Bayanin Yadda Ake SURPRICE COOKIES
Bayanin Yadda Ake SURPRICE COOKIES
*MUKOMA KITCHEN2,2&3*
馃嵐馃嵎馃崡馃嵈馃崝馃構
*_SURPRICE COOKIES_*
_*Ingredients*_
_fulawa_
_kwai_
_Dabino_
_kwakwa_
_Baking powder_
_vanillah_
_butter_
_suger_
_madara_
_*Method*_
_Zaki samu butter da suger ki hada su ki bubbuga har sai suger din ya narke sai ki zuba kwai da madara ki juya ki zuba vanillah sai ki hada garin fulawa da Baking powder ki dinga barbadawa a cikin kwabin butter din da kika yi kina juyawa har yayi tauri ya dan fi kwabin cake kauri kar ya kai na cincin sai ki ajiye ki dakko dabino mai kyau ki gurza a greater ki ajiye shi a gefe sai ki samu kwakwa ki kankare bayanta itama ki gurza ki ajiye ki fasa kwai shima ki ajiye a gefe sai ki dinga dibar kwabin da kika yi na fulawa kina dunkulawa ki taba shi da hannunki yayi fadi kar yayi tudu sosai sai ki saka shi cikin dabinon ki dangwalo sai ki tsoma cikin ruwan kwai ki barbade shi da garin kwakwar da kika gurza sai ki ajiye ki ta haka har ki gama sai ki jere shi a farantin gashi ki sa a oven ya gasu_
_*By: Admin:*_
_*Aysha Suleiman*_
_07066189950_
_*Aysha Haruna*_
_07062430310_
*MUKOMA KITCHEN1,2&3*
馃嵐馃嵎馃崡馃嵈馃崝馃構
0 Response to "Bayanin Yadda Ake SURPRICE COOKIES"
Post a Comment