba shine da Vannes a gasar cin kofin Faransa yau litinin, kafin su kara da Lyon a gasar ligue 1 a ranar 9 ga watan Janairu.
Tun daga ranar Litinin, gwamnatin Faransa za ta bullo da sabbin ka’idojin keɓancewa waɗanda ke nuna cewa mutanen da suka kamu da cutar kuma aka yi musu allurar dole ne su ware na kwanaki bakwai kawai, maimakon 10.
0 Response to "Anga Messi yana rawa a wurin wani shagali"
Post a Comment