-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Za Mu Ƙara Fitar Da Sunayen Mutum 500,000 Da Suka Samu N-Power— Sadiya Umar Farouk

Za Mu Ƙara Fitar Da Sunayen Mutum 500,000 Da Suka Samu N-Power— Sadiya Umar Farouk

Za Mu Ƙara Fitar Da Sunayen Mutum 500,000 Da Suka Samu N-Power— Sadiya Umar Farouk

Mun Zaɓi Mutum 550,000 A Rukunin C Na N-Power— Ma’aikatar Jin Ƙai, Kare Afkuwar Annoba da Walwalar Jama’a ta ce aƙalla mutum 550,000 ne suka cancanci samun aikin N-Power na Rukunin C daga cikin mutum miliyan 1.8 da suka nemi aikin. Sadiya Umar Farouq, Ministar Ma’aikatar ce ta bayyana haka a wani taron manema labarai ranar Talata a Abuja. Sadiya ta ce ranar 11 ga Maris ne ma’aikatar ta ƙaddamar da Shirin Kyautata Walwalar Jama’a, NASIMS, na Rukunin C.Ta ce an buƙaci masu neman aikin na N-Power da su sabunta bayanansu, daga bisani kuma suka yi tes a shafin Intanet na NASIMS.

“A mako na uku na watan Mayu, 2021, fiye da mutum miliyan 1.8 ne sun sabunta bayanansu kuma sun yi tes.

“An ƙara wata tantancewar inda mutum dubu 550,000 suka cancanci zuwa matakin ƙarshe don su shiga cikin mutum 500,000 da dama tuni suna aikin N-Power”, in ji Ministar.

“Wannan Rukunin C ne. Za a fito da jerin sunayen mutum 500,000 a rukuni na biyu kamar yadda Shugaban Ƙasa ya bada umarnin ɗaukar mutum 1,000,000 a Rukunin na C”, ta ƙara da haka.


Turawa Abokai

0 Response to "Za Mu Ƙara Fitar Da Sunayen Mutum 500,000 Da Suka Samu N-Power— Sadiya Umar Farouk"

Post a Comment