Tallafin COVID-19 (Non- Interest) idan aka turo maka wannan sakon to kana cikin wadanda za’a bawa kaya na rance marar kuɗin ruwa
Tallafin COVID-19 (Non- Interest) idan aka turo maka wannan sakon to kana cikin wadanda za’a bawa kaya na rance marar kuɗin ruwa
Ƙungiyar Marubutan Arewa A Kafofin Sadarwar Zamani “Arewa Media Writers” Tana Kira Ga Al’ummar Arewacin Najeriya Dasu Hanzarta Wajen Cike Sabon Tsarin Bada Ranche Da Gwamnatin Tarayya Ta Fitar COVID-19 (Non- Interest)
Ƙungiyar Marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani “Arewa Media Writers” ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar na ƙasa Comr Abba Sani Pantami, tana kira ga al’ummar Arewa da su hanzarta wajen cike sabon tsarin bada ranche da gwamnatin Tarayya ta fitar.
Idan bamu manta ba a kwanakin baya gwamnatin Tarayya ta fitar da sabon tsarin bada ranche a ranar 27/8/2021, wadda a yanzu haka wadda suka nemi bada ranchen a cikin satin da aka bude har sun samu sakon amincewa da bayanan su wato “Approved”.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa zata cire matasa da marasa aikin yi mutum miliyan 8 daga ƙangin Talauci, wadda hakan yasa aka buɗe wa ‘yan AREWA wannan Portal ɗin.
Tunda gwamnatin Tarayya take buɗe portal na Bada tallafi ko bashi Bata taɓa fitar da Portal mai saurin tafiya da Kuma saurin amincewa da bayannan mutum ba kamar na wannan karon.
A cikin Jahohi 36, da muke dasu babu wadda suke amfana da wannan bashin kamar a’ummar mu na Arewa, Idan muka duba jihar Kano a cikin makon da aka fara cikewa sun samu mutum 500 wadda aka musu Approval, a sati na biyu kuma sai da suka samu mutum 1000, wadda aka yiwa Approval.
Yanzu idan ka buɗe portal din ka saka BVN Naka muddin baka fito daga cikin jihohi 20, da muke dasu na Arewa ba to bazai taɓa wucewa ba, sai dai ya nuna maka fari ko kuma yaƙi shigewa saboda anyi abinne domin ‘yan Arewa su amfana ganin yadda aka barsu a baya.
A wancan lokacin da aka fitar da Portal na COVID-19 idan aka amince da bayanan ka wato aka Maka “Approve” to za kaje ne kasa ka BVN number naka zasu nuna Maka bayanan ka da Kuma adadin kuɗin da zasu baka, daga nan Kuma sai ka saka lambar asusun ka sai su saka maka Kuɗin ka a ciki.
Amma wannan karon ba haka tsarin yake ba, wannan karon idan suka maka Approve su da kansu zasu haɗa ka da wakilin su wato “Vendor” duk abinda ka cika shi zai saya maka, misali idan ka cika musu kana sai da waya ko Kwamfuta to idan sun maka Approved zasu haɗa ka ne da shi “Vendors” domin kuje kasuwa ya saya maka sai ya baka abinka.
Mene ne vendor Kuma Mene ne Aikin Shin?
Aikin sa shine ya ɗauki wadda aka yiwa Approval zuwa kasuwa domin ya saya masa abinda ya cike a lokacin da yake neman bashin sai ya bashi abinsa a hannun sa.
An fitar da wannan tsarin ne duba da yadda wasu suka samu irin Wannan bashi amma basa abinda ya dace da kuɗaɗen hakan yasa suka sanya Vendor a tsakiya domin tabbatar da anyi abinda ya kamata da kuɗin.
Shi vendors shine zai tabbatar da cewa abinda ka cika ya saya ya baka shi a kasuwa daganan kuma saiya baka a hannun ka sai kasa hannun wato shedar ka karɓi kayan ka da hannun ka shi Kuma saiya mayar musu da shedar ya saya maka kaya kuma ya baka a hannun ka.
Wadda bai cike sabon tallafin marar kuɗin ruwa na NIRSAL Microfinance Bank ba zai iya cikewa ta wannan Adireshin ɗin yanar gizo
Idan kashiga zai baka zaɓi guda biyu kamar haka “Household da Kuma SMEs”
Idan kana da kamfani Kuma kayi rajista da CAC to zaka cike SMEs idan Kuma baka dashi sai ka cike household, duk wadda zai cike ya tabbatar daya kwafe TCF Nombansa saboda gudun matsala.
0 Response to "Tallafin COVID-19 (Non- Interest) idan aka turo maka wannan sakon to kana cikin wadanda za’a bawa kaya na rance marar kuɗin ruwa"
Post a Comment