BAQAR MACE Hausa Novel
usa Novels
MEENATU DMS!
BAQAR MACE Hausa Novel
1
Haba mana Farouq try to undrstnd me mana!
Why can't you open your eyes and see what i'm
trying to tell you??
Nifa i'm not rediculing her, i just want you.....
Farouq ne ya tsaida shi ta hanyar daura hannun
sa bisa lips dinsa.
Farouq yace Ishaq nifa idan ba xaka bani goyon
baya ba akan wannan yarinyar toh wallahi ka
gyale ni.
Ishaq yace nikam banga abnda ka gani jikin
wannan BAQAR MACEN BA!
Gata BAQA ga Muni, kai nifa wallahi na rasa gane
kan wannan yarinyar.
Kuma ni abnda yafi bani haushi, yadda take da
wani irin jan aji kamar wata mai kyau.
Farouq juyowa yayi da manyan idanun sa, yace
jan aji ay abu ne mai kyau.
Duk macen da bata da jan aji ay ba mace bace.
Ishaq dafa kafadar Farouq yayi, sannan yace
Farouq dan Allah ka dubi kanka.
Ka duba kaga dame Allah ya rage ka. Amma ka
rasa wacce xaka ce kana so sai wannan BAQAR
halittar.
BAQAR MACE!
Kafa duba kaga yadda mata masu class kyawawa
suke sonka.
Some of them are even crying for your love while
some are begging.
Amma duk baka ga wannan abun ba.
Sai ka rasa inda xaka mace saiga BAQAR MACE.
Farouq buge hannun Ishaq yayi daga kafadar sa.
Sannan yace mata marar sa class dai, duk macen
dake liqe ma namiji ay bata da class.
Ishaq yace toh ay ba haramun bane, domin
Annabin mu yace mace tana da right din da xata
fadi ma wanda take so cewar tana son sa.
Is just that wannan xamanin da muke ciki mutane
sun maida abn wani abu daban.
Farouq yace maganar ka gaskia ne, amma kaima
kasan yanxu mace tace tana sonka saika raina
ta.
Kai nifa kada ka isheni da wasu surutun banxa.
Kawai ka samo mani wata idea yadda xan samo
kan Farida.
Ishaq daria yayi sannan yace kai yanxu dan Allah
ba xaka ji kunyar nuna ta cikin friends dinmu
ba??
BAQAR MACE!
Ka dube kafa! Babu ta inda Allah ya rage maka
kamala.
Amma ka rasa.... Farouq yace kai dallah Malam
rufe mani baki.
Taya xanji kunyar nuna abnda nake so?? Idan
kana tunanin xanji kunyar nuna Farida idan na
aure ta.
Toh wallahi kayi kuskure, domim idan akwai
abnda nake qauna sosai toh Farida ce.
Kuma babu abnda xai hanani nuna ta ga abokai
na da duk wani wanda ya dace yasan ta.
Idan ma kana tunanin nam toh garama ka daina.
Ishaq yace yayi maka kyau, amma nidai....
Farouq yace my dear please kindly get out of my
room!
Kama hannun Ishaq yayi, saida ya fidda shi daga
dakin sannan ya kulle qofar dakin ya koma
hisa gado ya kwanta.
Rufe idon sa keda wuya, ya fara tunanin Farida.
Addu'a yake cikin ransa Allah yasa Farida ta fara
sonsa. Kamar yadda shima yake sonta.
Da wannan tunanin bacci yayi gaba dashi.els
MEENATU DMS!
BAQAR MACE!
4
Farida ce xaune ita da Umman ta suna cin abnci!
Bayan sun gama Farida ta kauda komai ta dawo
wurin Umma ta xauna.
Daura kanta tayi bisa qafar Umma yayin da
Umma ta kira sunan ta.....
Farida amsawa tayi, Umma ta shafa kanta tare
da fadin.
Farida ya kamata ki nutsu ki daina ma Farouq
abnda kike masa.
Nifa wallahi ina son yaron nan, yaro mai hankali
ga nutsuwa.
Amma ki tsaya kiyi ta ja masa aji, ki lura da
abnda hausawa ke fada idan jan aji yayi yawa.
Toh fa ajin tsinkewa yake. Dan haka ki daina
masa abjda kike masa kada Allah ua jarrabe ki
kema.
Kifa duba kiga yaron nan kamar balarabe,
Barakallahu!
Amma ya tsaya ya nace akan shidai ke yake so.
Ke kanki kinsan idan dan ta kyau ne da koh
kadan Farouq baxai taba cewa tana sonki ba.
Ke kanki kin san gaskia, Farouq baku ma dace
dashi ba.
Domin yayi miki nisa, kawai dai Allah ya dora
mishi sonki.
BAQAR MACE!
Toh Umma In Shaa Allahu xan gyara hali na.
Amma wallahi.... Umma tace nidai ban son jin
wata magana.
Ki gyara halin ki! Ki gyara halin ki!! Ki gyara halin
ki!!!
Farida cewa tayi toh Umma, baxan sake yi masa
abnda nake ba In Shaa Allahu.
Umma tace toh shikenan Allah yayi miki albarka.
Bayan sun gama maganar ne Farida tace Umma
bari naje nayi wanka.
Umma tace Allah yasa a fito lafia kedai Allah ya
daura miki yawan wanka.
Farida daria tayi ta wuce daki, bayan ta gama
wankan ta.
Ta shirya cikin wata atamfa riga da skirt! Kayan
sunyi mata kyau ta sha uban jan baki.
Abun ka ga BAQAR MACE kwalliyar fuskar tata ba
wani fice tayi ba. Duk da uban jan bakin da tasha
.
Sai qamshi ke tashi daga jikin ta, domin Farida
akwai son qamshi.
Har fatar jikin ta qamshi take ko ta saka turare
koh bata saka ba.
Ita Umma abn har mamaki yake bata. Wani lokaci
kuma abn ya daure mata kai.
BAQAR MACE!
Bayan ta dawo parlour ta xauna! Taji wayar ta na
ringing.
Tasan koh baa fadi mata ba tasan cewar Farouq
ne.
Umma kallon ta tayi sannan tace ba xaki dauki
wayar bane koh yaya?
Farida tace aa Umma dauka xanyi, Umma tace
kedai jan aji yayi kyau dake.
Daukar wayar tayi, yau da sauki domin ta saki
fuskar ta.
Gaishe dashi tayi, nan yake gaya mata cewar
yana qofar gida.
Ce mashi tayi ya shigo kasan cewar Abba ya
hanata xance qofar gida.
Bayan sun gama maganar ta kashe wayar, Umma
tace toh saura ki kwada masa baqin hali.
Farida daria tayi tace kai Umma bafa ni da Baqin
hali kema kin sani.
Umma tace toh ay Baqin hali kike kwadawa
Farouq. Farida tace ay Umma baxan sake ba.
Umma daki ta wuce yayin da Farida itama ta
koma daki domin qara gyarawa.
Duk da cewar babu abnda kwalliyar fuskar ta
tayi. Amma saida ta sake feshe jikin ta da turare,
sannan ta dauki gyalenta ta yafa.
Saida taje kitchen ta dauki trey ta hada masa duk
abnda ya dace sannan ta nufi parlourn baqi.usa Novels
MEENATU DMS!
BAQAR MACE!
7
⃣ Da sallamar ta tashiga parlour, shi kadae ta
tarar hakan yasa taji wani dadi.
Domin dama bata son ganin Ishaq domin tasu
bata xo daya.
Da xaran yaxo tofa dama kafin ya tafi sai sunyi
fada.
Ta gaishe da Farouq cike da ladabi, domin yau ta
saki fuskar ta.
Farouq ganin smiling dinda yake afuskar Farida
ba qaramin dadi yake ji ba.
Dan ya lura da canjin da aka samu daga fuskar
ta.
Ya lura yau duk maganar da yayi mata cikin
ruwan sanyi take maida masa sabanin yadda
suka saba firar tasu.
Farouq cikin jin dadi ya kalli Farida yace please
Farida will you marry me??
Daria idan da sabo ta saba jin wannan kalmar
daga bakin Farouq.
Yanxu kam Farida rufe fuskar ta tayi sannan ta
ruga da gudu ciikin gida.
Farouq smiling yayi tare da fadin why the sudden
changed from my Fari?
Daga hannu yayi sama ya roqi Allah akan ya
daura sa bisa Farida.
Tashi yayi ya nufi parlour wajen Umma.
Da sallama ya shiga, ya kuwa ci saa Umma tana
xaune.
BAQAR MACE!
Waje ya samu kusa da qafar Umma ya xauna.
Bayan ya gaishe ta sunyi fira kamar yadda suka
saba.
Farida ta fito parlour, abn ya daurewa Farouq kai
daga shi har Umma.
Dan bata taba xuwa parlour ba idan Farouq yana
xaune da Umma.
Yau kuwa gashi har tana dan saka musu baki
cikin firar tasu.
Ahankali take kai idonta kan Farouq.
Cikin ranta take fadin, Allah yayi halitta, Umma
dai ta lura da yadda Farida take satar kallon
Farouq.
Farouq shima tun bai lura ba, har takai sun saida
suka hada ido da Farouq sau 2.
Kunya ta kama Farida hakan yasa akaro na biyi
da suka, hada ido saita ruga daki.
Shi Farouq abn daria ya bashi, haka Umma!.
Umma ce take ta qara kwantar masa da hankali!
Aranar haka Farouq yabar gidan, cike da farin ciki!
Driving yake amma hankalin sa yana kan Farida
da yadda tayi behaving infront of him!
Dadi yaji sosai harya qagara ya koma gida domin
sanar da Ammi abnda yake faruwa.a Novels
MEENATU DMS!
BAQAR MACE!
9
Farouq ne xaune gaban Umma sai labari yake
bata akan yadda Farida ta canxa.
Suna cikin wannan maganar Ishaq ya shigo.
Da sallamar sa ya isa wajen Umma.
Waje ya samu ya xauna bayan sun gaisa yaji
labarin da Farouq yake bama Umma.
Ishaq wani irin kallo yayi masa!
Sannan yace Umma wannan yarinyar fa ashe
bayan Munin ta har Aljanu ke gare ta.
Umma tace Aljanu fa kace??
Farouq wani mugun kallo yayi masa tare da fadin
Ishaq i don't want to see your face again in my
whole life time.
Please get out of dix house, i really don't know
your problem, why are poking your nose into my
affairs?
Umma ce tace Farouq keep your mouth shut!
Farouq komawa yayi ta xauna sannan yace
Umma wallahi Ishaq haushi yake bani yanxu.
Wai bai san babi kyau xuga cikim aure bane koh
yaya?
Kuma abnda yafi bani haushi wannan yarinyar
babu abnda tayi masa.
Infact bata da wani baqin hali wanda xaisa
mutum yaqi auren ta.
BAQAR MACE!
Amma kawai yabi ya dame ni, kamar shi xai
xauna mani da ita.
Bayan dubun kushe ta da yake kuma yanxu yaxo
mani da wata magana wai tana da aljanu.
What's there dan tana da aljanu?
Shi mai aljanu ba mutum bane? Koh ba haka
Allah yake son ganin mutum ba?
Look Ishaq macen da nake da ra'ayi xan aure not
your choice.
Dan haka kada ka sake kawo mano wata magana
akan Farida.
Ba Aljani ba koma miye In Shaa Allahi xan aure
ta.
Umma ce tace Farouq tashi ka shiga daga ciki
and i don't want to hear a word from you again.
Bai sake cewa komao ba ya fita kamar yadda
Umma tace.
Bayan ya fita Umma ta kalli Ishaq ta kira sunan
sa.
Umma tace Ishaq tunda Farouq Allah ya daura
masa son wannan yarinyar bana son kana sage
masa qafa.
As his best friend kamata yayi ace kai kake bashi
goyon baya.
BAQAR MACE!
Umma tace kuma kai waye ya fadi maka cewar
Farida tana da Aljanu??
Ishaq yace wani dan anguwar sune yake fadi
mani.
That's why nace bari na fadi may be koh ya fasa
auren nata.
Umma tace ka taba ganin inda lalurar Aljanu ta
hana aure??
Nidai ina ganin it will be better idan ka daina
kushe Farida tunda itace Choice dinsa.
Kasan it hurts a lot abnda mutum yake striving
akan sa.
Ya xamana ana sage masa guiwa!
Bare yanxu daya samu yadan fara shawo kanta.
Ishaq yace toh shikenan Umma In Shaa Allahu
baxan sake ba.
Dama gani nayi duk kyaun Farouq yace yana son
wannan.
Umma tace babu komai ka dai taya shi da addu'a
Allah yasa ta xame masa abokiyar kwarai.
Ishaq yace toh ameen Umma.
Haka Umma tayi ta masa nasiha, daga qarshe
suka yi sallama.
Umma tunani take yi wanda ita addu'ar ta Allah
yasa Farida taso Farouq kamar yadda yake sonta.
Umma na cikin maganar Ibrahim ya shigo, ya
xauna kusa da ita.
Umma tace Auta harka dawo... Ibrahim yace eh
Umma....
Umma tace toh kaje kaci abnci saika dawo.
Miqewa yayi ya qara gaba, tare da cewa Umma
ina big Brother? Umma tace yana daga ciki.......
MEENATU DMS!
BAQAR MACE!
12
⃣ Farida ce xaune sai baqin rai take, tunda
Umma taga haka tasan cewar Aljanun ta ne suke
da niyyar tashi!
Gashi gida babu kowa hakan yasa Umma ta
dauki wayar ta, ta kira Malam Ahmad qanin
Abban Farida.
Domin dama shine yake mata Ruqiyya!
Kamar jira suke Umma ta gama wayar kuwa
Aljanun Farida suka taso.
Umma ce taje ta debo ruwa cikin cup tayi mata
addu'a sannan ta watsa mata ruwan.
Aljanun Farida sai ihu suke, suna kiran ki daina
watsa mana wannan ruwan.
Umma suna cikin wannan hali sai ga Baba Sani
ya shigo da sallamar sa.
Nan ya shiga yi mata Ruqiyya, koh da aljanin ya
fita nan take Bacci ya dauke Farida.
Dama haka suke mata duk lokacin da aljani ya
fita toh saita yi bacci.
Idan kuwa batayi bacci ba, toh xata tashi jikin ta
sam babu kwari.
Wani lokaci sai ta riqa tambayar yaushe Baba
Sani ya xo or some thing like that.
Baba Sani ne yace Allah dae ya kawo ma yarinyar
nan sauki.
Umma tace ameen, amma yanxu naga abn da
sauki tunda yanxu tana kai kamar wata uku basu
tashi.
Unlike da tunda a da cikin sati sai su tashi sau 3!
Baba Sani yace gaskia kam abun sai godia.
Ahankali cikin ikon Allah sai kiga sun rabu da ita
har abada.
BAQAR MACE!
Umma tace Allah ya nuna mana ranar da xasu
rabu da ita gaba daya.
Domin wallahi yarinyar nan tana bani tausayi!
Tun bare idan ta tashi tana tambayar abnda ya
faru bayan sun sauka!
Ni roqona daya Allah yasa har ta ida karatu ba
xasu tashi ba!
Baba Sani yace ameen!
Alhajin baya nan ne? Umma tace eh bai dawo ba,
amma nasan kamar yanxu yana bisa hanya.
Bata gama rufe baki ba kuwa saiga Abba ya
shigo da sallama.
Baba Sani yace kin kuwa gani gashi nan!
Nan Abba ya xauna suka gaisa, yayin da Umma
taje dauko masa ruwa.
Bayan ta dawo yake tambaya halan Aljanun
Farida ne!
Umma tace ay kuwa dai sune! Abba yace toh
Allah ya sauke ma dan uwa musulmi.
Gaba daya suka amsa da ameen!
Bayan Baba Sani sunci abnci ne ya tafi gida.
Nan Umma da Abba suka cigaba da tattauna
matsalar.
Suna cikin maganar saiga Fatima da Hindatu sun
dawo.
Bayan sun gaida mahaifan nasu ne suke
tambayar Yayar tasu.
Umma tace tana daki, su shiga daga ciki.
Basu qara magana ba kuwa sukayi hanyar daki,
kowa da abnda yake saqawa cikim xuciar sa.usa Novels
MEENATU DMS!
BAQAR MACE!
14
⃣ WACECE FARIDA???
Cikakken sunan ta shine Farida Ahmad Mahaifin
ta Ba Kano ne amma suna xaune a Kaduna!
Mahaifinta yana da kudi but not that much dai
dai misali.
Sunan mahaifiyar ta Hajia Asma'u!
Mahaifiyar ta itama yar Kano ce aure ya kawo ta
Kaduna!
Mahaifan ta mutanen kirki ne! Gasu da taimakon
na baya gare su!
Suna xaune a Rigasa cikin garin Kaduna!
Su Uku ne wajen Mahaifan su!
Farida itace First born, Fatima sai Hindatu itace
Yar auta.
Farida BAQA CE and frankly speaking bata da
wani kyau.
idanun ta ba wasu manya bane, haka xalika lips
dinta dai dai, bata da gashi kai.
Domin wani namijin ma yafi ta gashi!
Amma kuma yar gayu ce taqin qarawa!
Farida ta kamu da cutar Jinni tun tana yarinya!
Amma yanxu abn nata da sauki tunda ba ko
yaushe suke tashi ba.
Ahalin yanxu Farida tana 400lvl!
Shekartun ta 23 tana karantar Biochemistry!
Yayin da Fatima take 300lvl sai Hindatu 200lvl!
Gaba dayan su suna karatu a Kaduna States
University!
Suna maida hankali sosai!
Abunda ke daure kan wasu yan mata game da
Farida shine yadda maxa sune sonta.
Domin duk inda ta shiga saita samu sarauyi.
BAQAR MACE!
Gani suke kamar Farida bata da wani matsayin da
Xaisa wani yace yana sonta.
Kuma abnda ke qara basu haushi duk wanda
xaice yana sonta daga mai Kudi sai handsome
guys!
Farida duk min yadda Allah yayi mata muni that
doesn't mean ta saki kanta any how.
Allah yayi mata wani irn kamun kai!
Hakan yasa wasu suke gulmar ta wai duk munin
ta amma ta cika girman kai as if ta hadu.
Ita dai Farida duk maganar da mutane ke yi akan
ta.
Bata damuwa, ita daria ma wata maganar take
bata idan sunyi.
Farida Allah yayi ta mai haxaka, yes tasan cewa
ita ba wata mai kyai baice.
Amma hakan baisa ta watsar da mutuncin ta na
'Ya mace ba!
Bata shiga harkar daba nata ba! Duk wanda ya
nuna yana yi da ita.
Toh itama tana yi dashi.
BAQAR MACE!
Babban abnda yafi damun mutane shine yadda
suka ga Farouq yana nan nan da Farida.
Ita kuma tana wani jan qasa!
Domin da fari Farida bata son Farouq koh kadan!
Shi kuma har skul yake binta, akwai ranar da
Farouq yayi ta bin Farida duk inda ta saka qafa.
Ay kuwa saida suka je har cafeteria taxo xama
shi irin yadda indiawa ke yi ya jawo mata kujera
ta xauna.
Ay kuwa mistakenly ya shafar mata hannu ay
kuwa ta wanka masa wani wawan mari.
Mutane duk suka jiyo suna kallon su maxa da
mata!
Gashi wurin cike! Harga Allah Farouq baiji
haushin abnda tayi masa ba.
Domin son da yake mata yayi over!
Shi ji yayi ma ta qara kwanta masa cikin rai!
Duqawa yayi har qasa yana bata hakuri.
Farida ji tayi kunya duk ta kamata ace babba
kamar Farouq ya duqa yana bata hakuri.
Cike da kunya Farida tabar wajen!
Nan fa mutane kowa ya shiga fadar albarkacin
bakin sa!
Wasu matan na fadin wannan Mummunar Faridar
ta cika iyayi.
Wata Aisha tace nifa i don't know why maxa suke
son ta after all gamu masu kyau farare amma
wai....
Zainab ce ta amshe ta da cewar nima kaina abn
nan yana bani mamaki!
Ki duba kiga yadda Allah yayi mana halitta babu
inda Allah ya rage mu amma waccen banxar
BAQAR i just hate her!
Ahaka suka cigaba da maganar Farida kowa yana
fadin albarkacin bakin sa!ausa Novels
MEENATU DMS!
BAQAR MACE!
17
⃣ Farida bata da wata intimate friend ita kowa
nata ne!
Amma sai idan ka nuna kana yi da ita!
Bata da wasu abokan shawara sai sisters dinta.
Duk gidan su Farida ita kadai ce Mummana
amma sisters dinta duk masu kyau ne.
Domin su sun biyo iyayen su kasan cewar
mahaifan ta fulani ne!
Farida bata damu da munin ta ba domin tasan
haka Allah yake son ganin ta.
Duk gidan su Farida babu wanda bai san Farouq
ba!
Domin har mahaifin su yasan da Farouq kasan
cewar yana xuwa ya gaishe shi.
Kuma Abban nasu yana son Farouq domin ya
yaba da hankalin sa!
Farida tana da farin jini koh cikin family dinsu
domin kuwa tana kirki sosai da sosai.
Abun hannun ta koh kadan baya rufe mata ido.
Kowa yabon ta yake!
Awajen karatun addini Farida ba daga baya domin
tayi sauka sau 2 yanxu ma hadda take.
Babban abnda yake jan hankalin jama'a koh ince
samari wanda suka san ciwon kansu.
Shine Farida koh kadan bata yin shigar banxa.
Koh da yaushe tana cikim hijabi duk inda xasu je!
BAQAR MACE!
Duk inda mace matashiya mai hankali takai toh
Farida takai wajen.
Sam babu wanda xai budi baki tace yau ga abnda
Farinda tayi mishi.
Knowingly sai dai me Dan Adam ajixi ne tara yake
bai cika goma ba!
Sisters dinta Fatima da Hindatu suna bata girman
ta sosai!
Domin ta kame kanta, and when it comes to
advice she seeks it from her sister or mother but
not from a friend!
Abu daya ne sisters dinta suke ganin bata
kyautawa akan sa kuma suna fadi mata.
Shine yadda take debasing din Farouq kuma
hakan yana bata musu rai kuma suna fadi mata
gaskia.
Akan ta daina masa abnda take yi it's not good.
Wani lokaci Farida taji haushi wani lokaci kuma
ta share su.
Ita kanta wani lokacin tana tunanin abnda take
ma Farouq bata kyautawa.
Amma wata xuciar sai tace mata maxan yanxu
sai ana musu haka.
Abu daya yake saka Farida tsayawa da Farouq
shine yadda taga Umma tana son sa.
Not only Umma but her family!
BAQAR MACE!
CIGABAN LABARI!
Koh da suka shiga daki suka ga Farida tana
bacci!
Fatima ce Allah dai ya bama Babbar Yaya lafia.
Hindatu tace ameen! Amma wallahi Aljanun nan
suna wahalar da ita.
Allah yaso yanxu ma da sauki akan da!
Fatima tace addu'a xamu cigaba da yi mata!
Hindati ce ta shafa mata goshi domin yadda AC
ke aiki hakan bai hana mata xufa ba.
Sun juya xasu fita daga dakin, Farida ta tsaida
su.
Tashi taxo yi amma jikin ta babu qarfi.
Hindatu ce tayi saurin qarasawa ta tayar da ita.
Farida tace yaisge kuka dawo? Fatima tace yanxu
muka shigo gidan.
Farida tace toh yanxu ina xaku je??? Hindatu tace
abnci xamu ci.
Kinci abnci kuwa? Farida daga musu kai tayi
domin wahalar maganar take ji.
Da taimakon su taje tayi wanka, kafin ta fito
Fatima ta fiddo mata kayan da xata saka.
Sannan suka tafi dining domin yunwa suke ji.
Bayan sun gama ne suka ji maganar Farouq a
parlour!
Clapping hands sukayi tare da fadin sis muje muyi
labari da Yaya Farouq.
Suna tashi Dayyaba mai aiki taxo ta kwashe
komai wanda suka gama dashi ta wuce domin yin
wanke wanke.usa Novels
MEENATU DMS!
BAQAR MACE!
20
⃣ Da Sallama suka qarasa parlour suka gaishe
da Farouq.
Cike da far'a ya amsa, nan suka shiga labari
shida su Fatima.
Umma na xaune tana sauraron su sai daria take
musu.
Suna cikim haka Farida ta fito sanye da hijabin ta
har qasa.
Har qasa ta duqa ta gaishe da Farouq!
Sannan ta samu waje ta xauna.
Da dai daya da dai daya su Fati suka bar parlour.
Parlour ya koma daga Farouq sai Farida.
Nan suka shiga labari Farouq yana yi yana sako
kalaman soyayyah.
Farida kuwa yana yi tana rufe fuskan ta.
Domim kunyar Farouq take ji sosai!
Ahaka suka sha labari kafin daga bisani suyi
sallama.
Farouq yace baxai ta fiba har saita fada masa
cewar tana son shi.
Farida rufe fuska tayi sannan tace nifa baxan iya
ba gaskia.
Maimaita maganar da tayi yayi. Farida cike da
Shagwaba tace Allah ka daina.
Farouq yace i won't until you tell me that you
love me.
Farida yace i'll but not now. Farouq yace ni kuma
yanxu nake so.
Farida tace i said i'll but not now, i'll tell you but
through the phone.
Farouq yace ok promise? Farida tace yh promise.
Ahaka sukayi bankwana Farouq ya tafi gida cike
da farin ciki marar misaltuwa.
BAQAR MACE!
WANENE FAROUQ??
Farouq shine na biyu awajen mahaifan su kuma
shine last born.
Cikakken sunan sa shine Farouq Sulaiman, sunan
mahaifitar sa Hajia Amina.
Mahaifin sa da mahaifiyar sa sunyi auren
soyayyah.
Mahaifin sa Attijiri ne suna xaune.
Suna xaune a anguwar Rimi gidan su gida je qato
kuma mai kyaun gaske.
Mahaifin sa Senator ne mahaifiyar sa kuma
Lecturer ce.
Amma ahalin yanxu ta ajiye aiki.
Babban yayan sa shine Usman yana da aure
harda yaya 2 duka mata.
Farouq yana da shekaru 38 yana aiki a NNPC
kuma yana business.
Farouq ya kasan ce mutum kirki ga mutane baki
daya.
Farouq dogo je fari yana broad chest, yana da
dogon hanci, cutely lips which are pink.... yana
da manyan idanu.
Sumar kansa kwance take, haka sajen fuskar sa!
Farouq ya hadu iya haduwa, hakan yasa yan
mata ke son sa sosai.
Duk cikin matan Farouq babu wacce ta liqe masa
kamar Salimat qanwa ce ga matar Usman.
Sunan matar Usman Hafsah, Hafsah tana son
Salimat ta auri Farouq domin tasan qanwar tata
xata huta.
Shiyasa Salimat kusan kullun tana nan wajen
Umman Farouq.U DMS!
BAQAR MACE!
22
Farouq koh kalli Salimat bata ishe shiba!
Domin sam ya tsani ya kalle ta, hakan yasa duk
lokacin da ya shigo side din Umma ya ganta.
Saiya bar wajen!
Umma dai bata damu da yadda Farouq yake wa
Salimat ba domin bata son bacin ran autan nata.
Ita kanta Umma yadda taga Salimat na wannan
iyayin hakan yasa Umma bata takura ma Farouq.
Farouq bashi da babban aboki irin Ishaq.
Domin kuwa childhood friend dinsa ne, hakan
yasa suke kamar yan uwa.
Duk wani hali da Farouq yake ciki, Ishaq ya sani
haka kuma Ishaq duk halim da yake ciki Farouq
ya sani.
Ishaq yayi aure harda yarinya daya.
Ishaq yaso ace sunyi aure tare amma tun
alokacin da Farouq ya hadu da Farida when she
was in 200lvl.
Tun daga wannan lokacin Farouq ya leqe mata.
Ita kuma alokacin bata da raayin sa koh kadan.
Shi kuma Ishaq abnda yasa yake qin Farida shine
yadda yaga tana wulaqnta Farouq.
Ishaq adunia ya tsani yaga wani yana debasing
friend dinsa.
Hakan yasa ya dauki kin Farida ya daura shi cikin
ransa.ausa Novels
MEENATU DMS!
BAQAR MACE!
23
⃣
Tun tashin Farouq ya kasan ce abn so da qauna
awajen al'uma!
Arayuwar sa baya wulaqanta kowa, gashi abn
hannun sa baya rufe masa ido.
Farouq yana girmama yayan Usman!
Domim yana yi masa kallo kmar Abban shine,
kasan cewar Usman yanxu yakai shekaru 44.
Kamar yadda yake girmama yayan nasa haka
yake girmama matar sa.
Sai dai abu guda daya tsana game da matar
yayan nasa shine yadda take turo masa Salimat.
Wannan abu yana cima Farouq tuwo aqwarya.
Gashi baya son shiga harkar Salimat hakan yasa
koh gaishe sa tayi baya amsawa.
Domin ya lura kanta yana yi mata rawa.
Salimat ta kasan ce kamar kaska ga Farouq!
Don akwanakin baya har office ta riqa binsa.
Saida yayi mata dukan gaske cikin office sannan
yayi mata korar kare.
Wannan dalili yasa Salimat jin tsoron Farouq
sosai da kuma ja baya gare shi.
Ta rasa gane dalilin da yasa Farouq baya sonta.
Abu ma farko dai ita tasan tana da kyau domin
koh cikin mata masu kyau toh ta kai.
Gata kuma yar gayu, amma Farouq koh kadan
baya ganin wannam baiwar da Allah yayi mata.
BAQAR MACE!
CIGABAN LABARI!
Kamar yadda Farida tayi alqawarin cewar xata
fadi masa cewar tana sonsa.
Haka kuwa akayi, domin bayan ya kira a waya ne
take qara bashi hakuri akan abnda tayi masa
baya.
Sannan tayi declaring cewar tana son sa.
Murna wajen Farouq baa magana.
Wasa wasa soyayyah tsakanin Farida da Farouq
ta ginu.
Soyayyah suke tsakani da Allah, babu wani aibu
acikin kalar son da Farouq yake mata.
Farida wani lokaci har mamaki take akan yadda
Farouq yake nuna kulawar sa akan ta.
Wani lokaci gani take kamar mafarki taki.
Wani lokaci kuma gani take anya bata cuci
Farouq ba? Domim shi mai kyau ita Mummuna.
Farouq da Ishaq sun shrya domin yanxu Ishaq in
banda yabon Farida babu abnda yake yi.
Hakan yasa suke shiri sosai da Farouq yanxu.
Kuma shi kanshi Ishaq ya gano halin Farida da
yadda take da mutunci.
Hakan yasa ya gane ashe abaya yadda ya dauke
ta ba haka take ba.
Ahalin yanxu Ishaq yana girmama Farida badan
komai ba kuwa sai yadda ya lura da halayyar ta
da dabi'un ta suke.
Maganar aure ta taso gadan gadan domin an
saka ranar biki wata biyu kacal.
Murna wajen Fati da Hindu baa magana.
Haka wajen Farouq da family dinsa Excluding
Hafsat and Salimat.sa Novels
MEENATU DMS!
BAQAR MACE!
25
⃣ Ahalin yanxu an saka ranar bikin su.
Wata uku kawai aka saka... Farouq ne xaune
yana tunanin inda xau samo ma Farida Maganin
aljanu.
Domin yanxu aljanun ta sun cika tashi.
Shirin biki akeyi, sosai domin yanxu baifi saura 3
weeks ba.
Anyi siyama Farida kaya na gani na fada. Amma
still har yanxu aljanun ta suna tashi.
Farouq aduk lokacin da aljanun Farida suka tashi
yana shiga damuwa sosai.
Hakan yasa yake qara sonta sosai domin wannan
lalurar tata.
Akwana a tashi yau baifi saura kwana 8 bikin ba
hakan yasa hidima koh ta ina ta kacame.
Dangi ta koh ina sun iso, Farida sai shiri suke ita
da su Fatima.
Haka Farouq shima duk wanda ya gansa yasan
yana cikin farin ciki.
Salimat tafi kowa baqin cikin wannan bikin.
Hakan yasa ta tattara ta koma Kano.
Domin ita a ganin abn kunya ne ace wanda take
so xai auri wannan BAQAR MACEN. what a big
slap on her face? That's what she thnk.
BAQAR MACE!
Yau Friday aka daura aure Farouq Sulaiman da
Farida Ahmad.
Bayan sallan juma'a, an daura auren ne abisa
sadaki naira dubu ashirin.
Babu wani party da akayi, da dare aka dauki
amarya aka kaita gidan ta dake, Malali.
Gida ne na gani na fada, matar Usman ji take
kamar ta kashe Farida dan baqin ciki.
The next day akayi walima, kowa ya gama gaban
sa tare da neman musu xaman lafia.
BAYAN WATA UKU.
Soyayyah suke tsakani da Allah, Farida tana bin
duk wata doka da umarnin Farouq.
Farouq yana qaunar matar sa koh kadan baya
son abnda xai bata mata rai.
Aljanun Farida suna tashi akai akai, Farouq yana
bala'in tausaya mata.
Ishaq yaxo masa da labarin Arriyad Islamic
Chemist!
Ba tare da bata lokaci ba suka je harda Farida.
Cikin ikon Allah aka basu magani, duk rana kafin
Farouq ya tafi Office sai ya bata tasha sannan ya
tafi.
Haka kuma da yamma.
Cikin ikon Allah yanxu Farida sai tayi... wata 6 ba
tare da aljanun sun tashi ba.e of Hausa Novels
BAQAR MACE!
27
Farida ce xaune bisa qafar Farouq.
Farouq sai jan ta yake yana fadin mai ciki...
Farida sai turo baki take tana fadin wallahi bani
son sunan nan.
Farouq ya fashe da daria, yace Allah dai ya
rabaku lafia.
Farida tace ameen!
Farouq yace inace yanxu cikin 6 months yake
koh?
Farida tayi saurin cewa wallahi, 9 months ne ka
daina maida ni baya.
Farouq ya fashe da daria, yace wai miya baki son
na maida ke baya ne?
Suna cikin maganar suka ji sallama.
Ahankali Farida ke shirin tashi dan bata son
atarar da su ahaka.
Farouq ne ya temaka mata!
Tun kafin su shigo Farida ke fadin Oyoyo ga
sisters.
Bayan sun shigo sun gaisa da Farouq, sun taba
yar fira, kafin daga baya Farouq ya bar gidan.
BAQAR MACE!
Hindu ce ke fadin wallahi sis cikin nan ya miki
kyau.
Nidai Allah yasa idan nayi aure nawa yayi mani
kyau!
Buge mata baki Farida tayi tare da fadin marar
kunyar banxa kawai.
Hindu turo baki tayi, tare da fadin ay gaskia ce.
Fati babu abnda take yi sai daria.
Basu bar gidan Farida ba saida sukayi Magrib
prayer sannan.
Farida ji tayi kamar kada su tafi.
Yau Farida ta tashi da nakuda.
Sun isa asibiti, an shiga da ita labour room.
Farouq sai safa da marwa yake yi.
Kafin kace haka dangi sun cika asibiti.
Farida ta sauka lafia inda ta haifi 'Yar ta mace
mai kama da Farouq.
Murna wajen Farouq baa magana.
Haka both families din!
Bayan an sallame su, gida aka wuce da Farida!
Farouq yaso ace gidan sa xatayi wanka amma
Umma ta hana.of Hausa Novels
BAQAR MACE!
29
Ranar suna yarinya taci suna Aisha!
Farida ta samu abn dunia dai dai misali.
Taron suna ya tashi lafia kiwa yana fadin Allah ya
raya.
Ya kuma maido su wata shekarar suna.
Bayan wata 3 suka koma gida.
Murna wajen Farouq kamar me, more especially
da yaga babyn sa sai qara kyau take gata bulbul.
Farouq yana taking good care of them.
Hakan yasa Farida ta qara kwantar da kanta
wajen mijin ta.
Aljanun Farida suna tashi amma ba sosai ba.
Bikin Fati da Hindu ya matso domin yanxu baifi
saura 14 days ba.
Hakan yasa suke ta shiri basu cika xama sosai
ba.
BAQAR MACE!
Anyi biki an gama lafia amare gaba dayan su
Kano aka kaisu.
Farida sunsha kukan rabuwa da yan uwan nata
ranat walima.
Sun dawo gida ita da Farouq kamar wasu marar
da lafia.
Farouq ne da yaga abn nata yayi yawa yace Allah
idan bata saki ranta ba xai ce bata qara xuwa
Kano.
Hakan yasa Farida ta saki jiki ta koma kamar da.
Amma tunanin sisters dinta cike da ranta.
Xaune take tana tunanin wannan kasalar da take
fama da ita yan kwanakin nan.
Basu bata lokaci ba suka isa asibiti. Gwajin farko
likita ya sheda musu Farida tana dauke da ciki
wata 4.
Farida abn ya bala'in bata mamaki domin
alokacin Mama shekarar ta daya da wata uku.
Farida bata tada hankali ba domin taga yadda
Farouq yake ta murna.
Hakan yasa ita ta taya shi murnan tasa.
BAYAN 6 MONTHS.
Farida ta sauka lafia, ta haifi danta namiji shima
mai kama da Farouq but some how yana kama
da ita.
Yaro yaci sunan Abban Farouq wato Sulaiman,
suna kiran sa da Junior.
Haka rayuwar tacigaba cikin jin dadi da qaunar
juna.
Farouq dai qara samun daukaka yake ta koh ina.
ALHAMDULILLAH!
Anan na kawo qarshen wannan littafi mai suna
BAQAR MACE.
Nayi wannan littafin badan komai sai dan na jayo
hankalin marubutan littafin Hausa.
Akan musan cewa bawai macr mai kyau fara
kadai bace in the world.
And ba ita daya bace maxa suke so.
And also ba Farar Mace mai kyau kadai take da
aji ba. Suma BAQAQE MA MATA NE. Kuma masu
Aji.
Masu aji, domin gaba dayan mu babu wanda yafi
awajen Allah sai wanda yafi tsoron Allah.
Na fiddo Star din wannan novel BAQA kuma
MUMMUNA. Kuma mai ALJANU.
Kuma ahaka classic guy ya aure ta. Kuma ya
gwada mata SO DA QAUNA.
No body is better than any one to Allah except
the one who fear him the most.
So ina son musan cewa kyau ba wani abu bane,
domin da wani kyan gara muni.
I Aminatu Dan-Musa dedicate dz novel to all the
BLACK MUSLIMS WOMEN where ever you may
be!
CHEERS TO BLACK WOMEN .
HADAWA BY
MARYAM AMEERA YOLA
RUQAYYA GAMBO AWE
SAKINA USMAN
0 Response to "BAQAR MACE Hausa Novel"
Post a Comment