-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Karin Bayani Akan Sabon Tsarin Rance Marar Kuɗin Ruwa Da Babban Bankin Nigeria CBN  Ta Fitar Ayau

Karin Bayani Akan Sabon Tsarin Rance Marar Kuɗin Ruwa Da Babban Bankin Nigeria CBN Ta Fitar Ayau

Karin Bayani Akan Sabon Tsarin Rance Marar Kuɗin Ruwa Da Babban Bankin Nigeria CBN  Ta Fitar Ayau

Mu tashi mu nemi bayanai akan yadda zamu karɓi tallafin babban bankin Nigeria CBN na bashi mara kuɗin ruwa wanda aka fitar da tsarin domin musulmai su ci gajiyar tallafin suma, wanda tuni bankin Nirsal suka yi nisa akan fara shirin domin baiwa mutane, dama ce ta zo mana kuma ya kamata mu yi amfani da ita wajan nema da cike duk wasu sharuɗa wanda bankin suke so mutum ya basu domin bashi wannan bashi ko nace aro.

Sharaɗi ga duk masu kamfanoni da za su nemi wannan bashi sai su na da takardun harkokin kasuwanci da kuma bayanai akan yadda annobar (Covid-19) ta shafi harkokinsu. Sannan kuma masu kasuwanci na kai a gida za su iya nema ba tare da wannan sharaɗin ba.

Shi dai wannan tallafin ya kasu kahi uku 3

Kashi na farko 1:  NON- INTEREST AGSMEIS : http://nibloans.nmfb.com.ng/agsmeisnoninterestlending

Kashi na Biyu 2: NON- INTEREST TCF (HOUSEHOLD) : http://nibloans.nmfb.com.ng/noninterestlendingtcfhousehold

Kashi na Uku 3: NON- INTEREST TCF (SME): http://nibloans.nmfb.com.ng/noninterestlendingtcfsme

Idan kunaso shafin yanar gizon yabude dasauri kuyi amfani da wayannan mahajojin Burauzin

i. Phoenix Browser

ii. Edge Browser

iii. Windows Explorer

iv. Chrome

Adadin kuɗin da kowane mai kamfani zai iya neman rancen shi ne Naira Miliyan 2,500,000, masu kasuwanci a gida kuma Naira 1,000,000.

Duk mai sha'awa zai iya cikewa ta wannan adireshi na: www.nmfb.com.ng, ko ya tuntuɓe su a lambar wayarsu: 09010026900. 

Duba wasu hotunan dan gane da rancen

Sabon shiri Daga babban Bankin Nigeria ta Hannun NIRSAL Micro Finance Bank da aka yi launching Jiya Juma'a 27th August 2021.

Tsari ne da za'a bada bashi (loan)  wa mutane domin inganta rayuwarsu kuma babu Kudin Ruwa acikin bashin (non interest Loan) 


Program Din Ya kasu kashi uku ne Gasu Kamar haka:


1️⃣ HOUSEHOLD : Shiri ne na gama garin Mutane, Wanda kowa zai Iya cikawa (Maza da Mata).


Idan mutum ya cika Wannan Tsarin zai iya samun  Kudi Naira Miliyan Daya (1M) zuwa Ƙasa.


2️⃣ SME: Shi Kuma wannan wani tsari ne da zai bawa masu ƙananan masana'antu damar bunƙasa Kasauwancinsu.


Idan Zaka cika Wannan Tsari ka Tabbatar Kanada abububuwa kamar Haka:


*️⃣ CAC Certificate, 

*️⃣ Certificate of Incorporation

*️⃣  Certificate of Business Name


Ida Ka cika Wannan Tsarin zaka iya Samun Naira Miliyan biyu da Dubu dari biyar (2.5M)


3️⃣ AGSMEIS: Shi Kuma wannan tsarine wadda za'a koyar da masu masana'antu dabarun kasuwanci na zamani, sannan Kuma a basu ranchen kayan aiki wadda darajar kudin su Kimanin Naira Miliyan Biyar (5M).


⛔ Shi wannan tsari na AGSMEIS yanada wassu dan process wadda ya hada da training, rubuta business plan, interview kokuma online Test. 


Dayawan Mutane zasu tambayi?


👉 Babu kudin ruwa ko kadan cikin wannan tsari.


👉 Idan ka taɓa cika wasu program na COVID-19 na NIRSAL Microfinance Bank a baya, Amma baka samu ba, toh zaka iya cika wannan. Amma, I dan ka samu previously, bazaka cika ba.


👉 Babu bukatar collateral ko Kuma wani guarantor.


👉 Sannan Kuma Babu bukatar kayi uploading na wani document ko hotonka. Illa iyaka BVN dinka ake bukata.


👉Zaa rufe cika wannan program din in d next 6 weeks inshallah. Amma fah Kar Ku manta, cikawa da wuri na iya baka daman samu na farko-farko wato 1st come 1st serve


DOMIN CIKAWA SAI ASHIGA LINK DAKE ƘASA👇

www.nmfb.com.ng


Ko Kuma kai tsaye


http://nibloans.nmfb.com.ng/noninterestlendingtcfhousehold


Yan'uwa ganin ba a jima da fara cikawa ba yakamata a sanar da al'ummarmu su cika wannan abin tun kafin ayi yawa, hakan zai bamu damar zama gaba gaba na farkon cikawa.
Don Allah Muyi sharing domin yan uwa su amfana mungode ku kasance damu ako yaushe

1 Response to "Karin Bayani Akan Sabon Tsarin Rance Marar Kuɗin Ruwa Da Babban Bankin Nigeria CBN Ta Fitar Ayau"