-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

'Yan Arewa Mu Farka: Gwamnatin Shugaba Buhari Za Ta Sake Raba Tallafin Bashi Marar Kuɗin Ruwa

'Yan Arewa Mu Farka: Gwamnatin Shugaba Buhari Za Ta Sake Raba Tallafin Bashi Marar Kuɗin Ruwa

'Yan Arewa Mu Farka: Gwamnatin Shugaba Buhari Za Ta Sake Raba Tallafin Bashi Marar Kuɗin Ruwa.

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari (GCFR), ta hannun ƙaramin bankin harkokin kasuwanci, (NIRSAL), ƙarƙashin babban bankin ƙasa (CBN), za ta sake rabawa ƴan Nageriya tallafin bashi wanda babu kuɗin ruwa a ciki.

Duk mai sha'awar bashin zai iya ziyartar wannan adireshi na: www.nmfb.com.ng domin ya cike buƙatarsa ta neman tallafin bashin.

Sharaɗi ne ga duk masu kamfanoni da za su nemi wannan bashi sai su na da takardun harkokin kasuwanci da kuma bayanai akan yadda annobar (Covid-19) ta shafi harkokinsu. Sannan kuma masu kasuwanci na kai a gida za su iya nema ba tare da wannan sharaɗin ba.

Adadin kuɗin da kowane mai kamfani zai iya neman rancen shi ne Naira Miliyan 2,500,000, masu kasuwanci a gida kuma Naira 1,000,000.

Duk mai sha'awa zai iya cikewa ta wannan adireshi na: www.nmfb.com.ng, ko ya tuntuɓe su a lambar wayarsu: 09010026900

Nirsal Microfinance Bank 

Allah Ya ba da sa'a da rabo mai amfani.



0 Response to "'Yan Arewa Mu Farka: Gwamnatin Shugaba Buhari Za Ta Sake Raba Tallafin Bashi Marar Kuɗin Ruwa"

Post a Comment