Rancen Household N500,000.00: Kar Mu Gaji Yan Arewa Har Yanzu Ana Cike Rancen Covid-19 Na Nirsal Microfinance Bank
Rancen Household N500,000.00: Kar Mu Gaji Yan Arewa Har Yanzu Ana Cike Rancen Covid-19 Na Nirsal Microfinance Bank
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bullo da tallafin gaggawa na kudi ga kananan 'yan kasuwa, kanana da matsakaitan masana'antu sakamakon mawuyacin halin da su ka samu kansu bayan bullar cutar korona a kasar nan.
Kudin wanda za a bayar da shi ta hanun wani bankin al'umma mai suna "Nirsal Microfinance Bank" mallakin Babban bakin Najeriya wato CBN, zai taimaka wa 'yan kasuwa da kananan masana'antun da suka durkushe ko kuma jarinsu ya yi kasa sosai.
Yawan kudin da babban bankin Najeriya ya ware don wannan tallafi ya kai Naira miliyan dubu hamsin(N50b).
Tuni dai 'yan abokan zaman a wannan kasa dake kudancin Najeriya su ka yi wannan yanki namu na Arewa fintinkau a wannan fanni, kuma da yawa daga cikinmu ba su san yadda za su samu wannan rancen kudi ba.
Saboda haka Haskenews.com.ng ta wallafa wanan kasida musamman ga ma su sha'awa.
Za ka/ki iya neman wannnan tallafi da wayar hanunki matukar ka/ki na iya hawa yanar gizo da ita.
Da farko za ku sanya wannan adireshin yanar gizo domin isa ga shafin da za ku cike wato:
Shafin cike Household loan: https://nibloans.nmfb.com.ng/noninterestlendingtcfhousehold
Shafin Dubawa Idan Anyi Nasara: https://covid19.nmfb.com.ng
Idan ya kai ka/ki shafin, za ku ga inda aka rubuta "HOUSEHOLD" a kasansa kuma an rubuta "APPLY" to kan APPLY za ku dannna don ku sami "form" da ku shigar dukkanin bayanan da aka nema a wajenku.
Bayanan da ake nema sun hada da sunanku, adireshin email, lambar BVN, kalar kasuwanci da ku ke, wajen da kasuwancin yake yawan kudin da ku ke bukata, da sauransu.
Bayan kun kammala sai ku tura, ku jira sakon da za su aiko mu ta hanyar sakon kar ta kwanan daga nan ne za su bukaci lambar asusun ajiyarku na banki da sunan bankin, inda za su turo mu ku kudin da ku ka samu.
0 Response to "Rancen Household N500,000.00: Kar Mu Gaji Yan Arewa Har Yanzu Ana Cike Rancen Covid-19 Na Nirsal Microfinance Bank"
Post a Comment