-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Yadda Kayan Lefen Muh'd Ya Tayarda Hankalin Matasa

Yadda Kayan Lefen Muh'd Ya Tayarda Hankalin Matasa

Yadda Kayan Lefen Muh'd Ya Tayarda Hankalin Matasa

Duba kayan lefen Muhammad da ya kaiwa amaryarsa 

A shafin BBC hausa sun bayarda ma anar lefe da cewa: Lefe wata al'ada ce da al'ummar Hausawa suke gunanarwa a lokacin da ake shirye-shiyen yin aure musamman auren fari tsakanin saurayi da budurwa.

Kayan lefe na ci gaba da raza samari inda akullum abin sai karuwa yakeyi, hakan yaja daru-ruwan samari kasa yin aure dawura, hasashe ya bayyana cewa kayen lefe daya daga cikin abubuwanda ke kawo tsaiko da kuma cikasa a lamarin aure inda 1daga cikin dari na baiko ke watsewa bisaga rashin kayan lefe. 

Wadansu mutane suna ganin cewa wannan dadaddiyar al'ada ta lefe tana da amfani kuma kyakkyawa ce, saboda haka ya kamata a habbaka ta, a inganta ta, a kuma rike ta da muhimmanci. Wadansu mutanen suna ganin wannan al'ada a matsayin mummuna wadda take cutar da al'umma musamman samari da ma 'yan mata da rayuwar aure.


Ra'ayoyin jama'a akan kayan lefen da wani saurayi ya kaiwa budurwarsa


Malam Ismail Boss yace

To wai ita yarinyar meye matakin karatunta na boko tana degree ko master Kuma tanada haddar qur anine sbd yarana shin wane irin tarbiyya aka ginata akai kunada tabbacin wani betaba saninta a ya maceba kafm tazo gidana???? Wadan nan baqaqen bidi oin sune suka janyo Zina tayi yawa a najeriya sbda bakada kudin wannan ga sha a we tasaka a gaba kawai sekaje kaci me arha kabada dari biyar kayi minti goma kadawo haiyacinka ko ka kwamishe yaran mutane kakaisu kango inkagama se kabar iyayenta da zuwa asibiti. |yaye kuji tsorron Allah Nima danake maganar ban tsiraba Dan haryanzu banida mata eheeeee .


Shi kuma Abdul lsah Musa ya kara da cewa

Wannan matsalarku ce fa 'domin wannan baya haddasa komai illa bala'i dakuma yaduwar Alfasha cikin al‘umma. Ku rage buri a wannan rayuwar sabida mu gudu tare mu tsira tare,sannan shi tsadan lefe yana daya daga cikin abinda ya janyo yawaitar fyade da kuma zinace_zinace a cikin al'umma. Ya rage naku inkun gyara Dan kanku ,inkuma xaku cigaba bismillah .


Duk da haka Ibrahim Nasir yace

To Saime yanMata ake kara jazawa ba|a'i..saboda sune sukeda lokacin aure wanda idan yawuce zasu zama abun tausayi..namiji kuwa Zai iya daukan tsawon lokaci batareda yayi aure ba kuma gidansu baza'a gaji dashi ba..shiyasa Mazajen aure sukayiwa yanmata wahala..kowace Ta dauki dogun buri nason abun duniya tasanya aranta. Mata sune sukafl Bukatar Aure flyeda namiji..don haka idan aure yayi sauki jindadin sune.haka idanma yayi tsada sune zasufl shiga damuwa. 


Sai muka rufe da Muhd Bellow Kut.. Yace

Lallae anbar sunnar annabin rahama dole muyii ta Shan wahala wallahii... Irin wannan kae kasan babu Allah aciki w|h...meye zaayi da wnn kayan Dan Allah idan ba dorawa kae masifa baaa... Samarii suna nan masu tarin yawa wadanda sana'arsu zata ishesu su riqe mata harda yara cikin mutunci Amma wannan bidi'ar ta hanasuu yin auren domin basuda wadannan kudaden masu yawa a hannu Wanda zaayi hidimar bikin.. Allah ya kawo Mana daukiii Muna San aure Amma ana qir qiro abubuwan da suke qara nisantamu da auren.


Bayyana ra ayinka dan gane wannan lefen

0 Response to "Yadda Kayan Lefen Muh'd Ya Tayarda Hankalin Matasa"

Post a Comment