-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

ATTAJIRI YA MUTU AMMA BABU WANDA YA JE JANA'IZAR SA

ATTAJIRI YA MUTU AMMA BABU WANDA YA JE JANA'IZAR SA

ATTAJIRI YA MUTU AMMA BABU WANDA YA JE JANA'IZAR SALabari mai matukar kyau, cike da darussa.

A wani ƙauye akwai wani attajiri da mahauci da mai yin burodi. Kowace rana, mai yin burodi yana kai burodi kowani gida kuma yana ba wa kowa burodi ɗaya.

Hakama mahauci wanda bayan ya yanka sa, yake raba rabin naman ga mutanen ƙauyen. Shi kuwa attajiri, baya bada komai. Wata rana attajirin ya kamu da rashin lafiya, yanayin rashin lafiyan yana ƙara tsanani a kullum, kuma mutanen ƙauyen babu wanda yaje ya gaida shi.

Daga ƙarshe sai Attajirin ya mutu, Iyalansa ne kawai suka binne shi, mutanen kauyen sun ki taimaka musu saboda a gare su, a lokacin attajirin yake raye bai amfane su da komai ba.

Washegari bayan rasuwar attajirin, mahauci da mai burodi ba su ci gaba da ba mazauna ƙauyen komai ba. Sai mutanen ƙauye sukayi ƙorafi ga mahauci da mai yin burodi akan sun daina basu kyauta burodi da nama.

Sai mahauci da mai burodi suka sanar da mazauna ƙauye cewa: attajirin ne yake sayan burodi da nama don rabawa ga mutanen gari. Amma tunda ya mutu, bazasu iya cigaba da rabawa ba, don babu wanda zai biyasu kadinsu.

Sai mutanen ƙauyennan suka dawo duk suna baƙin ciki don yin hukuncin da bai dace ba ga attajirin bisa rashin sani.

Allah ka bamu ikon Aikata daidai don neman yardan ka.

1 Response to "ATTAJIRI YA MUTU AMMA BABU WANDA YA JE JANA'IZAR SA"