-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

CIWON YA MACE hausa Novel

CIWON YA MACE hausa Novel

CIWON YA MACE hausa NovelA wannan yankin, ruwa ake tsugawa tamkar da bakin kwarya, ga iska mai k'arfi da ke shillo da tsayayyun bishiyoyin da ke harabar asibitin, duhun dare ya tsananta sanadiyar giragizan da suka yawaita a sararin samaniya. 


Banda walk'iya da ke haskakawa, da ba zaka iya hango ainahin abinda yake gabanka ba. 


Hankalinta ya k'ara tashi, tsoro da fargaba suka ci gaba da azabtar da ruhinta. 


Ta k'ara tattare hijabinta da niyar  tsallakawa izuwa inda ta adana motarta.
"Hajiya ba dai tafiya za ki yi ba?"
Baba Sule ya tari numfashinta.
Ta nisa cike da takaici, ta ajje walwalar da bata wuce kan fatar fuskarta ba, ta ce.
"Baba ina jira ne naga yadda hali zai yi, na bar yara a makaranta kada hankalinsu ya tashi."
Ya gyara d'aure tsintsiyar shara dake hannunsa ya ce.


"Da dai kin dan tsagaita kam, tafiya a irin wannan halin akwai had'ari a tattare da ita sai dai ace Allah ya kiyaye."
"Hakane baba."
Ta fad'a, bayan ta mayar da hankalinta akan agogon dake kan wutsiyar hannunta.
***
"Maganar banza da wofi, kin dai tafi shashanciki, har wasu ruwa akayi da zaki ce sun tsayar dake? To bari kiji Husna, wallahi ba zan d'auki wannan iskancin ba, muddin kika k'ara kai irin wannan lokacin a wurin aikin, to k'arshen zuwanki asibitin kenan."


Ya ci gaba da sababi tamkar zai yi mata duka.
Ya fice a hasale tare da banko k'ofar d'akin.


Ta ajje nannauyan numfashi ta kalli babbar 'yarta dake share kwalla. Husna ta saita fuskarta ta hanyar ajje kyakkyawan murmushin da ta san zai k'arfafa guiwowin 'ya'yanta.


K'aramar  'yarta mai shekaru hud'u ta kalli Husna tace.
"Mama, Baba zai miki duka ko?"


Husna tayi murmushi mai ciwo.
"Amina ba duka na zai yi ba, baki ga b'ata masa rai nayi ba?"
Ba tare da Aminar ta fahimce ta ba taci gaba da lamurranta.


Ta mik'e a wahalace daga kashin ruwan da tasha ta nufi bayi, ta cire kayan tare da sanya manyan kayan da zasu taimaka mata wajen kwantar da mummunan zazzab'in da take fama dashi.
A gurguje ta fito dan shiga madafa kasancewar yau itace mai girki. Tana shiga ta same Mami babbar 'yarta yar kimanin shekaru goma sha biyu tana k'ok'arin d'ora tukunya akan risho.
"A'a Mami waya aikeki?"


Mami ta kwab'e fuska cike da tausaya Mamarta tace.
"Mama baki da lafiya fa, dan ki bari in yi girkin yau sai anti Sakina ta nuna min komai."
"Haba Anti, ni fa nace tazo muyi girkin tun da naga kin sha ruwa kan hanya. Jeki sha magani kawai ki huta."


Sakina ta shigo madafin tana fada, yayinda ta d'auko kayan miya markadaddu.
Ganin babu yadda zata yi yasa ta juyawa tareda cewa.
"To shikenan, amma kada ku sa yaji dan Allah."
Ta fice tare da komawa d'akin dan gabatar da sallar magrib da taji ana yi, bayan tayi sallar ta d'an kwanta jin yadda kanta ke tsananin sara mata.
"Mama ki fito ga Baba ya dawo."
Amina ta tasheta daga baccin da ya sureta akan tabarmar salla.


Ta mik'e jiki a mace ta shiga bayi ta kuskure bakinta.
Dukansu a babban falo ake cin abinci dan haka kai tsaye can ta wuce. Tayi masa sannu da zuwa ta shiga gabatar da abincin.
Tuwon shinkafa da miyar kub'ewa sai k'amshin man shanu da aka zuba.
Ta zuba masa yayin da Sakina ta zuba nata ta zuba ma yara.
Daga lomarsa ta farko ta hango babban tashin hankali akan fuskarsa, jikinta ya fara rawa tuni hawaye suka ciko kwayar idanunta.


A hasale ya ture farantin ya watsa mata mugun kallo.
"Ke! Ba na ce kada ki k'ara girka min abinci akan risho ba? Meye amfanin itacen da na kawo? Wane irin iskanci ne yake damunki?"
"Ba...ba ni da lafiya ne...sai...sai Mami..."


"Tas!"


Ya d'auketa da kyakkyawan marin da yasa ta wuntsilawa har cikin abincin da ke gabanta.
Yaran suka fashe da kuka mai tsanani, Mami ce taja hannun sauran yaran suka shige d'aki yayin da Sakina ta mik'e a hasale.
"Wai ke Sagir wani irin mutum ne da ba zai tab'a yin uzuri ba? Matar nan ba tada lafiya, sannan kace sai anyi maka abinci akan itatace da sanyin daminar nan? Taya wuta zata kama itacen da suka sha kashin ruwa? Idan kayi zuciya kaje ka siyo gas mana idan kuma jira kake sai na sayo ayi maka girkin to wallahi kuwa ka fad'a kwata. Kuma ba zamu fasa girki da risho ba dan ba zamu iya hasa wutar murhu acikin ruwannan ba, mtsss!"


Taja mugun tsaki ta mik'e.
Yayi shiru tamakar ruwa sun ci sa.
"Munafukar banza ba zaki tashi ki bani wuri ba?"
Sakina da har ta kai k'ofa ta juyo ta watsa masa mugun kallo tace.
"Da ni ka ke?"
"Ba da ke nake ba malama."
Ya daka mata tsawa, wadda tasa Husna mik'ewa a guje ta shige d'akinta.


A k'aramin falonta ta tarar da yaranta kwance akan tabarma, Amina da Kausar sai kuka suke, yayin da Mami ke lallab'a su.


Ba tare da tace musu komai ba ta wuce k'uryar d'akinta tana rera kuka mai tab'a zuciya.
***


Husna Kabir Dikko, haifaffiyar garin Sakkwato ce. 


Lokacin da ta cika shekaru goma sha biyar ne Kawunta Tasi'u ya aurar da ita ga Sagir Sambo Kware, auren soyayya suka yi, haka kuma suna cikin kwanciyar hankali kasancewar yana da rufin asirinsa. Kawu Tasi'u ya d'auki nauyin karatunta tun daga kan Sakandire har ta samu gurbi a makarantar koyon jinyar mahaukata, wannan shine babban burinta a rayuwa, tana fatar ta samu damar kula da mahaifinta dake fama da cutar kai. Haka kuwa aka yi bayan shekaru hud'u lokacin ta na da 'ya'ya biyu ta fito da sakamako mai kyau, ba tare da b'ata lokaci ba ta samu gurbin zama ma'aikaciya a asibitin mahaukata dake garin Kware. Kasancewar mijinta Sagir acan yake, dan haka ba ta samun matsalar zuwa aiki ko kad'an. 


Kwatsam! Wutar matsaloli ta fara ruruwa a wannan gidan, tashin hankalin yau daban na gobe daban. Har ta kai Sagir na d'aga hannu ya daki Husna akan rashin fahimta k'alilan, musamman da ya samu kariyar arziki sai ya dawo tamkar mai tab'in kwakwalwa, ko kad'an baya yin uzuri dangane da lamurran cikin gidansa. Duk da kasancewar da rabin albashin Husna suke cin abinci, yayin da rabin take amfani dashi wajen kula da mahaifinta Kabiru.


Ana cikin haka ya fara neman aure, a cewarsa zai samo 'yar masu hannu da shuni dan shima ya samu, Ba tare da nuna damuwa ba Husna ta taimaka masa da kaso sittin na cikin hidamar neman auren Sakina, itama 'yar cikin garin Sakkwato ce, tun zuwanta gidan ta fahimci halin tsangwama da tsoro da Husna take ciki, hakan ya bak'anta zuciyarta dan ita macece mai son adalci a duk inda take, haka kawai kuma Ubangiji ya d'ora mata k'aunar Husna da 'ya'yanta. 


To a yanzu itace mafi gatan Husna a gidan, dan ita kad'ai ce mai takawa Sagir burki a duk sa'adda yazo cin mutuncinsa.


Matsala biyu da biyu ta hadewa Husna, ga Mahaifinta dake fama da ciwon hauka mai tsanani a cikin asibitin da take aiki ga matsalar Sagir da ya mayar da ita tamkar abokiyar adawarsa.


Wannan kenan.
***


Da sanyin safiya Husna ta tashi da zazzabi mai k'arfi, da yake Sagir bai kwana d'akinta ba, dan haka ba shi da masaniya har sai da ya shirya ya fito dan zuwa buga-bugarsa. 


A falonta ya same Mami na shirya yara zuwa makaranta, Sakina kuwa tana kitchen tana had'a musu abin kari. 


Fuska a d'aure ya amsa gaisuwar da suka yi masa cike da tsoronsa.
"Ina uwarku?"
Mami ta sadda kai tace.
"Tana ciki ba tada lafiya."


Ya mik'a zuwa d'akinta, a can k'arshen katifa ya hangota tana rawar sanyi.
"Wani sabon iskanci ne? Baki da lafiya kuma ba zaki iya fita ki samo magani ba? To meye amfanin bokonki? Indai haka malaman Mahaukata kuke to wallahi kuma lafiyar bata isheku ba."
Ya ciro kud'i daga aljihunsa ya jefa mata.
"Ga dubu goma daga cikin albashinki, sauran na biya bashi saura kuma za a samu abinda za'a ci."


Ya gyara zaman hularsa ya fice ba tare da ya damu da halin da take ciki ba.


Husna ta yaye k'aton bargon da tayi rufa dashi, tana jin ciwon da zuciyarta ke yi, tana mai takaici da Allah wadai da irin rayuwar da suke gudanarwa tsakaninsu.


Albashinta Naira dubu tamanin da biyar, amma daga ciki dubu goma ta samu. Ba yau ya saba ba, ba wannan ne farau ba, hakan da yake yi mata ya tilasta mata fara sayar da kayan d'akinta har sai da suka k'are karaf, face tabarmi da katifa biyu da suke kwanciya ita da 'ya'yanta.


Bayan fitarsa Sakina ta shigo d'akin tana faman zuba salati da sallallami.
"Anti ki tashi ki gani wai Sagir aure zai k'ara, wallahi yanzu Ummar gidanmu ke sanar dani k'awarta zai aura."
Duk da ciwon da take fama dashi hakan bai hanata mik'ewa zaune ba hankali a tashe.
"Aure fa Sakina? Ina zai saka ta?"
Sakina ta tab'e baki tace.
"Ohon masa, ai bari ya dawo ayi duk wadda za a yi wallahi dan sai na bar gidan nan a yau. Munafikin banza da wofi."


Husna ta kwantar da kai tare da rik'e hannayen Sakina ta ce.
"Haba Sakina, mijinki ne fa. Ki daina jifarsa da irin wad'annan kalaman, amma dai wannan karon ba zan k'ara bari ya cutar dani ba, Insha Allah ba zai yi auren ba."
"Hum! Ni meya shafe ni, wallahi ko yau na ya sake ni yasan ina da gata gaba da baya, ina dubu da zasu fito neman aurena."
Wannan maganar ta sosa ran Husna, ta tabbatar 'yan uwa gata ne a wajen mutum, to ita ai ya zame mata dole ta lallab'a da Sagir dan bata da kowa kaf a duniyar nan, Kawu Tasi'u ne, kuma yanzu babu shi a doron k'asa.
***
"So nake ki kwashe kayan kazantar nan naki, ki koma d'akin can na yara, gyara za ayi min anan."


Ya watso mata kalaman a wulak'ance.
Hawaye suka gangaro akan kumatunta, da kyar ta iya k'ok'arin cewa.
"Haba Sagir, yara ukku da ni a wancan d'an k'aramin d'akin? Ni dai bana buk'atar wani gyara ka bar min d'akina a haka."
Ya watsa mata mummunar harara kana yayo kanta a hasale.
"Ke? Har kin isa na baki umurni ki tsallake? To bari ki ji, bake zan gyarawa ba, gida nawa ne bana kowa ba dan haka ki tattara ki koma can idan kuma can d'in yayi miki kad'an sai kwashi kayanki ki koma gidan mahaukata dama 'yarsu kike."
Wad'annan kalaman sun k'ona mata zuciya sosai, hakan ya tilasta mata cewa.
"Ni ce d'iyar mahauka?"


Tayi guntun murmushinta mai karya zuciyar masu imani.
"Babu komai, naji d'in d'iyar Mahaukata nake kuma Alhamdulillahi tun da ni ban had'u da hauka akan talauci ba..."


Bata k'arasa ba ya d'auketa da mummunan marin da yayi sanadiyar wuntsilawarta har sai da ta buge bangon gini, nan take bakinta ya fara feshin jini. Ta fashe da wani irin kuka mai azabtar da ruhi.


Dai-dai lokacin su Mami suka shigo gidan, Sakina kuwa ta fito a d'akinta a guje.
"Amma wallahi Sagir ba kada imani, kuma wallahi tallahi yau sai na bar maka gidan nan ba dai mu zaka ha'inta ba? Kuma ina tabbatar maka Allah zai fitar da alhakin matar nan akanka."
Ya finciko Sakina ya hasale ya had'ata da bango.
"Kar ki gaya min maganar banza akan wata shashasha wallahi yanzu zan bangarar da ke."


Ta fincike shi da k'arfi tsiya har sai da yayi taga-taga zai fad'i.
"An gaya maka banzar, kai ne banza ai, kana cutar mace dan kaga tana hak'uri da kai, dan kaga ba tada kowa to wallahi ina gaya maka sai kayi dana sani..."


Zuciya ta kai sa da d'auketa da mari biyu masu kyau.
"Ni? Ni ka mara? Ai wallahi ka mari aurenka kuma sai nayi sanadiyar rufeka a gidan yari."
Ta fashe da kuka, a gaggauce ta koma d'aki ta had'a akwatinta ta fito.


Lokacin Husna kad'ai ce a falon tana sharbar kuka, tana ganin Sakina ta fito ta rugo gareta tana cewa.
"Haba sakina, dan Allah kada ki tafi ki bar ni. Dan Allah kiyi hak'uri laifina ne bana shi ba."
"Ke kam dai kinji haushi Anti, ban san wane irin so kike yiwa mutumen nan ba. To wallahi ni ba zan zauna ina kallon wannan cin kashin ba."


Taja gyalenta ta bar gidan.


Husna ta rab'e a k'ofa tana ci gaba da rera kuka, ta na mamakin zuciya irin ta Sakina, ita kam tayi sa'ar kishiya ba kamar wadda Mahaifiyarta ta zauna da abokiyar zamanta ba, ba ta tab'a tunanin sauran kishiyoyi ba irin Baba delu bane, ashe har yanzu akwai mutanen kirki.
Sakina na zuwa gida ta fayyace ma mahaifanta sanadiyar zuwanta, dama ta jima tana sanar dasu irin gallazawar da Sagir yake yiwa Husna.


Dan haka nan take Babanta ya kira Sagir ya tilasta masa ko ya saki Sakina ko kuma su maka shi a kotu.


Zuciyarsa a haye ya surfawa Baban sakina zagi ya bashi takardar saki biyu.
Kai tsaye gida ya shigo kamar dodo yana kwalawa Husna kira.


Jikinta na rawa ta fito daga d'akin yara.
"Munafuka? Kin rabani da Sakina kin huta to wallahi baki isa ba. Sai na yi miki mugun duka sannan kuma na sake ki saki ukku."


Ya b'alle mad'aurin wandonsa ya shiga bugunta ta ko ina. 


Husna tayi kuka tayi neman agaji har kuka ya gagareta, Mami ce tayi k'arfin halin fad'awa jikin Mamarsu ganin Sagir yana neman kasheta.
"Baba dan Allah ka daina dukanta, wannan zalunci ne."


Mami ta face da kuka tana jijjigar Husna da ta d'auke wuta. 


Cike da tashin hankali Mami ta haske fitila inda taji abu na zuba daga k'asan Mamarta, Jinin da ta gani ya k'ara daga hankalinta.
"Wayyo Allah, Mama kada ki mutu."


Ta fashe da kuka ta ruga izuwa ga Sagir dake zaune kan dakali yana mayar da numfashi.
"Baba ka taimaka, wallahi mutuwa zata yi."
"Ta dad'e bata mutu ba."
Ya mik'e a fusace ya bar gidan.


Mami da sauran yaran suka zagaye Husna suna kuka ba tare da sun san takaimammen abun yi ba.
Da safe k'arfe goma da rabi 'yan gidan su Sakina tare da ita suka zo kwasar kayan d'akinta.


Suna shigowa suka tarar da Amina da Kausar zaune a bakin k'ofar gidan, suna ganin Sakina suka yi kanta suna kuka.


Mami ce ta fito fuska a kumbure ta fad'a jikin Sakina tana cewa.
"Anti ki ka barmu gashi mama ta mutu ita kad'ai."
"Subhanallahi! Ina maman taku?"


Nan take suka nufi inda Husna take kwance a sume.


Basu yi wata-wata ba suka kwasheta sai asibiti.


Wanki ciki akayi mata sanadiyar cikin wata ukku da ya zube mata.
***


"Yanzu shi Sagir d'in duk ya sake ku? Ke har saki ukku anya lafiyarsa k'alau kuwa?"


Mahaifin Sakina yake jajantawa lokacin da Husna ke basu labarin abinda ya faru, taja dogon numfashi tace.
"Baba ni na godewa Allah da ban mutu a hannu 'ya'yana ba kamar yadda Mahaifiyata ta mutu a hannu na, Duk abinda Sagir yayi min sakayya ce ta bashin da mahaifina ya d'aukar min."


Ta fashe da kuka mai tab'a zuciya tana tonanu mugun tab'on da yaki gushewa a birnin zuciyarta.
"Tun ina 'yar shekaru goma na fahimci zaman bak'in ciki da mahaifiyata take a gidan Mahaifina, tana fama da ciwon zuciya mai tsanani da ciwon tari tun tana k'arama, wani abun mamaki mahaifinmu baya iya saye mata magani koda farasitamol ne, kuma duk ranar da yayanta kawu Tasi'u ya aiko mata da magani to fa ranar za a ga tashin hankali da masifa, har duka inda rabo samu take yi, muyi kuka har sai mun gode Allah, abinci ma sai munyi jari bola sannan mu samu abinda zamu ciyar da kanmu, bamu isa muje neman taimako ba wajen Kawu, har muka hak'ura muka saba da rashin zumuncin dake tsakaninmu.


Ba zan manta ba 'yar uwata Hassana ta mutu ne sanadiyar Mahaifina, wata rana ciwon Mamanmu ya tashi Hasana taje dan ta sanar da Babanmu a mashayarsu da yake zama da dare, bayan ta sanar dashi ya balbaleta da fad'a ya koreta, a saman hanya Abokanansa suka bi bayanta suka hakk'e mata, suka lalalata rayuwarta wanda yayi sanadiyar mutuwarta.


Bayan wasu kwanaki ciwon Inna ya tsananta.


"Husna je ki kira min babanki dan Allah."

0 Response to "CIWON YA MACE hausa Novel"

Post a Comment