eNaira Digital kwaransi: Mene ne eNaira?, Menene Amfanonin eNaira?, Mene ne eNaira Wallet?, A Ina Ake Adana Kuɗin eNaira?, A Ina Zan Samu Mahajar eNaira Wallet? - Duba Amsa Anan
eNaira Digital kwaransi: Mene ne eNaira?, Menene Amfanonin eNaira?, Mene ne eNaira Wallet?, A Ina Ake Adana Kuɗin eNaira?, A Ina Zan Samu Mahajar eNaira Wallet? - Duba Amsa Anan
Mene ne eNaira?
eNaira shine kudin dijital wani tsarine wanda Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta samar karkashin tsarin babban bankin Najeriya (CBN). Za a yi amfani da shi gefe ɗaya tare da tsohon tsarin "FIAT" (kira shi da, takardar kuɗi na al'ada/zahiri) kuma ana tsammanin wannan tsarin zai yi fice wajan wakiltar Naira ta takardar a kasar Najeriya dama fadin duniya. Shi dai wannan tsarin na e-Naira Digital kwaransi an samardashi ne domin farfadowa da martabar naira inda ake tsammanin hakan zai bawa kasar damar saukaka hada-hada da kuma cinikin Kasuwanci a fadin kasar dama duniya baki daya idan aka kwatantashi da biyan kuɗi zahiri.
A Ina Ake Adana Kuɗin eNaira ?
Ana adana kuɗin eNaira acikin mahajarda ake kira "eNaira Wallet" Wato asusun ingizon yanar gizon eNaira.
Mene ne eNaira Wallet?
eNaira Wallet shine aikace -aikacen ajiya na dijital na dijital wanda Babban Bankin Najeriya ya bayar don riƙe sabon kuɗin dijital, eNaira.
A Ina Zan Samu Mahajar eNaira Wallet?
Zaka iya samun Mahajar eNaira Wallet a rumbun mahajoji ta Google ko ka garzaya kai tsaye zuwa shafin eNaira na yanar gizo kamar haka: https://enaira.com/
- Masu amfani da Mahajar Android kushi Play Store
- Masu amfani da Mahajar iPhone kushi Apple Store
- Masu amfani da Mahaja ta daban zaku iya amfani da tsarin lambobi da ake kira USSD CODE
Menene Amfanonin eNaira?
- Ana amfani da kuɗin eNaira wajan yin hada-hadar Kasuwanci na gida dama fadin duniya.
- Tsarin eNaira zai samar da ayyukan yi ga matasa domin dogaro da kanzu.
- eNaira zai saukaka wahalhalu da tsaiko da ake fama dasu a bankuna, hada-hada, da kuma cushewar sabis.
- Domin Tuntuba ko war-ware matsaloli zaku iya aikawa da sako ta shafin sakon imel kamar haka: helpdesk@enaira.com
Muna godiya sosai
ReplyDelete