-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Tarihin Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya

Tarihin Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya

 Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya

Aisha Aliyu Tsamiya (an haife ta a 1992) a ƙaramar hukumar Nasarawa ta jihar Kano a Arewacin Nijeriya. A halin yanzu tana karatu ne a Jami'ar Yusuf Maitama Sule dake a jihar Kano

Aisha Aliyu, wata matashiyar ƴar fim da take da burin zama babba a harkar fim. An haifeta a ƙaramar hukumar Nasarawa ta Kano. Ta tafi makarantar firamare da sakandare ta Giginyu kuma a halin yanzu tana neman karatun ta mai zurfi.

Ta fara aiki ne a matsayin mai daukar nauyin fim ɗin ta da kantq saboda sha'awar fina-finai don isar da sako ga al'umarta, saƙonni kan canjin zamantakewa. Fim dinta na farko shi ne Tsamiya daga nan sai wani fim mai suna Rabi’a, Rayuwa Bayan Mutuwa, Uzuri da Dakin Amarya. Hakika Aisha Tsamiya ta nuna wa duniya ita ba kanwar lasa ba ce, domin har yanzu tana ci gaba da bayyanar da zalaka da kwarewarta a fagen finafinan Hausa. Tsamiya ta zama daya daga cikin fitattun ƴan fim goma a cikin jaruman Kannywood a shekarar 2016. Hakanan Kuma Tsamiya na da masoya ba mabiya masu ɗimbin yawa a shafukan sada zumunta na yanar gizo

Wasu daga cikin fina-finan da Aisha Aliyu Tsamiya tayi sun hada da:- Tsamiya

Ranar Baiko, Hanyar Kano, Bahaushiya, Da Kishiyar Gida, Dakin Amarya, Husna, Jamila, Mai Dalilin Aure (Match Maker), Makahon Gida, Munubiya, Niqab, Nisan Kiwo, Rayuwa Bayan, Mutuwa, Zeenat, Kalan dangi, Aisha Aliyu(tsamiya)

Aisha aliyu tsamiya matasiyar yar film ce data nuna fata da sha'awar shiga masana'antar da shirya fina finan hausa.

An haifi Aisha tsamiya a shekarata 1992 a karamar hukumar nasarawa ta jihar kano, ta tafi makarantar firamare ta Giginyu sannan ta halarci makarantar sakandire.

Ta fara aiki ne saboda sha'awar da takeyiwa sana'ar shirya fina finan hausa a cewar ta domin isar da sako ga al'umma. Film din tsamiya shine film din data fara suna a cikin shi, sannan ta fito a film din Rayuwa bayan mutuwa, Uzuri, Dakin amarya, kalan dangi da dai sauran su.

Aisha tsamiya ta zama matsayi na goma a shahararren film din salma, hakika har yanzun Aisha tsamiya tana daga cikin matan da tauraruwar su ta dade tana haskawa a masana'antar shirya film na hausa, kuma ta kware sosai a wannan sana'ar ta shirya fina finan hausa.

A halin yanzu dai Aisha tsamiya tana cigaba da neman ilimi a arewa. Aisha tsamiya har yanzun dai batayi aure ba amman tana kiyaye sunanta da duk mutuncinta, sannan tana da gurin kammala makaranra kafin tayi aure.

Wasu daga cikin Kyawawan hotunan Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya

0 Response to "Tarihin Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya"

Post a Comment