-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Cristiano Ronaldo ya karya Dadadden tarihin Ali Daei na duniya

Cristiano Ronaldo ya karya Dadadden tarihin Ali Daei na duniya

Cristiano Ronaldo ya karya Dadadden tarihin Ali Daei na duniya

Cristiano Ronaldo ya karya tarihin da Ali Daei da ya kafa na tsahon shekaru 15 a duniya bayan ya ci wa Portugal kwallon sa ta 110. Fagenwasanni.com ta rahoto.

Dan wasan mai shekaru 36 ya yi daidai da tarihin Daei a gasar cin kofin Turai a wannan bazarar kuma ya ci kwallaye biyu a ragar Jamhuriyar Ireland a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya a daren Laraba.

Bayan dawowar sa Manchester United, dan wasan ya shiga filin wasan Estadio Algarve da karfi sosai.

Ronaldo, ya ci takalmin zinare daga gasar cin kofin Turai tare da kwallaye shida,

Daei ya ci wa Iran kwallaye 109 tsakanin 1993 zuwa 2006.

Kwallon farko da Ronaldo ya ci a kasa ita ce kwallon da yaci a gasar Euro 2004 akan kasar Girka, kafin ya ci kwallon farko a wasan kusa da na karshe da Netherlands.

0 Response to "Cristiano Ronaldo ya karya Dadadden tarihin Ali Daei na duniya"

Post a Comment