-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Mun Rabawa Matasan Najeriya 7,057 Tallafin N3bn A Shirin NYIF, Cewar Babban bankin Kasa (CBN)

Mun Rabawa Matasan Najeriya 7,057 Tallafin N3bn A Shirin NYIF, Cewar Babban bankin Kasa (CBN)

Mun Rabawa Matasan Najeriya 7,057 Tallafin N3bn A Shirin NYIF, Cewar Babban bankin Kasa (CBN)

  • Hukumar kididdigan Najeriya ta bayyana cewa adadin mazauna Najeriya matasa ne masu shekaru 15 zuwa 34 kimanin milyan 100 ne
  • Daga cikin wannan adadi, hukumar Lissafi da bincike NBS ta ce kawo karshen 2020, kashi 38.5% na matasa basu da aikin yi
  • Saboda haka gwamnatin tarayya ta samar da tallafin matasa (NYIF) karkashin Ma'aikatar matasa da wasanni
  • Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN), yace a shirin da yake yi tare da ma'aikatar matasa da wasanni, kawo yanzu an rabawa matasan Najeriya 7,057 kudi N3bn.

An yiwa shirin take 'Asusun lamunin matasan Najeriya' (NYIF).

Wannan na kunshe cikin rahoton da CBN ya wallafa a shafinsa ranar Litinin, 11 ga Okotba, 2021.

A cewar rahoton, wadanda suka amfana da wannan kudi sun hada da daidaikun mutane 4,411, da kuma masu kananan sana'o'i 2,646.


Menene tallafin NYIF?

Bankin CBN ya fara shin NYIF ne a yunkurin da takeyi na baiwa matasa yan kasuwa tallafi domin samar da aikin yi wanda zai rage zaman kashe wando tsakanin matasa.

Rahoton ya kara da cewa NYIF na neman matasa masu shekaru tsakanin 18 da 35 don basu jarin kasuwanci.

Yace:

"Muna neman matasa masu ayyukan hannu da kananan kasuwanni wadanda zasu zama masu gidan kansu kuma su samar da ayyuka akalla 500,000 tsakanin 2020 da 2023."

 Source: Mujallar Labarai Ta Legit

2 Responses to "Mun Rabawa Matasan Najeriya 7,057 Tallafin N3bn A Shirin NYIF, Cewar Babban bankin Kasa (CBN)"

  1. babayusufoliya987@gmail.com niharyanzo babansamu wannan tallafiba nacice Amma haryanzo hirune

    ReplyDelete
  2. babayusufoliya987@gmail.com haryanzu hiru balabari tunda nacike

    ReplyDelete