-->

FOLLOW HASKE NEWS WHATSAPP CHANNEL

FOLLOW HASKE NEWS WHATSAPP CHANNEL
To continue receiving our daily updates on news, jobs, and opportunities, please follow our new channel above, Thank you for your continued support Haskenews Media & Publishing Services
Saukakkiyar Hanyar  Magance Matsalolin Fata

Saukakkiyar Hanyar Magance Matsalolin Fata

Saukakkiyar Hanyar  Magance Matsalolin Fata



A halin yanzu, sanyi ya fara sallama a wajaje da dama. Da zarar an fara ganin hazo ko hunturo lallai wannan alama ce ta nuna cewa sanyi ya shigo. A wannan lokutan ne yakamata a fara takatsantsan wajen kulawa da fatar jiki. Idan ba’a kula da fatar ba, har sai da ta gama bushewa ko yin gautsi, hakan na daukan lokaci kafin a samu a magancesu. Don haka ne a yau na kawo muku yadda za’a magance matsalolin fata a lokacin sanyi.


· Man kadanya; tun yanzu ne yakamata a fara amfani da man kadanya a fata. Yin hakan kamar rigakafi ne domin magance matsalolin fata. Idan fata ta fara datsewa sakamakon sanyi, dole ne a yawaita shafawa domin man kadanya na dauke da sinadarai masu warkar da cututtukan fata.

 Kaushin fata; idan an kasance ana da kaushin fata, dole ne a dunga sanya man ‘glycerin’ a cikin man shafawa. Koda alwala akayi yana da kyau a yawanta shafa man domin samun saukin lamarin.

· Fason kafa; yana da kyau a rika sanya takalma masu laushi ba masu tauri sosai wadanda zasu rika illata fatar ba. Idan an kasance ana da fason kafa, sai a rika tsoma kafar a ruwan dumi da gishiri na mintuna goma sannan a rika gogewa da dutsen goge kafa sannan a shafa man ‘glycerin’ sannan a sanya safa kafin a kwanta a kullum domin samun saukin matsalar.

· Sulbin fatar fuska; a samu ayaba sannan a kwaba ta tare da kindirmo sannan a rika shafawa a fatar fuska a bari na tsawon mintuna ashirin sannan a wanke da ruwan dumi a bari fuskar ta bushe da kanta kafin a shafa mata man fuska.

· Karyewar gashi; kada a rabu da man zaitun a koda yaushe. A kasance ana sanya shi a gashi da zarar anji fatar kai ta fara bushewa. Yawaitar sanya man zaitun ko kuma man kwa-kwa na hana gashin kai zubewa.

0 Response to "Saukakkiyar Hanyar Magance Matsalolin Fata"

Post a Comment