'Yan Arewa Kar Mu Gaji, Mudaure Mu Cike Wannan Sabon Tsarin Rance Marar Kuɗin ruwa na NIRSAL
'Yan Arewa Kar Mu Gaji, Mudaure Mu Cike Wannan Sabon Tsarin Rance Marar Kuɗin ruwa na NIRSAL
'Yan arewa mu farka da daga barci kamar yadda mukaji Sanarwar ana ci gaba da cike tallafin Marar Kuɗin ruwa na NIRSAL Micro Finance Bank, to mu sani cewa wannan tallafin gaskiya ne. Kuma ina kira ga wayanda suke cewa bazasu cike ba sabida sun cika tsarin har sau uku 3 basu samuba da su kara hakuri su cike wannan Sabon Tsarin Rance Marar Kuɗin ruwa na NIRSAL.
Mu tashi mu nemi bayanai akan yadda zamu karɓi tallafin babban bankin Nigeria CBN na bashi mara kuɗin ruwa wanda aka fitar da tsarin domin musulmai su ci gajiyar tallafin suma, wanda tuni bankin Nirsal suka yi nisa akan fara shirin domin baiwa mutane, dama ce ta zo mana kuma ya kamata mu yi amfani da ita wajan nema da cike duk wasu sharuɗa wanda bankin suke so mutum ya basu domin bashi wannan bashi ko nace aro.
Sharaɗi ga duk masu kamfanoni da za su nemi wannan bashi sai su na da takardun harkokin kasuwanci da kuma bayanai akan yadda annobar (Covid-19) ta shafi harkokinsu. Sannan kuma masu kasuwanci na kai a gida za su iya nema ba tare da wannan sharaɗin ba.
Shi dai wannan tallafin ya kasu kashi uku 3
Kashi na farko 1: NON- INTEREST AGSMEIS : http://nibloans.nmfb.com.ng/agsmeisnoninterestlending
Kashi na Biyu 2: NON- INTEREST TCF (HOUSEHOLD) : http://nibloans.nmfb.com.ng/noninterestlendingtcfhousehold
Kashi na Uku 3: NON- INTEREST TCF (SME): http://nibloans.nmfb.com.ng/noninterestlendingtcfsme
Idan kunaso shafin yanar gizon yabude dasauri kuyi amfani da wayannan mahajojin Burauzin
Browser ta i. Phoenix Browser
Browser ta ii. Edge Browser
Browser ta iii. Windows Explorer
Browser ta iv. Chrome
Adadin kuɗin da kowane mai kamfani zai iya neman rancen shi ne Naira Miliyan 2,500,000, masu kasuwanci a gida kuma Naira 1,000,000.
Duk mai sha'awa zai iya cikewa ta wannan adireshi na: www.nmfb.com.ng, ko ya tuntuɓe su a lambar wayarsu: 09010026900
Nacika tallfin non interest tcf, House hold ammasunce sainacika reference number
ReplyDelete