-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

N-Power: Za mu ƙara ɗiban matasa dubu 400 – Sadiya Umar Faruk

N-Power: Za mu ƙara ɗiban matasa dubu 400 – Sadiya Umar Faruk

N-Power: Za mu ƙara ɗiban matasa dubu 400 – Sadiya Umar Faruk

Ministar harakokin Jinƙai da ci gaban Rayuwa ta ƙasa, Sadiya Umar Faruk ta sanar da cewa gwamnatin tarayya na shirin sake ɗaukar matasa dubu 400 a shirin N-Power.

Ministar ta yi sanarwar ne a Kano a juya Laraba a gurin yaye ƴan rukunin C1 na N-Knowledge a jihar Kano.

Ta ƙara da cewa adadin wani ɓangare ne na matasa miliyan ɗaya da shugaban ƙasa ya sahale a ɗauka.

Ta ce matasa dubu 510 ne su ka amfana da shirin a rukunin C 1, inda ta ƙara da cewa nan ba da daɗewa ba za a fara rukunin C 2.

Sadiya ta yi bayani cewa shi shirin na N-Knowledge zai taimakawa matasa ne wajen gogar da su kan harkar aikin ofis, ƙirƙire-ƙirƙire da kuma harkokin kasuwanci a gida Nijeriya da ma ƙasashen waje.

Ministar, wacce ta samu wakilcin Mataimakin Darakta a ma’aikatar, Muhammad Sambo, ta ce matasa dubu uku ne da ga yankin arewa-Maso-Yamma su ka samu horo kan na’ura mai ƙwaƙwalwa a rukunin na C1.

Ta kuma yi kira ga matasan da su ka amfana da su yi ƙoƙari su yi aiki da horon da su ka samu domin bunƙasa tattalin arzikin su a rayuwa.

Source: opportunitieshub


Allah ka ciyarda mu Alherinsa

0 Response to "N-Power: Za mu ƙara ɗiban matasa dubu 400 – Sadiya Umar Faruk"

Post a Comment