-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Cikakken Bayanin Yadda Zaki Gamsarda Mijinki Ta Hanyar Jima'i

Cikakken Bayanin Yadda Zaki Gamsarda Mijinki Ta Hanyar Jima'i

Cikakken Bayanin Yadda Zaki Gamsarda Mijinki Ta Hanyar Jima'i



GAMSAR DA MIJINKI TAHANYAR JIMA'I


Gamsar da namiji a jima’ince yafi sauki wajen gamsar da mace, duk kuwa

da cewa dukkannin halittan da aka yiwa mace a jima’ince suma maza suna

da irinsa. Kamar yadda ake samun harijin namiji haka nan ma

ake samu harijan mace, yadda ake samu mazan da suke jimawa babu gajiya

a lokacin jima’i hakama matan. Ana samun maza da mata ragwaye a wajen

jima’i da kuma wadanda sam jima’in ma bata damesu ba a dukkannin

jinsunan biyu.

Da akwai wasu mazan da basu cika son doguwar wasannin motsa sha’awa

ba, wasu kuwa suna bukatan lokaci maitsawo ana masu wasa duk kuwa da

macen tafi namiji bukatar wasan motsa sha’awa mai tsawo.

Abu na farko daya kamata mace ta fahimta a tattare da mijinta shine

abunda yafi bukata a yayi wasannin motsa sha’awa da kuma lokacin

kwanciya irin na jima’i, domin da akwai inda da zaran mace ta tabawa

mijinta maimakon ta motsa mishi sha’awarsa sai kawai sha’awar tashi ya

gushe. Hakama a kwanciyar jima’i, yana da kyau ki fahimci irin yanayin

kwanciyar da mijinki yake so. Shi yasa malamai na jima’i sukecewa

sadarwa a jima’i yanada matukar alfanu ga ma’aurata domin ta hanyarce

zasu iya fihimtar abubuwan da suke bukata a yi musu kamin, lokaci da

kuma bayan jima’i.

Da akwai mazan da zaran mace ta fara wasa dasu nan da nan suke gamsuwa

ba tareda sun shegetaba, da akwai wadanda da zaran azzakarinsu ya

shiga shikenen kuma sunyi zuwan kai kenan. A akwai mazan da sukan

dauki lokacin mai tsawo suna jima’i da mace kamin suyi zuwan kai, wasu

mazan kuwa a lokacin da suke kawowa a lokacin ne gabansu ke kara yin

karfi har sai sun kawo sama da biyu koma biyar kamin suke gamsuwa da

mace. Ke naki mijin yaya yake, domin dole sai kin fahimci yadda yake

kamin ki iya gamsar dashi.

Sai dai maza masu wuyan sha’ani a jerin mazan da na ambata sune masu saurin zuwan kai da kuma masu daukan lokaci mai tsawo suna gurza mace basu gamsu ba, sai dai kuma da zaran mace ta samun illimin sarrafa

irin wadannan maza ta gama dasu. Maza masu saurin zuwan kai sune mazan da sukafi cutar da matansu, domin wata matan sai ta gurzu

take gamsuwa, don haka matsalar irrin wannan mazan yana tattare ne da

kodai suna da cuta da suke bukatar ganin likita, ko kuma sabbin shiga ne wato mazan da suka yi aure sabo-sabo ko suka jima basu yi jima’i ba

hakan na faruwa da su.

0 Response to "Cikakken Bayanin Yadda Zaki Gamsarda Mijinki Ta Hanyar Jima'i"

Post a Comment