-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Kuncin Rayuwa Yasa Nayi Yunkurin Kashe Kaina - Ummi Zeezee

Kuncin Rayuwa Yasa Nayi Yunkurin Kashe Kaina - Ummi Zeezee

Kuncin Rayuwa Yasa Nayi Yunkurin Kashe Kaina - Ummi Zeezee

Fitacciyar jarumar masana’antar Kannywood, Ummi Ibrahim, wacce aka fi sani da Ummi Zeezee, ta ce ta shiga yanayi na kuncin rayuwa, inda har ta kan ji kamar ta kashe kanta.

A ranar Asabar Ummi ta fadi hakan a wani sakon da ta wallafa a shafinta na Instagram.

“A ‘yan kwanakin nan, na shiga matsanancin kuncin rayuwa, ta yadda har na kan ji ina so na kashe kaina.” Ummi ta rubuta da harshen Ingilishi.

Sai dai jarumar wacce ta yi fitattun fina-finai irinsu ”Jinsi,” “Gambiza” da “Tutar So” ta ce kada kowa ya tambaye ta dalilin da ya sa take so ta aikata wannan danyen aiki.

“Amma don Allah kada kowa ya tambaye ni dalili me ya sa, abin da nake bukata a gare ku shi ne, addu’a.” Jarumar ta ce, wacee ta yi amfani da manyan harrufa wajen rubuta wasu daga cikin kalamanta.

Ummi ta kasance daya daga cikin jaruman masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood da tauraronta ya haska a farkon jerin shekarun 2000.

Ta yi fina-finai da dama da fitattun jarumai irinsu Ali Nuhu, marigayi Ahmed S. Nuhu, Abba El Mustapha da Ibrahim Mai Shunku.

A lokacin da take haskawa, ta yi tashe tare da jarumai mata irinsu, Jamila Nagudu, Farida Jalal, Ummi Nuhu, Hafsat Shehu da Rashida Mai Sa’a, Rukayya Dawayya da Mansura Isah.Sai dai daga baya an daina jin duriyarta na tsawon wasu shekaru da dama a harkar fina-finan Hausa, lamarin da wasu suke ganin ya sa tauraronta ya dishe.

@Daga VOA Hausa

0 Response to "Kuncin Rayuwa Yasa Nayi Yunkurin Kashe Kaina - Ummi Zeezee"

Post a Comment