Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke ministoci biyu na ma'aikatun Noma Sabo Nanono da kuma na Lantarki Sale Mamman
Wednesday, September 1, 2021
Comment
Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke ministoci biyu na ma'aikatun Noma Sabo Nanono da kuma na Lantarki Sale Mamman.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin shugaban Najeriya, Femi Adesina ya fitar a wannan Larabar.
Sanarwar ta ce Ministan Muhalli, Mohammed Abubakar ne zai maye gurbin Ministan Noma, yayinda karamin Ministan ayyuka, Abubakar Aliyu zai maye gurbin Ministan Lantarki.
Matakin wani ɓangare ne na sauye-sauyen da shugaba Buhari ke aiwatarwa, a cewar Femi Adesina.
Source BBChausa
0 Response to "Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke ministoci biyu na ma'aikatun Noma Sabo Nanono da kuma na Lantarki Sale Mamman"
Post a Comment